← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 52

Sashe 48

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun da ba zaki gaya mini ba, sai na gaya wa mutanen gidan."Ta ƙarashe maganar tare da wage baki za ta yi ihu

Da sauri ta toshe mata baki ta ce."Ba fa kisa zan yi ba. Ni musulma ce da imani."

"To me kike sawa a abincin!" Ta jefa mata tambayar.

"Abincin Ya Aliyu ne kuma ma...."

"Kashe shi za ki yi? In har kashe shi za ki yi ba zan damu ba, domin babu amfanin rayuwar mugu azzalimi." Ta furta abin da Mufida ta karanta har cikin zuciyarta, wanda ya sanya ta ce,"Eh, ka.sh..e shi zan yi saboda kamar yadda yake miki mugunta haka ya yi mini."

"To me kike jira ki sanya masa maganin da yawa, yadda da yaci zai fara shure-shure, domin na tsane sa da zan samu dama zan iya kashe shi." Ta furta tare da rufe mata kofar cikin farinciki.

Mufida sai ta cika da mamaki sosai jin bin da ta ce. A yadda ta nuna a fuskarta da gaske ba za ta gaya wa kowa ba. Mamaki sosai na tsanar da suke wa junansu. Cikin kwanciyar hankali ta saka maganin ta ɗauka.

Gabanta na dukan tara-tara ta kwanƙwasa ƙofarsa. A tunaninsa Umma ce don haka ya ce,"Yes, come in."

Yana zaune daga shi sai gajeren wando babu riga. Gefensa abokinsa Imran yana danna wayarsu suna hira.

Ɗaurewa ta yi ta shigo. Ganin yadda yake sai jikinta ya kama rawa ta kasa ƙarasawa.

Captain Aliyu yana kallon wayarwa ya ce,"Umma, ije Allah ya sa kin zuba da yawa, na manta na ce miki ina tare da Imran, duk da ba da...." Maganar ta maƙale masa lokacin da ya ɗago ya ga Mufida ce.

"Ke! Are You stupid?" Ya ce mata tare da miƙewa yana zare mata idanu.

Ganin yadda ya daka mata tsawa sai ta ije abincin ta fice da sauri.

Tsaki ya yi ya zauna."Yarinyar nan ba ta da hankali, amma zan koya mata." Ya ce yana hararar abincin.

"Hmmmmh. In dai ka ga kare na shinshinan takalmi dauka zai yi." Ya ce tare da jawo abincin ya fara ci.

"Ashe kuwa iska na wahalar da mai kayan ƙara." Ya furta tare da komawa ya zauna, ba tare da ya kalli abincinba domin ya fita ransa.

Imran ya ci abincin sannan ya tashi ya tafi. Bayan ya raka shi ya kira Umma ta kwashe kwanukan.

Mufida,cikin fargabar kar su ci abincin su biyu ta fice daga ɗakin. Duk yadda ta damu da ta sanya maganin, amma xuciyarta ba ta yi farinciki da samun nasarar sakawa da ta yi ba.

Falo ta dawo ta zauna, xuciyarta cike da tsoron kar Jimmalo ta gaya musu, amma sai ta ga babu abin da ya dame ta, sai kallonta da take yi, so take tambaye ta ko ta sanya.

Fuska ta daure ta mayar da hankalinta kan tibi, amma sai da ta san yadda ta faki idanun mutane ta koma gefenta ta zauna cikin raɗa ta ce,"Kin sanya mishi?"

Duk da raɗa ta yi mata, sai da ta zare idanunta tana kallon mutanen falon. Ganin hankalinsu bashi a kansu sai ta kalle ta da tayi mata ƙuri, xuciyarta na addu'ar Allah ya sanya ya mutu a yau.

"Eh na sanya maganin amma a hankali zai shiga jikinsa."

"Da kin sani wanda zai ci nan take ya fara shure-shure kika siya." Ta furta xuciyarta a ƙuntace ta koma gurinta ta zauna.

Hamdala ta yi, tare da sauke ajiyar zuciya ganin ta koma gurin da take zaune, a xuciyarta mamaki take yi domin Jimmalo ta wuce a kira ta mahaukaciya.

Da safe bayan sun karya suka fara shirin komawa. Tun da Jimmmalo ta fahimci hakan, sai ta fara haɗa kayanta ta kafe kan dole tare za su tafi. Nan fa aka shiga dirama musamman a lokacin da suka fito. Duk rarrashin da ta yi mata ta kafe kan dokin na ƙi.

Da ƙyar Anty Amarya, ta samu ta shawo kanta bayan ta yi mata alƙawarin da zarar sun yi hutu za ta kira a kawo ta yi hutu. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta domin har xuciyarta take ƙaunarta. Ita ma rungume ta tayi tana jin tausayinta don jinta take yi kamar Surfy ƙanwarta da suka fito ciki ɗaya.

Tana rarrashinta rungume da juna, a haka Aliyu ya fito da makullin mota yana karkaɗawa. Yayi kyau sosai, domin in har da abin da yafi kyau za a iya fasalta shi da shi.

Kasancewar in ya kaisu Kaduna zai wuce Abuja, sai ya shirya cikin kayan sojoji. Kayan sun yi masa matuƙar kyawu sosai. Yana riƙe da wayarsa, da makullin mota sai glass ɗinsa da yake ƙoƙarin sanya wa.

Ganin su a haka ya dakata tare da daka wa Jimmalo tsawa."Haba Anty! Wannan kucakar yarinyar za ki bari ta shiga jikinki? In har kina son mu shirya gaskiya ki daina kula ta." Ya furta tare da watsa mata mugun kallo yana bata fuska.

Sakin juna suka yi Jimmalo ta watsa masa mugun kallo."Anty Amarya, don Allah kar ki manta alƙawarin ki?" Ta ce tana share hawaye.

