Sashe 51
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon Daddy ta yi, da ya dafe ƙirji yana ƙoƙarin magana, amma ya kasa sai buɗe baki ya ke yi. Sai kuma ya yi taga-taga zai fadi. Kafin ta yi yunkurin tare shi har, ya yanke jiki ya faɗi ƙasa.
Jimmalo da take kallon su cikin mamakin maganganun da suke faɗi. Mamaki ta fara dama ɗan iska ne yake mata kallon banza? Lokaci guda ta ƙara tsanar shi, domin tun a ƙauye ta tsani ace mutum ɗan iska ne. Ba ta manta wani Tanimu da ya ke ɓata mata a ƙauye su. Da Jimmmalo ta tasa shi a gaba har sai ya bar garin, domin ita ganshi da dutse take raka shi.
Mommy da Nufaisah, suka saka ihu sosai ganin ya kice suna kira sunan shi, amma Daddy ya sume ƙau babu numfashi.
Ganin ba ya motsi, sai Mommy ta ƙwala ihu ta kira direba. Cikin sauri ya kinkime shi zuwa asibiti.
Lubaiynah
sai hankalinta ya kwanta ta ɗauki jakarta ta fice. Zuciyarta fes ta san cewa da zarar ya farfaɗo, dole zai sanya a neme ta don ya aura mata shi.
Murmushi ta saki tana gyara zaman jakanta, domin daga yau ta fara yarda Aliyu zai zamo nata. Kai tsaye gidan su Fadila ta wuce ta rungume ta.
"Na gode da kika bani shawarar nan, domin mahaifin Aliyu ya sume lokacin da na gaya masa. Sannan abin mamaki lokacin da na je, sun ga condom hankalinsu ya tashi."
"Kin ga shawarar da na gaya miki ko? Yanzu dai ki jira kira daga mahaifin Aliyu ya aura miki shi."
"Zan koma gida na zauna ina jiran kira, amma na san cewa zan fuskanci ƙalubale a gurin Aliyu."
"Kar ki damu komai zai wuce."
"Haka ne, amma ba ki ji yadda na ji ba wallahi na tsorata. Don kawai na kira shi ya ce mini yana hanya, amma da ba zan iya zuwa ba, saboda inda ace yana gidan Aliyu zai iya kashe ni."
"Ki daina jin tsoronsa, ki dake don kin san ba za ki sha ruwan daɗi ba, amma in kika jajirce za ki same shi a hannu."
"Na gode ƙawar kirki, zan kira ki da zarar mahaifin Aliyu ya kira ni."
"Ok, Allah ya tsare sannan in ya kira ki, kar kiji tsoron idanunsa ki gaya musu gaskiyar abin da ke tsakanin ku."
"Zan faɗa ai ba zan cuci kaina ba." Ta furta tare ɗaukar jakarta, ta yi mata sallama ta wuce Kano.
Mommy cikin tsanannin tashin hankali suka isa asibiti. Da sauri likitoci suka yi kansa don bashi taimakon gaggawa. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba, suka yi nasarar farfaɗo da shi.
Mommy fita ta yi daga cikin ɗakin, ta dawo harabar waje. Wayarta ta jawo, ta danna numbar Aliyu cikin tsananin ɓacin rai.
Alokacin yana Kaduna gidan Anty, suna shirya yarda tafiyar zai kasance kiran ya shigo.
Da sauri ya ɗauka ganin numbar Mommy. "Hello Mommy..." Ya kasa ƙarashe maganar jin yadda ta kira sunan shi a fusace.
"Lafiya Mommy?" Ya yi mata tambayar tare da miƙewa.
"Ba lafiya Aliyu domin ka bamu mamaki. Ma za ka dawo Kaduna ko da ace ka kai kai inda za ka je.."
"Mommy, mai ya faru?" Ya ƙara tambayarta yana mamakin abin da ya sanya ta furta haka.
