Sashe 2
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki kai ƙara gaba da nan. Birni za ki je ki kai mu ƙara gurin 'yan sanda, in kika tsaya iya nan ba ki ci ba." Kaka Tani ta ce tana harararta.
"Ni takaici ya hana ni cewa komai, so na yi na karya mata wuya, tun da har cikin gidanmu ta shigo." Jimmalo ta furta tana zare ido.
"To ku wuce mana, kun zuba mana idanu munafukai kawai!" Kaka Tani ta daka ma mutanen dake tsaye, a tsakar gida tsawan tana faɗin haka.
Da sauri suka fara fita sum-sum ba tare da sun furta komai ba.
"Munafukai kawai! Wallahi daidai muke da kowa a garin nan, tun da kuka nuna ba kwa sona da jikata." Cewar Kaka Tani tana gyara ɗaurin ɗankwalinta.
"Ki sha kurumunki ki bar ni da su. Ni kawai na ishe su kakata, ba sai kin wahalar da kanki ba."
"Haka ne jikalle ta, amma ki kula kar wani ya illanta mini ke..."
"Ni! Har a garin nan akwai wanda zai iya dukana?" Ta yi mata tambayar, tare da zare ido cikin mamaki ta dafe ƙirjinta.
"Na san babu wanda zai iya dukanki, amma ba na san asamu akasi, kin san ke kaɗai nake gani na ke jin daɗi."
"Ki sha kurumunki kakata, don ni Jimmalo na zama gagara badau! Kuma na gagari kowa a ƙauyen nan har maigari." Ta yi wa kanta kirari da hakan tana danƙwashi kanta.
"Kin ga Jimmalo, na gaya miki ya kamata ki kwance kanki na siyo miki fiya-fiya, ki sanya ma ƙwarkwatan kanki."
Dariya ta yi tana ƙara rankwashi kanta da ƙarfi, saboda zafi har sai da ta ce,"Wash!" Tare da cige leɓe.
"Aradu babu wata fiyafiyar da zan sanya, saboda ina jin daɗin kashe tana cewa ƙas!ƙas!!" Sai ta ƙara kwashe da dariya tana dukan kan.
"Ya dai kamata gyara kanki."
Jin abin da ta ce, ya sanya ta ta shige cikin ɗakin ba tare da ta ce mata komai ba, domin idan akwai abin da ta tsana ace mata ta gyara kanta. Tana da zafin kai, kuma ya haɗu da ƙazanta.
Ma'u cikin kuka ta ƙara da gurin gidan maigari. Kuka ta ƙara saki sannan ta kwashe komai ta faɗa masa, sannan ta ƙarashe maganar tana faɗin,"Maigari ka yi mini tsakani da ita, wallahi na gaji da rashin mutuncin da take mini, har gida take bina tana ci mini kayan sana'ata, kuma ba ni da ikon na yi magana su haɗu su yi mini duka."
"Kai wallahi na gaji da ƙarar da ake kawo mini na mutanen nan! Ace mutane biyu sun gagari ƙauye nan? Ko jiya sai da aka kawo mini ƙarar yarinyar nan, ta je ta zagi wani tsoho."
"Jimmalo ba ta da tarbiya kwata-kwata kakarta ba ta mata tarbiya mai kyau. Allah ko ni yarinyar nan ina haƙonta, don dukan da ta yi wa ɗana Usmanu."
"Je ka yi mana kiransu." Ya faɗa cikin takaici jin abin da ya ce.
Miƙewa ya yi jikinsa na zikiri ya fice da sauri. Yana tafe yana addu'ar Allah ya sanya ayi mata dukan tsiya.
"Assalamu alaikum," Ya kwaɗa sallama tare da jingina da garu.
"Waye yake damun mu da sallama kamar munci masa ba shi?" Ta fito tana tafiya cikin gadara.
Harara ya zabga mata yana yatsina fuska."Ai sai ki fito ki gani fitsarrarriya mara kunya."
"Ga ka Malam ka daina kirana da fitsarrarriya, don ba haka uwata da uban suka sanya mini ba. Ta ce mishi cikin tsawan.
"Zagina za ki yi?" Ya yi mata tambayar cikin zallar mamaki.
"In ta kama mai zai hana? Don wallahi bana tsoron uban kuwa, kuma dama duk babban da bai ja girman shi ba, ai sai yaro ya yi wasa da girman a ƙasa."
Mamaki ya cika shi ganin yadda take zare idanu, kamar tana magana da sa'anta.
"Ke kan Jimmalo, albasa ba ta yi halin ruwa ba, saboda kowa ya san iyayenki suna da mutunci. Allah ya ɗibe miki albarka. Kamata tsoho da ni fuska duk gemu kike zagi?"
"Ni fa Malam ka kama girmanka." Ta furta tare da ɗaga masa hannu.
"Ba komai za ki haɗu da gamonki. Sai ki je in kin ga dama maigari yana neman ki da kakarki."
Jin abin da ya ce, ba tare da ta tsorata ba ta kama ƙunkunai. "Zaginsa za ki yi kenan?"
"In ji maƙura sai na gaya maka." Ta faɗi da ƙarfi tana zabga masa harara.
"Allah ya kawo mana guguwar da za ta kwashe ki ki bar garin nan, domin a ranar sai mun zuba ruwa a ƙasa mu sha."
"Tun da ga annoba ta tafi ba, to ina nan zama daram-dam a cikin ƙauyen nan." Ta ce tare da jan tsuka ta shige ciki.
"Da ikon Allah sai kin bar ƙauyen nan, muna nan muna jan miki yasin da tabaraka. Yarinyar sai ka ce jujal duk tabi ta addabi mutane." Ya ce yana tafiya.
