← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 52

Sashe 8

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya yi wanka, ya fito daga cikin ɗakinsa, yana duba tsaƙonnin da Lubaynah ta turo masa.

Daddy da yake zaune yana ganin ya shigo cikin falon, ya taso ya rungume shi cikin so da ƙauna.

"Son, you are welcome."

"Thanks daddy, I missed you."

"Missing you too son." Ya ce tare da zama gefensa.

"Soja mazan fama." Ya ƙara cewa suka yi dariya.

Murmushi ya yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da Nufaisah ta ƙaraso gabansu ta ce,"Dad, and Ya Aliyu food is ready."

"Ok," Ya ce mata yana kallon ta sai kuma suka miƙe zuwa dinning ɗin.

Suna cin abinci suna hira cikin ƙaruwar ɗan nasu. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Yauwa kafin ka tafi don Allah, ina son muje wani ƙauye wai shi Damagaran"

"Ƙauye kuma?" Ya yi masa tambayar yana ya mutsa fuska kamar ya ga kashi.

"Eh, ƙauye ka ji na ce. Ka san Hajiya da rikicinta. Cewa ta yi akwai wata 'yar'uwarta da aka neme ta aka rasa, sai yanxu suka samu labarinta. Shi ne take son ta je ƙauyen, ni kuma na hana ta, na ce ta bari na je na ga yanayin ƙauyen. Ka san yadda 'yan baddits suka yi yawa a ƙauyaku?"

"Haka ne daddy. Besides ni fa sam bana son abin da zai sanya na je ƙauye."

Dariya ya yi jin abin da ya ce,"Ban da abin Aliyu ƙauye ai tushen kowa ne. Duk wanda ka ga yana birni asalinsa ƙauye ne."

"I really hate village and villagers, saboda wani irin rayuwa za ka ga suna yi, musamman 'yan matansu babu wayewa da ilmi, ni fa mamaki na ke yadda 'yan matansu suke samun miji, ko da yake ai maza bagidaju suke aurensu."

"Abincin wani ai gubar wani. Waɗannan matan da kake rainawa, su ne suke sanya maza cikin wani hali in suka rasa su."

"Shashashu kamar su ba, amma ni ina namiji kamata Daddy ai duk ƙauye babu wanda zan shiga damuwa saboda ita."

"Don kawai ba a ƙauye kake bane."

"Hmmmmh!" Kawai ya ce tare da ci gaba da cin abincinsa.

"Yaushe za mu je ƙauyen?" Ya yi masa tambayar yana kai loma a bakinsa.

"Please daddy, ku je ban da ni." Ya ce masa cikin rashin kulawa.

"Dole za ka je, domin kowa a gidannan za shi har su Nufaisah da Umma."

Nufaisah ta saki murmushin jin daɗi jin abin da ya ce.

"Yauwa Daddy zan je ni ina son ƙauye, musamman kwalliyarsu dariya suke ba ni." Cewar Umma cikin farinciki.

"Duka za mu je har da mominku da auta, tun da ranar weekend za mu je."

"Ubangiji ya kaimu lokacin." Cewar Mommie tana kallonsa.

Daddy ne ya kalli Aliyu da ya haɗe rai, saboda tilasta masa zuwa Damagaran da ya yi."Aure fa Aliyu sai yaushe za ka yi?"

Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi jin abin da ya ce,"Lokaci ne da zarar ya zo zanyi ai kamar mutuwa yake."

"Shiririta kawai ka tsaya ba wai lokacin ne bai yi ba." Mommy ta furta tana kallon sa.

Jin abin da ta ce, ya ɓata ransa ba tare da yace komai ba, ya ci gaba da cin abincin.

"Ya dai kamata ya yi, saboda lokaci na gudu. In ka duba sa'anninka a Zariya duk sun yi aure har da yara. Mus'ab ɗan gidan Gwaggo Fatu aure na biyu yake nema, amma kai har yanzu ba ka fara neman na farko ba.

