← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 52

Sashe 47

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai sa'anki a gurin nan? Da za a tambaye ki ce kin yi masa ƙufula. Uban mene ne ƙufula."

"Ɗaga shi na yi na maka shi da ƙasa."

"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Kika ɗaga ɗan mutane kika maka da ƙasa kamar dutse?" Daddy ya yi tambayar cikin damuwa.

"Ai dole ki karya shi. Yaro ɗan primary one!" Mommy ta jinjina kanta tana faɗin haka.

Aliyu zare idanunsa ya yi ya ce,"Ta karya yaro fa kuka ce?"

"Karya shi ta yi, kuma babu ruwan mu da hukuncin da iyayen yaron za su ɗauka, sannan mun koreta daga makarantar." Jin abin da ya ce sai ya harzuƙa Aliyu. Da sauri ya kama hannunta yana faɗin,"Tun da kika karya yaro saboda rashin imaninki. Nima sai na karya ki." Kafin su yi aune ya murɗa hannunta da ƙarfi.

Wani irin ƙara ta saki jin zafi yana shiga ƙwaƙwalwarta.

"Aliyu lafiyarka kalau, in ta karya shi ka ma sai ka ƙaryata?" Daddy ya yi masa tambayar cikin ɓacin rai tare da daka matsa tsawa.

"Zalinci ta yi dole a rama masa. Shashashar banza daƙiƙiya ko kunyar ba kya ji. Kina cikin ƙananan yara, ba dole ki yi zalunci ba."

"Wayyo Allah! Mugu kawai azzalumi. Wallahi ya karya mini hannu." Ta furta tare da saka ihun da sai da suka matsa.

"Aliyu, kar na ƙara ganin haka in ba sulhunta zancen za ka yi ba, maza ka bar gurin nan." Daddy ya ce masa yana nuna masa hanya.

Babu musu ya juya domin bai zo don ya sulhunta. Abin da ya kawo shi ya yi zuciyarsa fes ya shiga cikin gidan don ya shiga mota.

"Yaron nan ba shi da imani da gaske ya karya ta." Cewar Mommy ganin yadda take ihu domin ko ba karaya bane, tabbas ya yi mata tsaguwar kashi ko targaɗe.

Principal sai ya tsaya cikin mamakin abin da Aliyu ya yi, sannan ya tafi ba tare da tausayi ba.

"Ni fa ban kawo muku ƙara ba, don ku ƙaryata. Ku dai shirya duk matakin da iyayen yaran za su ɗauka." Ya ce ma Daddy yana kallonsu.

"Tare zamu tafi asibitin gurin yaron. In sha Allahu zan sasanta lamarin. Mommy ki shiga da ita ciki, ki sanya direba ya kaita a gyara mata hannun." Ya ce mata yana kallonta.

Jin abin da ya ce sai ta kama hannu Jimmalo da take ta ihu tamkar an kashe ta.

"Wayyo hannuna ya karya ni kaka Tani." Ta furta tana kallon hannun da har ya fara tasawa.

"Mu shiga ciki ko ranki ya ɓaci. Ai kin cancanci haka tun da shi yaron da kika karya ba mutum bane. Haba Jimmmalo wallahi ba kya jin magana." Mommy ta daka mata tsawa tana faɗin haka.

"Wallahi sai na rama, tun da ya karya mini hannu sai nayi masa tabon da ba zai manta da ni ba." Ta furta tana ɗaga hannunta da yake raɗaɗin zafi.

"Ba kya ji ko? Zuwa zaki yi ki ƙara takalarsa. Allah ya ba ki sa'a kin san ke za ki wahala." Ba ta ce mata komai ba, tana kuka ganin haka sai ta kama hannunta suka shiga ciki.

Anty da take juye abinci a kula ta ji kukanta yana tashi, Mommy na yi ta mata faɗa, wanda ya sanya ta rufe ƙular da sauri ta fito suka yi magama a falo.

"Subuhanallahi! Ciwo ta ji?" Ta furta tare da isa gareta ta kama hannun.

"Yarinyar nan tsaf za ta iya kashe mutun da mugun halinta. Zuwa ta yi ta karya yaron mutane. Shi ne masu makarantar suka kawo ƙara. Shi kuma Aliyu ya karya ta ita ma."

Salati ta saki tare da zare idanu. Sai ta rasa cikinsu wa yafi rashin imani.

"Jimmalo, da gaske kin karya yaro? Shi kuma Aliyu yana da hankali kuwa?"

"Na rasa hukuncin da zan yanke. Yaran nan so suke su kashe ni." Ta furta tare da zama kan kujera. Fuskarta bayyane da damuwa dake xuciyarta.

Ganin ihun da ta ishe su da shi. Kan dole ka je asibiti aka gyara mata hannu. Mamakin kukan da ta yi suke yi, saboda targaɗe ba karaya ko tsaguwar kashi ba.

"Idan ke kina kuka haka, shi kuma yaron da kika karya sai ya mutu ko?" Anty ta yi mata tambayar tana kallon hannun daya suntuma.

"Rashin kunya ya yi mini kuma na gaya musu zan iya karya shi."

Tsaki suka saki a tare ba tare da sun ce komai ba, domin kowa ta kai shi wuya.

Da suka koma gida, tana ta kuka da ƙyar Anty ta rarrasheta sannan ta ji abinci. Da ta tuna an koreta a makarantar, sai hankalinta ya kwanta ta daina jin zafin ciwon, amma ta ɗau alwashin tun da ya ƙaryata, sai ta yi masa abin da ba zai manta ba.

Tana zaune har sauran yaran suka dawo. Nan suka yi mamakinta sosai domin ta wuce tunaninsu. Hanifa da Mufida da suka dawo gidan ƙawarsu, sun cika da mamakin abin da ta yi.