"Babu abin da bai faru ba. Mahaifinka ya yanke jiki ya faɗi don haka asibiti zaka zo..."
"Innnali wa inna ilahir raju'un! Mai ya faru?" Ya ƙara tambayar, amma ba ta amsa mishi ba ta ce,"In har ka ƙara minti biyar ba ka juyo ba, sai na yi maka Alllah ya isaa nonon da na shayar da kai."
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un!" Ya furta tare da wurgi da wayar cikin tsananin tashin hankali.
"Captain mai ya faru?"Anty da tun da ya fara wayar, ganin yadda ya canza take tambayarsa.
Rintse idanunsa ya yi yana tuna kalmar da ta furta."Ban sani ba, amma koma mene ne lamari ne babba. Mommy da gaske take gaya mini za ta yi Allah ya isa ka shayar da ni da ta yi, sannan da Daddy ya sume yana asibiti." Ya furta cikin damuwa yana jin tamkar zai yi hauka.
"Ya Salam!" Ta ce jin abin da ya faɗa.Lokaci guda gabanta ya faɗi, domin ƙwaƙwalwarta ce ta hasko mata Lubaiynah ta zo, amma don kar ta ƙara tayar masa da hankali sai bata gaya masa tunanin da ta yi ba.
"Bari in je Anty Amarya, zan kira ki."
"To Allah ya sa lafiya. Don Allah da ka koma ka kira ki, dole gobe mu zo."
"Zan kira in sha Allahu." Ya furta cikin sanyi muryarsa a sanyaye.
Sharaf ta zauna tana tunanin lamarin. Dama ta san yadda yarinyar take son shi, da wuya ta zura masa ido ya yi aure. Ko da ya gaya mata zuwan da ta yi, tun lokacin hankalinta bai kwanta ba. Ta dai ƙyale shi ne ganin yadda yake ta murna.
Tun da ya fita daga ɗakinta yake gudu, ba tare da ya damu da kula da hanya ba.
Daddy a lokacin da ya farfaɗo. Ya buɗe idanunsa yana kallon saman ɗakin a hankali.
"Sannu Daddy." Mommy da Nufaisah, suka taso zuwa gadon tare da furta hakan a tare.
Ba tare da ya amsa musu ba, sai ya fara tunanin dalilin da ya suma har aka kawo shi asibiti. Lokaci guda komai ya dawo masa, har da hoton da ta nuna masa.
Daddy ya fara ƙoƙarin tashi, amma sai Mommy ta hana shi. Hawaye yake gangarowa yana jiƙa kan gadon da yake kwance. Yana kwance ya kasa cewa komai. In ya tuna abin da Aliyu yake aikatawa, sai ya ji kamar zai haɗiye zuciya ya mutu. Kullum ya yi sallah sai ya yi addu'ar; Allah ya tsare mishi yaranshi daga zina, amma sai ya zamar masa fuska biyu. Sosai yake zubar hawaye cikin tsananin ɓacin rai.
Mommy mamaki sosai take yi yadda Aliyu ya rufe shi baibai. Ashe iskanci yake yi a can, amma yake nuna masa mutumin ƙwarai ne. Tabbas Aliyu ya zama fuska biyu. Ya zama kura da fatar akuya, amma a ransa sai ya ƙudira tunda ya yi masa haka, ya ɗauki alwashin sai ya yi masa abin da zai kunyata rayuwarsa. Daddy sosai yake ji zafin abin da ya yi masa. Kula yake yi yana takaicin ɗan da ya haifa da cikinsa ya iya ije mace har yana tafiya da ita. Sai lamarin ya rinƙa ba shi mamaki, tuna har ya gama samartakarsa bai yi wannan shashancin ba.
Mommy mu ta yi zuru tana kallon sa. Duk rarrashin da take mi shi ya ƙi daina zubar hawaye. Duk da cewar ita kanta abin ya bata mamaki, amma halin da ya shiga sai ta tsorata, ganin yana son ya cutar da kansa.
