← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 52

Sashe 42

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jimmalo sai ta ƙara wage baki."Na rantse ko tsire ni za a yi, ba zan ƙara zuwa makarantar nan ba. Shegu mugayen masu zuciyar arna." Abin da ta furta kenan lokacin da ta shigo falon.

Umma tsaki ta yi, burinta kawai ta shige ɗaki ta je ta kwanta, kuma yau ta rantse sai dai a kaita wani ɗakin ta kwana.

Idanu suka zuba mata har ta shigo tana kukan. Anty Amarya mamaki sosai ta yi ganinta, domin ta ɗauka babba ce sosai, musamman ganin yadda Aliyu yake data jijiyar wuya in yana maganarta.

"A mayar da ni Damagaran, saboda na gane ƙarya kike mini wayo kika yi mini aka kai ni makaranta. Mugayen sun cire mini kayan da na gada gurin kakata, kuma sun yi mini wanka." Ta furta cikin baƙincikin hakan tare da zubowar hawaye a fuskarta.

"Masha Allah! Ubangiji ya yi musu albarka, domin sun biya ni. Jimmalo kin ga yadda kin yi fasali kuwa? Sam ba kya wannan warin, yau za ki yi kwanan daɗi?" Mommy ta yi mata tambayar tana kallon ta.

"Ni kawai a kaini ƙauye na fi son rayuwar ƙauye, domin ba zan yi karatun bokon ba." Ta furta tare da zama gefen kujera.

"Yanzu ina littafanki?" Mommy ta yi mata tambayar da son kauda zancen.

"A can na bar musu saboda ba shi da amfani a gurina. Na rantse ko na Muhammadiya ce ba zan yi ba, ballnatana ta arna."

"Za ki yi ilmi shi ne gishiri zaman duniya, domin shi ne yake bambanta matacce da rayayye, kuma wanda ba shi da shi. Misalin jaki ne aka ɗaura masa dakon littafai."

Jin wata murya ta yi mata daban, sai ta ji muryar ta yi mata wani iri. Da sauri ta ɗago idanunta tana kallon Anty Amarya da take kallonta cike da tausayawa. Ace kamar wannan ta rayu babu sallah babu tsafta, duk da cewar ta yi wanka, amma da ka ganta kasan tana rayuwa ne cikin ƙazanta da rashin kula. Dole Aliyu ya tsane ta, domin ko ita wani lokacin mamakin tsaftar shi ta ke yi.

"Ke kuma ina...." Ta buɗe baki za ta yi mata rashin kunya, amma kuma idanunta da ta ɗora bisa nata sai ta kasa. Wani irin ƙwarjini ta yi mata, har sai da ta cire idanunta sannan ta ƙara mayarwa. Bayan Kaka Tani za ta iya cewa babu wanda take ƙauna a cikin duniyar, domin kowa keta masa rashin mutunci take yi, amma yau ta haɗu da wacce ta ji ba za ta iya mata rashin kunya ba. Wacce za ta iya mayar da ita 'yar'uwa. Wacce lokaci guda soyayyar jini ta haɗa su ta yi mata ƙwarjini sosai. Har take jin za ta iya ba ta wani gurbi a cikin zuciyarta. Idan da ita za ta yi rayuwa, tabbas za ta haƙura da kuka da ɓurari da take yi don a mayar da ita Damagaran. Sosai shaƙuwar jini ya shiga tsakaninsu.

Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri ba.

To fa Jimmmalo ki rasa wacce za ki ji ta yi miki sai yar gidan Aliyu da yake jin babu kamarta? Hmmmmh lailai za ki tashi kan Aliyu. Comments kun san fa shi yake karawa marubuci karfin yin rubutu.

Jimmalo za ta haƙura ta ci gaba da zuwa makaranta? Aliyu zai zauna a gidan sannan zai samu damar auren irin macen da aka zaɓa masa? Ku dai biyo ni cikin littafin.Na gode da comments da kuke yi Ah ya barmu tare.

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 21

*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*08130902505*

Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri ba.

