← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 52

Sashe 30

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 15

Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun, sai ta kasa tafiya ganin halin da take ciki.

"Wash! Jimmalo, mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi, hawaye yana zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo.

Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma.

"Shekaranjiya ne kuma na bata bauri."

"Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula da magunguna."

"Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi ki barni?" Sai hawaye shar ganin yadda take nishi da ƙyar.

Tana zaune a gefenta tana ta share hawaye. A maimakon jiki ya yi sauki sai ya ƙara zafi, domin har jijjiga take yi jikinta kamar tukubar mai tsire. Ganin haka hankalinta ya tashi sosai, ta koma ta kira Audi mai kyamis

"Jimmalo, akai Kakarki birni gaskiya ciwonta ya fi karfin kulawata."

"Wayyo na shiga uku!" Ta furta tare da kamo ta tana hawaye.

"Bari na kira miki abokina Tanimu ya kaiku. Na bar shi a shagona yana cin abinci zai je birni." Ya ƙarashe maganar tare da ciro wayarsa Tecno mai botira.

Bayan ya kira shi ya sanya ta shirya mata kaya. Jimmmalo tana shirin kayan tana hawaye, ganin yadda ta koma. Tunawa da shekaranjiya suna zaune suna hira cikin raha.

Da sauri ta yarda kayan, da ta fito za ta sanya mata ganin idanunta na ƙafewa." Kaka Tani! Ba mutuwa zaki yi ki barni a duniya ni kaɗai ba?" Ta yi mata tambaya tare da fashewa da kuka.

Ganin halin da take ciki na tsananin wuya, sai Audi mai kyamis ya kama hannunta yana dubawa, can kuma ya sauke hannunta ya fara ƙoƙarin kamata zuwa keke napep.

"Don Allah kar ku kai ni ko ina saboda mutuwa zan yi. " Kaka Tani ta furta cikin murya mai rauni.

"Ba za ki mutu ba Kaka Tani! In kika mutu ki barni da wa a cikin duniyar nan? Ke ce wacce na rayu da ita kuma na ke ƙauna."

"Jimmalo, ki yi haƙuri lokacina ya yi, saboda wannan ciwon ba na jin zan tash.."

"Na shiga uku!" Ta furta tare da sakin kuka ta ƙara rungumeta.

"Kaka Tani don Allah kar ki mutu ki bar ni. Ki bari har na yi aure ki ga jikarki. Kaka Tani zan so Bala mu yi aure in har ba za ki mutu ki bar n..."

Innar Salame ta kalle ta ta ce,"Lokaci ya ƙure Jimmalo, Kakarki Allah ya aiko mata da mala'ikan da gaggawa. Halin yanzu ki bari mu maimaita mata kalmar shahada in tana da rabo ta yi." Ta ƙarashe maganar tare da janyeta daga jikinta.

"Wayyo Allah Kakata. Don Allah kar ku bari ta mutu ku taimaka mini." Jimmalo tace tana ihu sosai, ganin halin da take ciki.

Audi mai kyamis ya duƙa kusa da ita, yana maimaita mata kalmar shahada.

"Jimmalo, ina son na yi magana da ita." Ta furta tana jin kukanta har cikin zuciyarta, amma babu abin da za ta iya, saboda ga ta yau a kwance tana ciwon ajalin da za ta bar ta ita kaɗai, a cikin duniya ba tare da ta san mai zai faru nan gaba a cikin rayuwarta ba.

"Kakata ina jin ki gani a kusa da ke, don Allah ki gaya mini ba mutuwa za ki yi ba na yi shiru?" Ta ce tare da kama hannunta ta ɗora a fuskarta.

"Jimmalo, a yau zan tafi na barki a cikin rayuwar da na ɓata tarbiyarki. Kalaman da Hajiya ta gaya mini tabbas haka ne. Na cuce ki saboda son da na ke miki ban ba ki tarbiya ba. Na san cewa ko na mutu babu wanda zai ɗauke ki, har su Hajiya ba za su ɗauke ki ba, amma Jimmalo in har suka yafe abin da muka yi musu su ka zo gareki, ki tafi birni ki canza rayuwar..."

"Kaka Tani babu inda za ni ina nan tare dake, in kuma kin mutu zan koma da rayuwata a ƙabarin da aka birne ki, saboda ba zan iya rayuwa babu ke a cikin duniyar nan ba."

Kaka Tani ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fara tari tana jijjiga. Kafin kace me ta fita hayyacinta har idanunta sun fara rufewa. Ganin haka hankalin Jimmalo ya kira tashi. Kuka take tana ihu tana zambarwa ganin za ta mutu ta barta.