Murmushi ta yi tare da ɗauke mata hawayen ta ce,"Ba zan manta ba 'yar ƙanwata, amma ki tuna na gaya miki kar ki rinƙa sanya wa Mommy damuwa?"

"To," Ta furta a sanyaye.

Tsaki ya saki ya shiga cikin motar, tare da sakin musu hon babu ƙaukautawa.

Mufida da Hanifa, a lokacin da ya fito da suka bi shi da kallo tamkar sabbin mayu. Ko wacce tana fatan ina ma ace wannan mamallakin surar ya zamo mallakinta.

Jimmalo da Mommy suna tsaye har ya fara tuƙa motar. Mommy sosai take musu addu'ar isa lafiya har suka fice.

Mommy sai ta kalle ta ganin yadda ta sha kunu. Xuciyarta cike da tsoron kar ta koma gidan jiya.

Jimmalo bayan tafiyarsu ta shiga damuwa sosai. Haka ta wuni suku-suku har dare.

Daddy hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya tabbatar da Principal ya haƙura sannan ya kaita makarantar da kansa, bayan ya yi mata kashedi sosai. Ba ta tanka ba ballantana ya sa ran ta ji.

Haka ta ci gaba da zuwa duk da xuciyarta ba ta so, amma babu yadda za ta yi. Addu'arta kullum lokaci yayi ta je gidan Anty Amarya.

Captain Aliyu ya so su je a kwanakin da ya so, amma sai kuma aiki ya riƙe shi wanda kan dole ya bar zuwa ƙarshen wata.

Lubaiynah
kamar yadda suka tsara shirin su. Sau biyu tana zuwa gidansa, amma Solo ya hana ta shiga. A na ukun sai ta je gidan Kalim. Bayan sun gaisa Kalim ya sanar da ita ta yi haƙuri sam Captain ba zai aure ta ba.

Mamakin mugun son kansu ya kamata. Wato su lalata mace sannan su ƙyama ce ta, domin tun da Captain ya yi mata hakan shi ma ba zai ƙi yasar da budurwarsa a bola ba. Sai ta rinƙa kallon sa kawai.

"Eh, ni ma na haƙura da shi, saboda na ga sam ba zai aure ni ba. Yanzu ma na zo ne na gaya masa na samu miji zan yi aure."

Jin abin da ta ce sai Kalim ya ce,"Yauwa da kyau. Gara da kika cire zuciyarki ga wanda ba ya ƙaunarki. Shi ma Captain In sha Allahu Ya kusa aure, domin ya sanar mini ya samu matar aure."

Lubaiynah, ba ƙaramin ƙoƙari ta yi da ta ɓoye tashin hankalinta ba. Ji ta yi tamkar sama da ƙasa za su faɗo mata. Sai xuciyarta ta ƙara gasgata mata captain ba ya ƙaunarta, domin za ta iya sanya shi a cikin maƙiyinta na ajin farko. Bayan ya lalata rayuwarta ya kawar da abin da ko wace mace take tutiya da shi. Sannan zai je ya auri wata mace. Sai ta ji xuciyarta na bugawa da sauri, har ta ji ba za ta iya jure tashin hankalin da take ci ba, domin in har ta tsaya Kalim zai fahimci tuban maxuru ta yi, sannan ya gane da wata manufa ta zo.

"Masha Allah! Allah ya tabbata da alkhari. I want to use the restroom." Ta yi ƙoƙarin sanya dakiya a xuciyarta ta furta hakan cikin rawar murya.

Duk yadda ta so ta daure, amma sai da ya fahimci halin da take ciki. Sosai ya tausaya mata ganin yadda lokaci guda fuskarta ta canza.

"Amin, You can go in." Ya ce mata yana nuna mata hayar bayin.

Murmushin yaƙe ta yi tare da miƙewa ta ce,"Thanks." Sai ta wuce cikin sanyin jiki. Kafin ta shiga cikin bayin ta ji hawayen da take ƙoƙarin mayar wa sun zubo a kuncinta.

Tana shiga ta fashe da kuka sosai. Anya akwai wanda ya kai Captain zalunci kuwa? Ta ya ya zai yi mata haka? Ko da ace bai keta haddinta ba, ba ta iya jin za ta iya barin ma wata 'ya mace shi, ballantana ya kwashe abin da yake da daraja da ƙima a rayuwata.

Gudun kar Kalim fahimci kuka ta yi sai ta yi ƙoƙarin tsaida kukan. Ta wanke fuskarta da ta ci sa'a ba wata kwalliya ta yi mata ba da za ta fito.

Kalim, da hankalinsa yake kan wayarsa, jin ta buɗe ƙofa sai ya kalleta.

"Are You ready?"

"Yes," Iya abin da ta iya furta masa kenan.

Tafiya suke yi, amma babu wanda yake wa juna magana. Ko da ace yana mata sam ba za ta ji shi ba, domin xuciyarta ta yi balaguron yadda za ta rama abin da ya yi mata.

Kalim ganin halin da ta shiga sai ta ba shi tausayi. Ya san cewa dole za ta yi kishi.

Captain Aliyu zaune kan dinning yana cin abinci. Ya ga kiran Captain Kalim. Ba tare da tunanin tare yake da Lubaiyna ba, sai ya miƙe ya buɗe masa ƙofa.

Yana tsaye da ga shi sai gajeren wando. Duk halittun da sun bayyana waje. Ganin Lubaynah sai ranshi ya ɓaci ya tokare ƙofa.

"Saboda me za ka shigo mini da ita?" Tambayar da ya yi masa, sai ya shanye mamakin tokare ƙofa da ya yi.
Chapter 48 · 0% Book details