Sashe 32
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 16
"Ni ce zan koma birni, Saboda me? Na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan, domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta mutu."
Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu.
"Jimmalo, ki ji tsoron Allah! Bana tsafi ko maitar da zan cinye 'yar'uwata." Hajiya ta faɗa cikin muryar kuka.
Harara ta banka mata ta ce,"Ban yarda ba, saboda ko qur'ani za ki bani zan dafa ku kuka kashe mini Kakata."
Daddy kuwa kasa magana ya yi jin sharrin da ta yi musu.
"Magana ta ƙare ko cinye ki za su yi, kin san Allah sai kin bar ƙauyen nan. Dama albarkacin Tani kike ci, amma yanzu wallahi ba za mu barki a ƙuyennnan ba, in kuma kika kuskura kika zauna, duk rashin mutuncin da kika yi sai mun yi miki na jaki."
"Dallah malam Jatau, ka fita idanuna kai ne za a ce ka bar ƙauyen nan, tun da ba ka da gidan kanka haya kake yi. Ni kuwa ina da gidan da Kakata ta bar mini zama daram ɗan karo kawai."
Yadda ta yi maganar, ya tabbatar wa mutane mutuwar Kaka Tani bai canza ta ba.
"Ke Jimmalo wace irin ɗiya ce mara tarbiyya? Wannan tsohon kike wa rashin ɗa'a? Wato mutuwar Kakarki bai zamar miki aya ba?"
"Au dama kun yi tunanin mutuwarta, zai sanya na kwanta sai ku taka ni yadda kuka ga dama ko? To yanzu ne zan nuna muku kalata, don wallahi ko yatsa mutum ya nuna mini sai na karya, saboda babu Kaka Tani dole na miƙe na ƙwaci kaina."
"Tab ashe har yanzu rayuwarki da saura." Cewar Kallah yana mamakinta.
"Ke Jimmalo zauna!" Maigari ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Gungunan ta yi sannan ta zauna a ɗofane. Kallon su take yi tana ganin duk azzalumai ne, sai kuma ta fara hawaye tuna da yanzu tana bayan kaka Tani tana kare ta.
"Yan birni kun ji wasiyar 'yar'uwarku? Kun dai san babu kyau mamaci ya yi wasiyya ba a cika masa ba, don haka ya kamata ku cika ku ɗauki wannan guyababbar yarinyar mu samu sauƙi a cikin ƙauyen nan, saboda mutuwar kakarta kamar wasu kalar rashin mutunci ta fito da su."
"Ni fa ko mai za a ce ba zan bar ƙauyen nan ba, kuma duk wanda ya takale ni wallahi sai na yi mishi wankin babban bargo ko da gemunsa na jan ƙasa ne." Ta ce tana jijjiga.
Daddy da Hajiya suka ɗago kai suka kalle ta cikin sanyin jiki. Hajiya tsoro ta fara bata. Wato suna son su raba kansu da masifa su jajiba musu? To amma ya za su yi tunna sune 'yan'uwanta kuma har ta bar wasiyya. Ta gane kuskuren ta na irin tarbiyar da ta ɗora ta har ta bar wasiyar a gyara rayuwarta. To ta ina za su fara da yarinyar da bata ganin kowa da gashi, sannan ba ta da tsoro idanunta a tsaye suke? Irin wannan tarin tambayoyin ya cika zuciyar Hajiya da Daddy.
"Eh za mu tafi da ita a sayar da gidan nata, sai a bani zan koma birni yau." Daddy ya ce yana kallon maigari.
"Sayar da gida ba mai wahala bane, don ko ni yanzu zan siya, in har za ku bar mana garin da wannan ja'irar yarinyar."
"Na rantse, in har ka sayi gidan nan sai mun rinƙa muku fatalwa ni da Kaka Tani. Wayyo Kakata ki taso daga ƙabari ki ga maigari zai sayi gidanmu." Ta ce tana kuka sai ta miƙe tana zare ido.
Tana gani aka kira dillalai aka sigar da gidan. Daddy ya bayar da kyautar kayan gidan yana shirin raba kayan Kaka Tani ta riƙe akwatin."Na rantse ba wanda za a ba kayan nan. Su zan rinƙa sanyawa na tuna da Kaka Tani."
Zare idanunsu suka yi suna kallonta."Kayan tsohuwa za ki saka kina yarinya? Ki bari muje birni zan siya miki wasu."
"Allah ya kyauta an gaya muku zan biku birni ne? Ni ma ku je ku yi tsafi da ni, bayan kun gama da Kakata. Ina nan ƙauye ko a kusa da ƙabarin Kakata na yi rayuwa."
Kasa cewa komai suka yi, suna tunanin yadda za su sanya ta a mota. "Yarinyar nan fa in har ba ɗaure ta aka yi ba, sam ba za ta biku ba, saboda in kuka shigar da ita haka za ta iya ja muku hatsari ba ta da tsoro." Maigari ya furta yana kallonsu.
