Sashe 6
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Oh please, no! Kar ka yi mini baki." Ya katse shi yana faɗin haka.
Mamaki ya sanya shi kallonsa ganin haka ya kurɓi lemun, sannan ya ije ya kalle shi ya ce,"Kasan kalar macen da na ke so na aura kuwa? Mace zan aura tsarkaka wacce ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba. Uwa ta gari zan zaɓawa 'ya'yana, bana fatan Ubangiji ya jarrabce ni da aurar mace mara kamun kai kamar Lubaynah."
"Ok, wanzami ba ya son jarfa kenan? Ita Lubaynah da ka ɓata, wa kake son ya aure ta?"
"Kan me za ka tambaye ni? Sai ka ce ni na kawo ta barikin?"
"Saboda ita ma watarana uwa za ta zama, amma ka ɓata mata rayuwa, Lubaynah is not wore son ka ya sanya ta aminta da kai."
"Dole na yi mata? I didn't force her, kuma ni kaina ina fatan Ubangiji ya shirye ni na daina aikata hakan."
"Hmmmmh!" Ya ce masa yana kallonsa cikin mamaki ganin ya haɗe rai.
"Ni dai a tunanina bai kamata ka yi wa Lubaynah haka ba, musamman da she was virgin kai ka fara sanin..."
"Kuma ni na kawota barikin da za ka tilasta mini na aure ta? Na ga kaima ya kamata ka auri matan da kake hurɗa da su."
"Duk cikinsu babu wacce na fara saninta. Sannan Lubaynah yarinya ce, wacce ta fito daga gidan mutunci. Iyaye ta they well of. Ga shi duk tana da qualities da kake so."
"Ba zan iya aurenta ba, kuma don ni na fara sani ta bani da tabbacin ni kaɗai take kulawa, sannan inda ba ta yi ninyar zama, mara kamun kai ba za ta yarda da ni ba."
Cikin mamaki yake kallonsa."Yarinyar nan fa soyayyar da take maka ya sanya ta faɗa irin rayuwar nan."
"Ok, in na fahimce ka, so kake sai ka ce dole sai na aure ta? Tun ba yau ba na sha gaya maka matar da zan aura. Yarinya natsatstsiya mai addini, wacce na san iyayenta sun ba ingantacciyar tarbiyya, sannan ba zan yarda na auri mace jahila mara ilmin addini ba. Duk cewa da kake Lubaynah na da ilmi, sam ba ta da na addini, domin duk macen da ta je makaranta, ba za ta mallaka ma namijin daba muharraminta kanta ba. So don haka Please kar ka ƙara mini sha'awar mace irin ta. I dan na tashi aure za ka yi mamakin uztaxiyar da zan aura."
"Da irin halayenka Captain Aliyu? Karka manta azzaniyatu wazzani."
"Wace mace kaga na taɓa kulawa, bayan Lubaynah da ta kawo mini kanta?Da har za ka danganta ni da auren mazinaciya?"
"Ina dai ba ka shawarar ka aure ta, saboda duk saboda kai ta faɗa wannan harkar."
"Ba zan iya auren mace da ranar first night ɗinmu, zai kasance mini baƙar rana ba, domin na riga na santa sam ba zan yi ɗokin ranar ba. Bayan haka da kake cewa na aure ta, wane tabbacin kake da shi na cewar ni kaɗai take kulawa? Ni fa ban yarda da ita ba, saboda idanunta ya buɗe, don haka ko xan yi mu'amala da ita sai na yi amfani prevention."
"Duk ba mafita bane Captain. Sannan Lubaynah ba za ta zura ido tana kallo ka yi aure ba, yarinyar she is mad in loving you. Za ka kunna wa kanka wutar da ba za ka iya kashewa ba. Kasan yadda mahaifinka ya yarda da kai, amma ka zamar masa fuska biyu. Duk ranar ta da ta ji za ka yi aure. Tabbas za ta sanar da iyayenka, kuma hakan zai rushe yardar dake tsakaninka da su. Kar ka manta ka yi wa Daddy alƙawarin duk ranar duk ranar da ya kamala da wani hali mara kyau za ka ije aiki, ko kuma ya ɗauki duk hukuncin da ya ga dama. Ina ba ka shawarar, ka auri Lubaynah in ya so sai ka auri kalar macen da kake so."
"Duk abin da za ka ce, sam ba zan yarda na auri mace da ta siyar da mutuncinta a waje ba, don haka ka daina wahalar da bakinka, sannan am very smart and wise, Daddy ba zai taɓa gane fuska biyu na ke da shi ba."
"Hmmmmh! A juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe. I'm a good friend am just advising you. Ka san A friend in need is a friend indeed."
"I know my friend, stop fearing am so wise nothing bad will happen."
"I hope so." Ya ce masa sai kuma ya buɗe baki zai kara cewa wani abu, domin yana kallonsa a matsayin azzalimi mai son kansa.
"Please let's change the topic. I'm frustrating." Ya ce masa cikin ɗaga murya.
Dariya ya yi ganin lokaci ɗaya yadda ya hau. Hannu ya ba shi da nufin su tafa, amma sai ya ƙi yana harararsa.