Suna cikin wannan yanayin Aliyu, ya yi sallama cikin tashin hankali ya shigo."Daddy, mommy mai ya faru?"
Kallonsa suka yi domin sai ya zamo musu baƙo. Sosai yake basu tsoro zama fuska biyu da ya yi. Tun lokacin ya fara basu tsoro.
Mommy ce ta yi ƙarfin hali, ta ƙarasa gurinsa ta wanka masa mari. Kafin ya gama shanye mamakin marin Daddy ya rinƙa zuba masa masa lafiyayyu.
"Ashe dama Aliyu abin da kake aikawa kenan? Ashe yaran mutane kake ɓatawa a Abuja? Ka sa zunubin aikata zina?"
Tambayar da ya yi masa, yafi marin da yake mishi razana shi. Da sauri ya ɗago idanunsa yana kallon Daddy da yake zuba masa mari.
"Aliyu, ka cuci rayuwarka ka sanya Ubangiji yana fushi da kai! Zina da kake yi Aliyu wane irin tarbiyya ce ba mu yi maka ba?"
Sai ya ji matsanancin rashin hankali ya ƙara xiyartarsa, har ya kasa cewa komai. Tunanin yadda a yi suka sani ya fara yi.
"Lubaiynah!" Ya ji zuciyarsa ta zarge shi, sai ya ji tsannanin tashin hankali lokaci guda kansa ya fara juyawa.
"Wallahi ka bani mamaki Aliyu, ban taɓa tunanin haka daga gareka. A kodayaushe ina gayawa mutane yarona soja ne, amma kuma na gari, ashe kallon mara hankali suke mini. Duniya ta riga ta gama sanin kai mazinaci ne, tun da har mace kake ijewa a gidan...."
"Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ya furta lokaci guda idanunsa suka kaɗa, sai ya ji tamkar ya tsaga ƙasa ya shige saboda tsananin kunya.
Dama Hausawa sun ce; kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Tabbas haka ne domin ya daɗe yana sheƙe ayarsa, amma Allah ya tona asirinsa yau.
Rintse idanunsa ya yi, yana fatan ya zama mafarki, domin ji yake ba zai iya haɗa idanu da su ba. Domin ya yarda ya zama kura da fatar akuya. Sun yarda da shi, amma ya ɓata yardar da ke tsakaninsa da iyayensa.
Hawaye sosai yake yi ya durƙusa gaban Daddy."Na san cewa na yi kuskure don Allah ku yafe mini, amma wallahi na tuba tuntuni na zama na gari. Tabbas na aikata ba daidai ba, sai dai duk na daina halayena."
"Kaconka Aliyu! Ka yaudari ne domin na yi tunanin ƙaryawa za ka yi. Gaya mini za ka yi, ba ɗan da na haifa da cikina bane yake aikata zina. Na ɗauka za ka gasganta mini cewa gizo idanuna yake mini har na ga hotonka da ta nuna mini, amma Aliyu kai da kanka kake gaya mini ka aikata zina. Ina alƙawarin da ka yi mini cewar ba zaka taɓa aikata abin da wasu sojojin suke yi ba?" Ya ƙarashe maganar yana girgiza shi cikin hawaye.
Kunya, nadama da kuma tashin hankali, suka sanya shi ya sunkuyar da kanshi yana hawaye.
Murmushi mai ciwo ya yi yana kallon sa."Yadda ka aikata mini, haka sai na rama kwatankwacin abin da ka yi mini, don sai na sanya ka kuka da idanunka. Ba zan aura maka yarinyar nan ba, saboda bana son na haɗa ka aure da ita, domin za ka iya zama da ita nan gaba. So na ke zuciyarka ta yi ƙuna kamar yadda nawa take ƙuna. Ni nake da iko da kai da Safeeya wallahi ka ji na rantse a yau zan aura maka it..."
Da sauri suka ɗago idanunsu, suna kallonsa cikin tsannanin tashin hankali.