Sashe 45
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai Aliyu ba zai zo gidanmu ba, kuma kin san irin abin da zuwansa zai yi. Mahaifina ba zai zura masa idanu ba."
"Haka ne amma ni shawarata, ki fara nuna masa kin tuba ku yi zumunci kawai, sannan sai ki je gidansa wannan jakar da kika ce mini in zai je gidan iyayensa yake tafiya da ita, kuma ba ya canzawa sai ki samu ki sanya masa kwalin condom a ciki."
Shiru ta yi don ba ta ga amfanin gurguwar shawararta ba.
"Ba kin ce Aliyu na da tsari jakar da yake zuwa gida da ita daban, haka na gurin aiki da kuma kayan da yake sawa?"
"Eh haka ne amma ban ga amfanin tambayarki ba."
Gyara zama ta yi ta ce,"A cikin jakar za ki sanya inda ba zai lura ba. Ki nuna kawai zumunci za ku yi irin na ya da ƙanwa. Zan iya haɗaki da Gali a matsayin wanda zai aure ki har ki haɗasu. In kika samu ya yarda da hakan, na san za ki iya sanin kalaman da za ki yi masa ki shiga cikin gidansa, don ki samu ki aiwatar da abin da muka yi ninya. Dalilin sawa kuwa za ki rinƙa kiran shi akai akai kice in za shi Kaduna ya gaya miki za ki ba shi tsaƙo ya kaiwa ƙanninsa, yana gaya miki za shi sai ki kawo masa tsarabar kayan kwalliya, ta yanda za ki samu ki sanya masa condom ɗin, sannan bayan ya tafi washegarin ranar, ki je gidan iyayensa ki gaya musu irin yaudarar da yayi miki..."
"Are you out of your mind? That you are giving such advice?"Ta furta cikin ɓacin rai tana kallonta.
Ni this isn't workable! Kin san abin da haka zai kawo? Ni fa ban ga wani amfanin wannan banzar shawarar ta ki ba. Aliyu tsanata zai ƙara yi, kuma kin san ba zan iya rayuwa babu shi ba."
"Daɗina da ke ba kya jiran kici ribar ƙarshen zance." Ta ce mata cikin takaici.
"Saboda gurguwar shawara kike ba ni. Mahaifin Aliyu ya sanya yarda sosai a kansa, kina ganin in har na yi sanadin rushe yardar nan. Aliyu zai ƙara kallona da fuskar rahma?"
"Ba ki da wayo Lubaiyna. Hutu da wayewa da kika taso cikinsa ya sanya kanki ba ya kawo wuta. Wannan yardar da mahaifinsa ya yi masa da shi za mu yi amfani ki samu Aliyu a hannunki."
"Hmmmmh!" Kawai ta ce tana mamakin wautar shawararta.
Ganin ta yi shiru kawai sai ta ɗora da cewa,"In har ya tafi sai ki bishi kije ki saka kuka ki ce wa mahaifinsa Aliyu har ciki ya yi miki, sannan ya yi miki alƙawarin aure ya ƙi aurenki. Iyayenki sun yi fushi dake shi kuma ya guje ki. Ki gaya mahaifinsa in har bai yarda ba zai iya bincike sosai domin ba za a rasa wanda suka san mummunar halinsa ba. Kina iya cewa aje gidansa domin hatta kayan sawanki yana can. Kin ga anan mahaifinsa zai zurfafa bincike ya gano gaskiya. Wannan condom da kika sanya mishi sai ki ce ko Kaduna ya zo, sai ya kira ki kin biyo shi, kin ga zai bincika har ɗakinsa na gida, ya ga condom ɗin. Kin ga bayan ya gano gaskiya ba zai ƙi aura miki shi ba, domin na san ta wannan hanyar zai huce fuska biyu da ya zama, don in har zai yi adalci ba zai ƙi ba, saboda shi ma na san yana da 'ya'ya mata. Ba zai so hakan ya kasance da shi ba. Bayan haka ya faru sai mu shiga bin malamai don mu jawo hankalinsa gareki, amma yanzu kun rabu ko magani aka ba ki, don ki sanya masa cikin abinci ba za ki samu hanya ba."
Shiru ta yi xuciyarta na son yarda, amma tunaninta yana gaya mata gurguwar shawara ce. Lokaci guda sai ta fara yadda musamman da ta tuna yaudararta da ya yi. Kuma sai ta ga in har za ta aure shi ta rayu da shi, sam ba za ta damu da tozarci da wulaƙancin da zai yi mata ba, sannan yana matsayin mijinta dole ta yi amfani da kissar da za sanya har ya gaji da tsanarta ya daina. Lokaci guda sai ta yarda, da shawarar ta kuma ta amince har ta yi mata alƙawarin aikaita haka.
A haka suka bar shawarar, Lubaiyna ta koma gida cikin tsananin farinciki. Wayarsa ta fara kira amma ya sanya ta a black list. Ba ta damu ba, don haka ta sanya ranar da za ta je gidansa
Aliyu
A ranar da Anty Amarya ta sanar da shi ya yi kwanar farinciki, domin tun kafin ya ga yarinyar ya riga ya gama ji a jikinsa ya samu matar aure. A daren ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi ba, da bai karɓi numbarta ya kira ta ba, har ya miƙe zai je gurin Anty amarya ta ba shi numbar, sai kuma ya fasa ya kwanta, da nufin ya kira ta tun da ba ta online.
Har ya dubo numbar zai kira, zuciyar sa ta ba shi shawarar, kan ya yi haƙuri zuwa nan da kwana biyun, domin ba ya iya tunanin zuciyarsa za ta iya wuce kwanakin.