"In sha Allahu zan yi. Matan ne sai a hankali yanzu rashin tarbiyya da kamun ka ya yi musu yawa, dole na tsaya na natsu na samu mace ta gari wacce zata bawa yarana tarbiya.." Ya ce musu yana kallonsu.

"Haka ne ka yi tunani mai kyau amma duk wayonka, da ƙoƙarin zaɓar mace ta gari, dole sai ka haɗa da addu'a, saboda kamar yadda maza ba a ƙwanƙwansawa haka su ma matan. Shi ya sa ake son mutum ya zama na gari, sai Allah ya duba ya ba ka mace ta gari mai irin halinka."

Jin abin da ya ce sai gaban shi ya faɗi. Tunani ya yi halinsa, nan take ya ji ya ƙara tsanar tarayyarsa da Lubaynah.

Duk yadda captain Aliyu ya kaucewa zuwa ƙauye Damagaran, amma bai ci nasara ba, domin kwana biyar da dawowarsa, Daddy ya shirya sha tara na arziki suka tafi.

A ranar da za su tafi ransa a ɓaci yake. Ya shiga cikin motar yana kallon ƙasa fuskarsa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Daddy yana lura da shi, amma bai ce masa komai ba, har suka fara tafiya.

Sun yi nisa yana zaune yana kallon hanya, har suka fara shiga cikin ƙauyuka. Ƙaramin tsuka ya ja, saboda yadda motar take ta bugawa da duwatsu tana tsalle kamar za ta kife.

"Kai gaskiya ba zan iya tuƙa motarta na shiga ƙauye ba, domin asara kawai zan yi. Haba, ya kamata a ace an samu cigaba an gyara musu titin su."

"Laifin gwamnati ne ba ta kula da rayuwarsu ba."

Tsaki ya ja ba tare da ya ce komai ba, ya zaro wayarsa ya zai kunna data. Haushi ya sa shi jefar da wayar kan cinyarsa ganin network ya ɗauke.

Gabakiɗayan su sun gaji da zaman, Captain Aliyu ya kalli Daddy da yake kallon hanya.

"Da wannan nisan Hajiya take son ta zo ƙauyen nan?"

"Don na hanata da tare za mu taho."

"Aiko da tasha baƙar wuya, saboda da na san haka zamu zaunu a hanya, babu abin da zai sa na zo."

"Wallahi ni kaina na gaji so na ke na huta." Mommy ta ce tana gyara zama.

Nufaisah da Umma da auta duk bacci suke yi.

Sun shigo cikin ƙauyen motarsu ta lalace. Fitowa suka yi cikin damuwa, suka tsaya suna kallon direba da yake ta ƙoƙarin gyara motar.

"Alhaji, ruwa ne ya yi ƙaranci a motar dole na je tafi na samo." Ya ce masa yana kallonsa tare da buɗe Boot ya ɗauki jarka.

"Na gaya maka ka rinƙa kula, ka tabbatar da ka duba ruwa da mai, saboda mu kiyaye ɓata lokaci."

"Sai da na yi hakan kasan ƙarfe nasara."

Shiru ya yi, ba tare da ya ce komai ba cikin takaici. Ganin haka ya sa shi fara tafiya don ya samo ruwan.

"Karo na farko da na je ƙauye kuma na tsani zuwa." Ya ce tare da dukan bayan motar.

Babu wanda ya tanka masa domin su kansu a gajiye suke.

Fara taku ya yi, yana kallon dajin da yake ɗauke da kayan lambu. Kamar su mangwaro, kashu, gwaiba, da malmo.

Tsintar kansa da son ganin dajin ya yi, saboda shi mutum ne mai tsananin son shuke-shuke, domin duk shukar dake cikin gidansu shi ya shukata.

Bishiyar mangaro ya ƙarasa, yana kallon yadda suka girma suka yi jajir. Ba sha zai yi ba, kalan mangwaron ya burge shi.

Yana ta kallon mangwaron cikin sha'awa, yana tunanin in ya koma sai ya nemi kalarta. Wayarsa ya ɗauki zai ɗauki hoton.