Audi mai kyamis ya rufe mata idanu, lokaci da ya fahimci ta cika, bayan ta amsa kalmar shahada sau ɗaya.

"Allah ya jiƙanki Tani." Jin abin da Innar Salame ta furta tana share hawaye, sai kawai ta yi wani irin ƙara ta zube a gurin.

Ruwa aka sanya mata ta farfaɗo, ta rungume gawar Kaka Tani tana wani irin kuka. Gani take kamar ba ta mutu ba, saboda ba ta taɓa ganin mutuwa ba. Gani take kamar za ta tashi su ci gaba da rayuwa, don haka ta rungumeta ta hana kowa ya taɓa ta.

"Jimmalo Tani ta rasu ki matsa mutane su fara mata wanka don a kaita gidan gaskiya."

Idanunta ta ɗago da suka yi jajir jina bin da Innar Salame ta ce. "Babu in da zan yarda a kai mini Kakata, wacce ita kaɗai na sani kuma na yi rayuwa da ita. In na bari kuka kaita ƙabari ni kuma na rayu da wane? Kaka Tani ba za ta mutu ba, saboda ta gaya mini sai ta ga jikokiina. So kuke ku raba mu saboda ku samu damar da za ku rama rashin mutuncin da na yi muku." Ta ƙarashe maganar tare da ƙanƙame gawarta tana faɗin,"Kaka Tani kin ga azzaluman mutanen nan so suke su raba mu. Kaka Tani ki tashi daga baccin ki gaya musu ba ki mutu ba." Jijjiga ta take yi tana faɗin haka cikin kuka.

Tun suna sanya ran za ta bari ayi wa gawar sutura har suka cire. Da ƙyar aka samu maza majiya ƙarfi huɗu suka rabata da gawar, sannan aka fara mata wanka don a kaita gidan gaskiya.

Jimmmalo, tun da ta ga da gaske za su raba da ita ta cika ƙauyen da ihu tana ƙaraji, domin ta san cewa rayuwarta ta shiga garari In har babu Kaka Tani a duniya. Wa zai rinƙa tare mata tsiwa kuma ta rinƙa hira da ita? Jin Kaka Tani take ko iyayen da suka haifeta albarka, tun da ba ta yi rayuwa da su ba. Tun lokacin da ta mallaki hankalin kanta ita kaɗai take gani kuma ita ce duniyarta. Saboda mutuwa dare ta yi domin a lokaci har an kira sallar magariba duhu ya yi, kan dole za ta yi kwanan keso da safe a kaita.

Jimmalo kasa bacci ta yi, har lokaci gani take bacci take yi. A kusa da ita ta kwana sai Innar Salame da kuma wata tsohuwa ƙawar Kaka Tani. Daren ranar Jimmalo ta kira shi a baƙin dare, saboda ba ta yi bacci ba tana ta jijjiga ta tana kiran sunanta, a haka ta kwana har gari ya waye aka fara shirin kaita.

Tana cikin wannan halin da take ganin kamar duk a mafarki ne, aka yi mata sutura aka kira ta don ta yi mata addu'a a kaita makwancinta. A nan ta zama mahaukaciyar domin ƙaton icce ta ɗauka, ta tsaya kan gawar duk wanda ya zo sai ta kai mishi duka.

"Babu wanda zai raba ni da Kakata. Ashe ƙiyayyar da kuke mini ta kai haka? Har zaku iya cewa Kakata ta mutu, don kawai ta warke ta samu dogon bacci?" Duƙawa ta yi kusa da ita ta shafa fuskarta.

"Kaka Tani ki yi bacci ki tashi, ina gadinki babu wanda zai kai mini ke rami." Ta ce tana kallon ta sai kuma ta kalle su ta ɗora da cewa,"Kun gani murmushi take mini."

Tsanannin tausayinta ya cika zuciyarsu, domin sun san dole hakan ya faru. Kaka Tani da tambayar da kanta ƙaramar yarinya take biyewa duk abin da ta yi.

Kaduna.
Cikin dare Hajiya ta kasa bacci, sai mugayen mafarkai take yi. Hankalinta ya tashi sosai da ta farka ta kasa bacci. Tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a ta yi sosai tana fatan mafarkin da ta yi ya zamar mata alkhairi.

Da ƙyar ta samu ta koma bacci, sai dai kwanciyarta ke da wuya ta yi mafarkin Kaka Tani. Cikin firgici ta farka tana yin duk addu'ar da ta fito daga bakinta. Tun da ta yi mafarkin sai ta kasa komawa. Zama ta yi kan tsakiyar gadon tana tunanin mafarkin da ta yi.
Chapter 30 · 0% Book details