Da ƙyar Daddy ya samu aka kashe zancen, bayan ya biya kuɗin da aka kashe, sannan ya toshe bakin iyayen da kuɗi. Yana asibitin har sai da aka yi kiran sallah. Sam ya manta da batun abinci saboda samuwar da yake ciki. Abin da ta yi sai ya ci alwashin sai ya yi mata dukan tsiya, amma sai kuma Aliyu ya yi hukuncin mahaukata.

Da ya dawo, faɗa sosai ya yi mata kamar zai aro baki. Ita dai hankalinta a kwance. Burinta ya ce ba zai iya zama da ita ba, sai a a haɗa ta da Anty Amarya ta koma gidanta. Tana wannan tunanin sai ta ji ya ce,"Dole ki koma makaranta, domin ba za ki rayu da jahilci ba

Ko islamiya har na siya miki form. Jira na ke a yi miki ɗinkin kayan islamiya da hadda."

Wannan mummunar albishir da ya yi mata ya sanya xuciyarta ɓaci. Fuu ta yi ɗaki ta faɗa kan gado. Kuka ta ci gaba da shi, babu wanda ya kula ta har Anty Amarya saboda ita kanta haushinta take ji.

Anty Amarya da take tunanin za ta fito amma shiru. Ganin haka ta ɗauki abincinta ta shiga dakin."Ki tashi ki ci abinci."

Tana kwance ba ta motsa ba jin abin da ta ce."Sam ba kya ji Surfy. Ba za mu shirya ba in har kika ce rashin ji za ki yi."

Ita kanta sai ta yi mamakin rashin jin daɗin da ba ta ji ba, da furta hakan domin ko lokacin da Kaka Tani take nan ba ta damu ba don ta yi fushi.

"Shi ne ya tone ni."

"To sai ki karya shi?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai.

Ganin yadda fuskarta ya bayyana damuwar fushinta sai ta hau kan gadon."Kar na ƙara jin kin yi haka. Maza ta shi ko ci abinci. Kin ga ga shi kin ja Aliyu ya ji miki ciwo."

Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ga rashin dacewar sanar da ita abin da za ta yi masa, domin ta san a ƙarshe cewa za ta yi kar ta yi. Ita kuma ta rantse sai ya yi kukan da ya fi nata.

"Ki ci abincin." Ta furta tana kallonta

Babu musu ta janyo filet ɗin za ta sauka ƙasa, wanda ganin haka ta taimaka mata ta saukar da abincin kasa.

Anty Amarya sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta kaya zuwa falo suna kallo.

Mufida damuwa sosai ta shiga ganin har ana gobe za su tafi ba ta samu hanyar da zata sa mishi maganin ba. Tana wannan tunanin duk suna falo sai aka kira Mommy a waya.

Kamar ance ta saurara sai ta ji tana faɗin,"Ok, yanzu za ta kawo maka har da ruwan tea da na dafa maka."

Tana kallonta har ta kashe wayar ta kalli Umma ta ce,"Yayan ki ya ce ki kawo masa abinci, sannan ki juye ruwan shayinsa a fulas."

Da sauri ta tashi jin abin data ce. Ganin haka sai Mufida ta bita zuwa kicin ɗin.

Tana ƙoƙarin juye ruwan flaks sai ta shigo."Na ga ba ki so ki taso daga kallon ba. Ki kawo na kai mishi sai ki je ki ci gaba." Ta furta cikin murmushi da sakin fuska.

"Wallahi, da yake ina son na kalla ban ga na wannan satin ba, amma kar ki damu zan kai mishi." Ta ce da ta tuna zai iya mata faɗa.

"Don Allah ki bani na kai masa, dama ina son nayi masa maganar ya biya mini kuɗin makaranta, saboda wannan semester Baba ya ce ba shi da kuɗi ne tambaye shi."

Ɗan jim ta yi, domin ta san da wuya in haka ne. Tsoro take kar ta je ta yi masa kwarkwasa, saboda ta san tana son sonshi, amma tun da ta roƙa babu yadda za ta yi.

"Ok, ga shi sai ki haɗa masa da ruwan tea."

"Ok, na gode. Bari na nemi tawul na ƙara gogewa kin san yayan namu mai tsafta ne."

"Da yake kular a tsaftace take, amma ni dai na tafi kallona ke kika sani." Ta ce mata tare da ficewa da sauri tana ja mata ƙofa.

Fitan ta yi sai ya yi mata daɗi sosai, da sauri ta ciro ƙunshin maganin da tun da ta zo da shi take yawo da shi, amma ba ta samu hanyar sakawa ba.

Tana ƙoƙarin zubawa Jimmalo da ta ji tana son shan ruwa, sai ta nufo kicin ɗin don ta iba a famfo, domin duk frij ɗin gidan ba ta iya buɗewa ba.

"Kai! Uban wa za ki kashe?" Ta ji ta yi mata tambayar da ya razana ta, wanda ya sanya ta juyo da sauri cikin tashin hankali, amma kuma ganin Jimmalo ce sai hankalinta ya ɗan kwanta kamar ta yi baƙo ya mutu, domin sam ba ta ɗauke ta a masu hankali ba.

Kasa amsa mata tambayar ta yi, tana in'ina wanda ganin haka ta ce,"Na rantse sai kin gaya mini ko na gaya wa mutanen gidan, domin tun da kika zo ban yarda da ke ba, sai wani zare idanu kike yi, sannan kina kallon Anty Amarya a yatsine in tana magana da Hanifa."

Sosai ta yi mamakin abin da ta ce, saboda ba ta taɓa tunanin za ta iya gane hakan ba.
Chapter 47 · 0% Book details