Daga saman bishiyar kuwa, Jimmalo ce zaune tana ta shan mangaro. Tun da Kaka Tani ta aike ta, ta je gidan ba ta nan, sai kawai ta taho nan tasha mangwaro. Duk cikin mangwaron ƙauyen babu wanda take so sai ita.

Tana cikin sha, ta kama reshe ta yi ɗare-dare sai ta kalli ƙasa.

Da sauri ta kama bishiyar tana salati don saura ƙiris ta rikito.

"Wa innahu sulaimanu.Tuf-tuf." Ta ce cikin tsananin razana tare da ƙwala ƙara.

"Wayyo na yi gamo da Balaraben aljani." Ta furta tana zare ido, saboda tsananin kyansa ya firgita ta. Sam ba ta yi tunanin shi mutum bane, saboda ba ta taɓa kawo cewar mutum mai kyau kamarsa zai iya zuwa ƙauyen ba.

Captain Aliyu, da yake ɗaukar hoton mangwaron sam bai ji ihu ta ba, saboda tazarar da ke tsakaninsu.

Yana shirin juyawa, daidai lokacin daidai lokacin da ta furta a ranta.

"Wannan aljanin sam kar ya tsorata ki Jimmalo, domin kin sha tabaraka kin sha yasin. Ki tsorata shi kawai ya bar gurin ki gudu."

Ga mamaki sai ta ji ta fara rage tsoron. Mangwaro ta tsinko wace ta nuna. Da sauri ta sanya hannu ta ligwigwitata, sannan ta saita shi ta maka masa aka.

Cikin tsoro ya ɗaya kansa yana kallon sama, sai kuma ya kalli kansa ganin yadda farar shaddarsa ta lalace, saboda mangwaron ta fashe duk a jikinsa.

Tsoro ya kama shi yana zare ido yana kuma kallon sama

Ganin yadda ya ruɗe sai ta saki dariya tana faɗin,"Shegu aljanu ashe suna tsoron bil'adama." Ta ce tare da tsinko mangwaron har uku ta ƙara kwaɗa masa aka.

Zafi da takaicin yadda kayansa ya ɓaci suka tunzura shi.

"Ko da ace aljani ne yake jifa na da mangwaron nan, wallahi sai na yi maganinsa." Ya ƙarashe maganar yana kallon kayansa cikin takaici.

Ganin yana kallon bishiyar kuma zai iya hangenta, sai kawai ta fara girgiza bishiyar tana kukan jaki.

Da sauri ya bar gurin cikin tsoro. Dakewa ya yi, amma zuciyarsa ta razana.

"Lafiya Aliyu, mai ya faru da kayanka?"

"Please mu bar gurin nan, akwai aljanu a gurin."

Yadda ya yi maganar ya ƙara tsorata kansa, kuma ya tsorata su.

"Mun shiga uku! Mu bar gurin don Allah." Cewar Nufaisah tana kuka saboda tana da tsoron aljanu.

Bayan Mommy ta ɓoye, don gani take aljanin sun shiga jikinsa yadda yake zare ido.

"Don Allah, mu bar dajin nan, in motar ta ƙi gyaruwa sai ya gyara ya kawo."

"Ku shiga cikin mota in sha Allahu za ta tashi." Direba ya ce yana kallonsu yadda suka firgice.

Cikin sa'a yana kunna motar ta tashi. Da sauri suka shiga ya fara tafiya. Da tarin gajiyar da suke ɗauke da shi, da kuma tsoro ya sa babu wanda ya ce uffan, har suka ƙarasa cikin ƙauyen.

Gidan maigari suka isa, tare da yi musu kwatancen gidan da suke nema. Maigari ya cika da mamaki jin sun ambaci Tani. Tsananin mamaki ya kama shi ganin mutane 'yan birni kyawawa suna nemansu.

"Aminu," Ya yi kiran ɗaya daga cikin ɗansa.

"Na'am," Ya amsa tare da ƙarasowa yana kallonsu kamar zai cinye su.

"Ma za ka nuna musu gidan Tani, kuma kar ka sake ka shiga gidan, ka dai san halin yarinyar nan."
Chapter 8 · 0% Book details