A karo na biyu, ta ɗago idanunta ta ɗora a kanta tana kallonta cikin ƙauna irin ta jini. Mommy sai tsananin mamaki ya kamata, ganin yadda jikinta ya yi sanyi take kallon Anty.

"Ni fa makarantar ne bana son na yi, ko da zan zauna a birni, amma a cire ni a makaranta." Ta furta hakan tana ƙoƙarin zama.

Mommy saboda tsananin mamakin ganin yadda ta yi, sai ta kalli Jimmalo da idanunta yake kan Anty Amarya.

Murmushi Anty Amarya ta yi ta zama a gefenta, tana kallonta domin ita sam ba ta ga taurin kan da ake faɗin tana da shi ba.

"Yanzu kin dawo, ma za ki je ki cire kayan makaranta ki canza sai ki yi sallah ki fito ki ci abinci, domin an gaya mini ba kya sallah, na san ba ki yi a makaranta."

"Zan yi in zan kwanta, anan gidan kike?" Ta yi mata tambayar da ya cika su da mamaki.

"A'a amma ni 'yar uwar gidan nan ne, ina zama a Zariya."

Saboda ba ta san Zariya ba, sai ta taɓa bakinta lokaci guda fuskarta ta canza, domin ta so a ce a gidan nan take.

Miƙewa ta yi, za ta nufi cikin ɗaki don ta cire kayan jikinta, saboda sam ba ta ƙaunar ganin kayan a jikinta.

Mamaki sosai ya ƙara kama Mommy."Wonder shall never ends. Jimmalo ce ta yi magana da ke ta fahimta? Laillai na yi mamaki ƙwarai, ke kuwa wane irin farinjini kike da shi? Domin tun da ta zo gidan nan take shuka rashin kunya, hatta Daddy ba ta ɗaga masa ƙafa ba.

Dariya ta yi ta ce,"Ikon Allah kenan! A cikin duniya ba ka rasa wanda za ka ji maganarsa. Ba kya ganin wani lokaci mukan yi tarayyar da mutanen da suke gaya mana magana mu ji kuma mu ɗauka, ba tare da mun bi na iyayenmu ba. Wasu yaran ko sanar da iyayensu ba sa yi. Ƙawa sai ta canza rayuwar danka, ta kuma ba shi muguwar shawara ya ɗauka."

"Na yarda da hakan domin ga zahiri nan. Ni kam zuwan ku babu abin da zan iya cewa, sai dai na yi miki godiya."

"Ba komai ai yaro na kowa ne. Har yau ina jin damuwar rashin haihuwa da bana yi, domin babu abin da ya kai haihuwa farinciki da yaye damuwa." Ta ƙarashe maganar hawaye yana zuba a ƙuncinta.

Ganin haka sai hankalinta ya tashi, ta ƙarasa gurinta tare da kama hannunta."Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke, kuma in ya so sai ya ba ki a lokacin da kika cire tsammani. Na sam cewa babu bin da yafi haihuwa daɗi, amma kar ki manta Ubangiji ya ce yana jin kunyar macen da bai ba ta haihuwa ba, sannan akwai bin da ya tanadar musu ranar gobe kiyama wanda ya barwa kansa sani."

Ta numfasa sannan ta ɗora ganin har yanzu da damuwar a fuskarta. "Akwai haihuwar da Allah zai ba ki, sa kin gwammace da ma ba ki haihu ba. Yaran da ake haifa suna lalacewa suna zamar wa duniya annoba. Kin ga da irin waɗannan yaran, gara mutum ya mutu ba tare da ya haife su ba. Sannan akwai yaran da su za su kai iyayensu wuta."

"Haka ne Ubangiji ya bani yaro domin da ciwo, don na samu kishiyar da ba ta mini ido kan yaranta, amma da yanzu xuciyata ta gaza da girman ƙaddarata, sannan ina son na haihu nima na ga sayin idaniyata, akwai ciwon da mutum zai yi dole sai jininka zai yi jinyarka."

Haka ne za ki samu haihuwa ki ci gaba da addu'a lokaci ne bai yi ba." Mommy ta ce mata cikin tausaya.
Chapter 42 · 0% Book details