"Sai a ɗaure mutum da ransa?" Hajiya ta yi tambayar cikin mamaki.
"Wannan ne mafitar da za mu iya tafiya da ita birni, saboda in har ba haka aka yi ba wallahi ba za ta bimu ba." Cewar Daddy yana kallonta da take tsaye, tana girgiza tana aika musu da harara.
"To shikenan, amma kar a yi mata ɗaurin da zai cutar da ita." Ta furta tana kallon Daddy.
Maigari da Daddy, ba su tanka mata ba ya wuce ya samo majiya karfi da igiyar. Saboda shegen wayonta sai ta fahimci abin da suke nufi. Rugawa ta yi da gudu suka bita. Ba su kamata ba sai da suka wahala sosai, sannan suka yi nasarar kamata bayan 'yan ƙauyen sun taimaka musu, domin kowa murna yake za ta bar ƙauyen. Samun sa'a ta yi ta yankawa Sa'adu cizo a hannunsa. Cikin tsananin azaba ya saketa yana ihu. Ƙoƙarin guduwa ta fara suka ɗauke ta. Da ƙyar suka haɗa hannunta da ƙafafunta
Ɗaureta suka yi, tana ihu tana zaginsu domin har maigari sai da ya samu na shi rabon na bankwana. Gabakiɗaya ƙauyen babu wanda ba ta yi jam'i ba ta zaga.
Haka suka kamata tana ihu tana kuka, tana kiran sunan Kaka Tani. Sai kuma ta kalli Salame da jikinta ya yi sanyi sosai."Kina gani za a raba ni da ƙauyen da na taso na yi rayuwa? Salame yau zan rabu da ku ba za ki zo ki cece ni ba? Mutanen birnin nan 'yan shan jini ne, saboda su suka shanye jinin Kaka Tani da kuɗin jini suke rayuwa, ba ki ga daular da suke ciki ba. Wayyo ki taimaka mini."
Kawai sai Salame ta fashe da kuka sosai take jin tausayinta da kewarta. Ta san cewa daga yau za su rabu. Jimmalo zata koma wata kalar rayuwa, domin ba lallai su yarda ta ci gaba da rayuwar da Kaka Tani ta ɗora ta a kai ba. Rayuwarta daga yanzu must be hard on her. Sun tashi tare sun yi faɗa sun yi dambe, domin duk lokacin da zasu haɗu sai Jimmmalo ta takali mutum, tun da ta san cewa ita ce ke da nasara. Duk dacewar ta girmi Salame, amma ba wasu shekaru can masu yawa ba. Sosai take kuka tana gani aka sanya a bayan mota.
"Don Allah ku ɗauki mini kayan Kaka Tani na rinƙa sanyawa na tuna ta." Tace cikin kuka.
"Don Allah ku ɗauko mata ina har za ta yi shiru." Hajiya tace tana kallon Daddy.
"Hajiya kayan tsohuwa za a bata wane irin rayuwa zata yi a birni? Da shigar tsofaffi mutane dariya za a rinƙa mata."
"Don Allah a ɗauko mata, in muka je birni na san yadda zan yi mu raba ta da kayan, amma yanzu in ba a bata ba, haka za ta yi ta kuka muna bin gari da ita. Kar a ɗauka sato ta muka yi."
"Shikenan a ɗauko mata." Ya ce tare da shiga cikin gaban motar.
Ganin an ɗauko kayan, an sanya mata a inda take kwance sai ta ɗan rage kukan. Ta yi ƙoƙarin ta kalli glass ɗin windon ta ce,"Allah ya tsine wa duk mutanen ƙauyen nan, tun da bakwa sona kuma gani za a tafi da ni Birni a shanye jinina, kamar yadda aka shanye na Kaka Tani. Kuma na rantse ina samu na kufto sai na dawo na cinnawa ƙauyen nan wuta duk kun mutu na yi rayuwata ni kaɗai." Sallamar data yi musu kenan, lokacin da motar ta tashi ta ci gaba da kuka.
"Alhamdulillah! Yau Allah ya kawo mana ƙarshen annobar kauyen nan. Jimmalo ta bar mana ƙauye can gasu gada..." Maigari ya furta yana daga kirjinsa cikin murna, domin daga yau ya daina alƙalanci kullum, saboda a ƙalla a rana ba a kawo masa ƙararta sai biyu ko uku ba, har fargabar gari ya waye yake yi ya shiga faɗa.
Saboda ihun da take musu, Daddy har da gudun tsiya ya haɗa don ya samu ya iso Kaduna. Gabakiɗaya ta sanya kishi gajiya, burinsa kawai ya isa gidan Hajiya ya je gidanta sha magani ya kwanta, saboda wani irin azzabben ciwon kai yake ji.