Da ya ga ya samu kalar matar da yake so, sai ya ji zuciyarsa da gangar jikinsa sun bijiro masa da buƙatar aure. Wataƙila lokacin da ya ɗauka yana jin ba ya sha'awar auren, don bai samu wacce yake so ba, amma yanzu sai ya ji yana son ya samu wacce in ya dawo gida. Za ta rugo da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙamshi mai daɗi da shiga mai jan hankali, sannan gidan yana fitar da wani ƙamshi mai daɗi, ga abinci wanda zai rinƙa ɗauke masa yunwarsa.
Shi kuma cikin shauki ya haɗa ta da jikinsa ya manna mata kis. Lokaci ya ja, har akwai lokacin da za ta haifa masa kyawawan yaran da ba su wuce guda uku ko huɗu. Ya ba su kyakyawar tarbiya, da duk wani ji daɗi na rayuwata. Sosai ya ƙosa ya je ya ganta domin har ya fara shiri. Duk da kasancewarsa ba mace ba, amma gyara da ƙalƙala da yake yi, bana tunanin ko ita macen aka ce zai zo za ta yi wannan gyaran.
Anty ta so su koma a washegarin da suka zo, musamman yadda ɗan gidan nata ya ƙosa ta koma don ba ya son ganinta da Jimmmalo, wacce a yanzu take tunanin ta samu wacce za ta zamar mata makwafin Kaka Tani. Da dare ya yi Daddy ya dawo, sai ya sha giyar mamaki. Domin ko kafin ya shigo cikin gidan, ya ji muryarta tana dariya suna hira da Anty Amarya. Da ta cika ta surutu har ta ji.
Da sallama ya shigo yana al'ajabi. Turus ya yi ganin yadda ta shige jikinta.
Ganin ya shigo duk duk haɗa baki cikin girmamawa suka fashe shi. Jimmalo har da motsi da bakinta duk da ba gaisuwar ta yi ba, ganin yadda Anty ta tsareta da ido.
"Ikon Allah!" Ya furta lokacin da ya ije tsarabar da ya shigo da shi.
"Hmmmmh! Ni kaina abin ya ɗaure mini kai. Tun da Amarya ta zo, Jimmalo ta saki take zuba a cikin gidan nan kamar ya'yan kanya."
"Na yi mamaki ƙwarai ban san sa'ar da kike shi ba." Cewar Dady bayan ya zauna.
"Sa'a ace babba ma kuwa, domin tun lokacin da na ga Aliyu, ba shi da wacce yake kulawa a Zariya sai ita ma tabbatar da ita mai sa'a ce, mutumin da mutane bai dame shi ba. Ko ni da na ke mahaifiyarsa ba ya damuwa da ya yi hira da ni. Ga kuma Jimmalo wacce ta gagari kowa a kauyen Damagaran."
Dariya suka yi Daddy ya miƙe, bayan sun ɗan taɓa hira ya shiga ciki yana murna sosai. Da aka kira sallah sai Anty ta miƙe zuwa ciki ta yi alwala.
Jimmalo tana zaune tana kallo. Ganin kowa ya tashi a falon, amma tana zaune sai ta fito daga cikin ɗakin ta ce,"Ta shi ki yi sallah."
Motsi ta yi da bakinta kamar za ta yi magana. Ganin haka ta riga ta da cewa,"Sallah ita ke bambance tsakanin musulmi da kafuri. In har ba kya sallah wuta za ki shiga."
"Ba zan shiga ba tun da ban girma ba."
"Kin girma Jimmalo tun da kika haura shekara sha huɗu. Addini daga shekara bakwai ya yi mana umurni damu fara dukan yaro in har bai yi sallah ba, don haka ki tashi ki yi sallah ko na fasa daina magana da Captain."
Babu musu ta miƙe duk da ba haka ranta ya so ba.
"Ki shiga bayi ki yi alwala, ina jiranki mu yi." Anty ta ce mata ganin yadda ta sha kunu.
Ba haka ta so ba, domin ta so ta yi ita kaɗai yadda za ta ci karenta babu banbaka, amma tuna za ta fasa alƙawarin sai ta shiga bayin, ba tare da ta ce komai ba, domin ita so take yi in za ta tafi Zariya su tai tare.
Da ta shiga cikin bayin ta fara alwala, sai Anty Amarya ta zauna a bakin gado ta jira ta. Sai dai lokacin da ta ɗauka ta fito ya sanya ta kalle tada sauri.
Kallon mamaki Anty ta bi ta da shi. Jimmalo har kin yi alwala a sakanni?"
Jin tambayar ta bata fuska ba tare da ta bata amsa ba, domin ita kanta ta san cewa ba alwalan ta yi ba ta dai watsa ruwa.
"Shiga na ya yadda kike yi." Ta ce mata tare da buɗe mata bayin
Ganin za ta yi mata musu ta ce,"In har kina son na cika miki alƙawarin da na ɗaukar miki. To ki cire tunanin mini musu a rayuwarki."
Ba ta amsa ba ta shiga ciki. A nan ta shayar da Anty duniyar mamaki. Domin ba alwala ba, shi kanshi tsarki ba ta tunanin ta iya.
Ganin wasa kawai take da ruwa, sai ta nuna mata yadda za ta yi alwalar. Suka fito bayan ta kammala tana mamakin yadda Kaka Tani ta yi mata rainon dabbobi, domin za ta iya cewa bayan gangar jiki da take da shi na mutane, gabakiɗaya rayuwar dabbabibi ta koyar da ita.