"Kaka Tani, kin ji maigari yana kiranmu." Ta yi maganar cikin shagwaɓa.
"To sai me? Kiran maigari kiran Allah ne. Ma za ɗauki mini mayafi mu je, in ta kama ai ko agabansa zan yi faɗa da kowa a kanki."
Murmushi ta yi, jin abin da ta ce tana kallonta."Shi ya sa na ke so ki kakata."
"Ni ma ina son ki Jimmalo takwarata."
A hanya suna tafe suna hira, tamkar ba laifi suka aikata ba har suka isa.
Cikin gadara ta tsaya a bakin ƙofa tana aikawa Ma'u mai gyaɗa harara.
"Za ki shigo ki zauna mara kunya." Cewar wani a cikin zauren.
"A ka yi mata a hankali, kar ka tsorata mini jikata." Kaka Tani ta furta tana kallon sa.
"Na gaji da ƙarar ku da ake kawo mana kullum. Jikarki tana aikata ba daidai ba, amma soyayyar da kike mata ya rufe mata idanu."
"Ka san ita mai ta aikata maigari? Matar nan fa har gida ta biyo jikata zata buga. Ni kuma da yake bani da hankali sai na tsaya ina kallonta? Wannan dalilin ya sanya na ɗauki matakin da kowa ce uwa za ta ɗauka, saboda ba zan iya gani ba ta dukan mini jikata."
"Wallahi maigari, yarinyar nan har gida ta shiga ta ibar mini gyada ina ina ƙullawa."
"Innalillahi! Amma baki da mutunci ƙarya za ki yi mini. Ba shi na siya kuma na ce zan biya."
"Ke!" Ya daka mata tsawan jin abin da ta ce.
"Sam ba kyau girmama manya ko?"
Tura baki ta yi tare da kallon gefe ba ta ce masa komai ba.
"Tun da bashi kika siya ki biya ta kuɗinta."
"Zan biya ina samu, dama ba ce ba sha nono uwa ba." Ta yi maganar a hankali, tana tura ɗankwali gaba tare da sakin ma kanta ranƙwashi.
"To ki ba ta kuɗinta."
"Za ta biya inta samu, saboda bamu da shi, kuma yanxu ko gwamnati ana binta ba shi."
"Kin ga Tani? Wallahi in har ba ki rinƙa wa jikarki faɗa ba zan saɓa muku a garin nan, in har kuka ƙara shiga sabgar wani sai na sanya an ko..."
Maganar ta katse sakamakon kukan da ya ji ta saka."Saboda zalunci sai ka yi mini barazana da barin ƙauye da aka haifi iyayena da kakannina? Shikenan ina gani a doki jikata kuma a hana ni na yi magana? Wa take da shi a duniyar nan da ya wuce ni." Kuka take sosai tana share majina.
Ganin haka ta saka kukan ita ma." Ki yi shiru ki daina kuka kakata. Kin san hawayenki kawai yake sanya jikinsa ya yi sanyi. Ki yi haƙuri tun kafin hawayenki, ya tunzura ni na cinna ma gidan nan wuta."
Zare idanu su suka yi cikin mamaki, jin abin da ta ce, wanda sun san tsaf za ta iya aikata wa.
"Dole na yi kuka Jimmalo, kina gani ni da ƙauye mu ana mini barazana. To wallahi ƙauye nan sai dai ina mutu akai kashewa bayan gari, don ko na mutu ban aminta akai gawata wani guri ba."
"Ki share hawayenki ko an kaiki, sai na je ƙabarin na ƙwaƙwulo na cika miki wasiyar ki, ballantana ba za ki mutu ba kakata."
Kuka suke yi sosai kamar su aka cuta. Mutanen cikin zauren sun kasa cewa komai sai kallon su suke yi. Saboda takaici sun kasa magana.
Ganin sun yi shiru, kamar yadda suka saba, sai suka miƙe suka fice daga zauren
Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu bar su suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar sai su rinƙa kukan munafunci kamar su aka cuta?"
"To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai iya ba, sai a natsu da Allah."
Zariya birnin Shehu garin ilmi.
Babban gidane a cikin unguwar Juma, wanda daga gani ka ga ginin da, domin irin ginin nan ne, mai ɗauke da ɗakuna sosai har da gidan sama. Saboda wadata da wasu daga cikin waɗanda suka taso a cikin gidan, sai aka yi gyare-gyare aka ɗan sauya gidan har da tayas da kuma filista a ka yi mishi, sannan kowa ya killace sashinsa, ya kewaye da kwano.
Tsakar gidan ya sha siminti mai kyau sosai. Kasancewar gidan ɗauke yake da matan yayyi da kanni har ma da kawunnai, sai aka samu yawaitar 'ya'ya a cikinsu, domin akwai 'yan mata kyawawa da kuma samarin maza.
Hanifah ce take sashin Anty Mariya, amaryar babansu tana kwalliya bayan ta fito daga wanka. Hindatu ce ta yi sallama ta shigo da anko da ta karɓo daga gurin ɗinki.
Da sallama ta shigo cikin ɗakin bayan ta gaishe da Anty Mariya ta wuce ƙuryar ɗakinta. Turus ta yi ganin Hanifah sai a lokacin take shafa hoda.
"Wai ni saboda Allah wane irin kwalliya kike yi? Tare muka fito wanka har na yi kwalliya na tafi gidan A'isha Tela na karɓo kaya, amma har yanzu kina nan kina shafa hoda. Hanifah ko fuskarki kike son canzawa sai haka."
Murmushi ta yi, tare da ɗaukar kwalli ta bayan ta ije soson hodan.