Lubaynah 'ya ce ga wani shahararren mai kuɗi a garin Kano, mai suna Alhaji Adamu Laska. Mutum ne da yake da kantina sosai a garin Kano. Matarsa ɗaya kamar rai Hajiya Shuwaima. Suna da 'ya'ya huɗu, ita ce ta biyu tana bi wa Yayarta Hannah da take aure a garin Abuja. Rayuwa suke yi cikin hutu da sangarta, domin a gidan duk abin da suke so shi suke yi. Mahaifinsa ba ya zama mahaifiyarsa 'yar boko riƙaƙkiya, sam ba ta da lokacin kanta. Rayuwa suke yi kowa abin da ya ga dama yake yi. Sakandire da firamare duk a Kano ta yi, bayan ta kammala ta shiga Jami'ar Abuja. Sosai idanunta ya buɗe, domin mace ce classical wacce ta iya wanka.
Ta haɗu da Captain Aliyu, a lokacin da ta raka wata mate ɗinta, Barrack ɗin sojoji gidan 'yar uwarta. Captain Aliyu shi kuma mijinta abokinsa ne. Tun ranar da ta ganshi ta mutu a kansa. Sai dai duk nacinta kallon kirki ba ta samu ba.
Tana mugun sonsa kamar za ta kashe kanta. A lokacin da ta bayyana masa ƙaunar da take masa, sai ya watsa mata ƙasa a ido, domin bai ɓoye mata ba, ya sanar mata ba type ɗinsa bace. Hankalinta ya yi mummunar tashi sosai ta shiga cikin damuwa.
Ta rinƙa nace masa tun ba ya kula ta, har ya fara kulata. Ganin ta kasa samun kansa sai ta shiga seducing ɗinsa, domin a tunaninta wannan hanyar kawai za ta iya shawo kansa.
Captain Aliyu, tun yana shareta har ta ci karfinsa ya fara kulata, domin a wancan lokacin tsananin addu'a da tuna kashedin da Daddy ya yi mishi, ya sanya shi ɗauke kansa daga matan bariki, duk da yadda abokansa suke ƙoƙarin cusa masa wannan halin. Sai dai, shigowar Lubaynah cikin rayuwarsa, ya sanya shi manta alƙawarin da ya yi wa mahaifinsa. Samunta da ya yi a matsayin budurwa ya sanya ta samu daraja a gurinsa. Wani lokaci in zai yi tafiya, har ɗaukar ta yake yi su tafi tare. Shi kansa yana sonta, amma ba soyayyar aure ba. Wani lokacin inta ɓata masa har dukan ta yake yi, amma ta kasa rabuwa da shi. Burinta kawai ya tura a yi bikinsu, amma kullum ta yi masa ƙorafin haka sai ya fara kaukauce mata yana kawo mata ƙauli da ba'adi.
Washegari bayan sun tashi ta yi sallah. Kicin ta nufa don ta haɗa musu abin karyarwa. Tan ƙoƙarin ɗora ruwan zafi a gas, ya dawo ya buɗe ƙofar kicin ɗin ya shgo.
Ganin za ta ɗaura girki ya ƙarasa gunta."Ki bar Peter ya yi mini breakfast, na gaya mini daga abincinsa sai na Momi na ke iya ci."
Kallonsa ta yi cikin takaici ganin ya kushe ƙoƙarinta."Haba baby, duk lokacin da na so na faranta maka sai ka nuna ba ka so. Nufinka in mun yi aure wa zai rinƙa muka abinci?"
"God forbid." Ya furta a ransa amma a fili jawota ya yi zuwa jikinsa.
"Kar ki damu da wannan ki bari lokacin ya yi, bayan nan matata ba za ta rinƙa girki ba."
"Don Allah Sojana, ka amince ka turo iyayenka gidanmu ayi maganar bikinmu. Ina sonka na matsu da mu yi aure." Ta ƙarashe maganar hawaye yana bin fuskarta.
"Mene ne abin damuwa bayan muna tare? Ina sonki kuma kina mini duk abin da na ke so, sannan duk lokacin da kika buƙaci ganina za ki iya zuwa gidana. Haka kuɗina ATM ɗaya na baki, a ganina rayuwa mu ke yi kamar mata da miji..."
"Akwai bambancin sosai. Aure yanada daraja kuma ko ina ana bayyana shi, amma zamammu babu wanda zan yi fatan ya sani. Da ace iyayenka za su buƙaci zuwa inda kake korana za ka yi, amma in ina matsayin matarka cikin farinciki xan jira zuwansu. Wallahi my man ina sonka, na yi maka alƙawarin duk abin da kake so zan yi maka."
Juya mata baya ya yi zai fice, ganin tana son ta ƙaryar da zuciyarsa, amma ko mai za ta ce ba zai taɓa aurenta ba. So yake ya auri matar ƙwarai.
"Ki yi haƙuri lokaci zai yi saboda ban shirya aure ba."
Jin abin da ya ce hawayenta suka ƙaru."Ba ka sona ne, ko kana tunanin aurena, saboda na yadda da kai tun kafin mu yi aure? Wallahi bayan kai babu wanda a taɓa mallakawa jikina. Soyayyarka ce ta makantar da ni har na yarda da kai kafin aure. Don Allah kar ka yi mini butulcin ɗa namiji. In har ban aurenka ba zan iya mutuwa, saboda ina maka mugun son da ban taɓa yi wa wani da namiji ba." Ta furta cikin kuka tare da ƙara rungume shi.
"Ban shirya aure ba, in har kin matsu da ki yi aure za ki iya."
Jin kalamansa, hankalinta ya tashi kuka sosai ta fashe da shi. "ka fito fili ka gaya mini baka sona Sojana, in har ka yi mini haka sam ba ba ka mini adalci ba."
"Kina gaya mini haka, kamar na tursasa ki dole ki ba ni jikinki. Seducing ɗina kika yi har yau ina dana-sanin saninki a 'ya mace, domin ke ce kika sanya na karya alƙawarin da na yi wa mahaifina."