Sashe 1
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 1
Ƙauyen Damagaran
Tsaye take tamkar wata soja, tana kallon Ma'u mai gyaɗa, cikin zallar rashin kunya da fitsara. Cikin shiga ta riga da zani da ɗankwali duk daban, sai kuma ɗammara da ta sha da baƙin gyale. Fuskarta ɗauke da kwalliya irin ta 'yan ƙauye, waɗanda suka amsa sunan su 'yan mata, kuma suke ganiyar tashen ƙuruciya. Wata kalar hoda ta shafa a fuskarta, duk ta yi mata butsu-butsu. Sai kuma gira aka ɗauke shi, tun da ga kan farkon girar, har zuwa kusa da idanunta, sannan aka haɗe jagirar da kwallin da ta sanya a idanunta. Wasu irin bille guda biyu ta zane fuskarta da shi, sannan aka ja baƙi a saman leɓenta. Silifas yake a ƙafarta duk ya tsiɗe, yayi datti, domin duk wanda ya ga silifas ɗin, zai rantse ba a taɓa sanya masa ruwa an wanke ba. Ita a dole ta yi kwalliya kuma ta yi kyau ta ƙure a daka, amma kana ganinta za ka tabbatar da ƙazamiya ce sosai, irin ƙazaman nan, da an gansu za ka gane su, saboda in ta matso kusa da mutum, da ƙyar zai iya shaƙar numfashi. Saboda ƙazantarta sam mutum ba zai iya gane fara ce ko baƙa ba, sannan kyakkyawa ce ko mummuna. Duk wanda aka sanya ya fasalta ta;mummuna, bagidajiya, ƙazamiya kuma mara tarbiya. Jimmalo jikar Tani kenan, wacce ta gagari kowa a ƙauyen Badarawa. Sam babu wanda yake shan ruwa a hannunta, babba ko yaro, saboda ba ta da kunya da haƙuri, uwa uba kuma ɗaurin gindin da ta samu a gurin Kanta Tani, wacce a halin yanzu ita ce ta zame mata uwa da uba.
Tsawon lokacin da ta ɗauka, tana tsaye ba tare da ta jirga ba, jiran Ma'u mai gyaɗa take yi, wacce ta bita har cikin gidanta ta ɗauko mata gyaɗa.
Bazawara ce irin masifaffun nan, domin jarabarta ya sanya ko sati uku ba ta yi ba, mijinta ya sake ta. Tun daga wannan lokacin ta fara aure ana sakin ta, saboda tsananin masifarta. Ko a ƙauyen mutane suna shakkarta, sai dai ta bambanta da Jimmalo, domin in har ba ka kula ta ba sam ba za ta shiga sabgar ka ba, amma Jimmalo ita kowa takala take yi. Tun da ta gane ana tsoron Ma'u a ƙauyen ita kuma ta ɗauka ɗamarar faɗa da ita. Duk lokacin da jarabarta ya tashi, gidan Ma'u take wucewa ta je ta iban mata gyaɗa don ta takale ta.
Sosai ta girme ta domin ba sa'arta bace, amma saboda jarabarta da rashin kunyarta take shakkarta. Jimmalo sam ba ta da haƙuri ga ta da nacin tsiya a faɗa, musamman in har ita aka cuta. Ta rinƙa bibiyar mutum har sai ta rama abin da aka yi mata. Shekarun ta duka sha huɗu, amma abubuwan da take yi ya girme shekarunta. Sai dai duk wannan halayen da take da shi, tana da girman kai da nuna isa da kuma gadara, sannan ga shegen kafiya, akwai lokacin da duk yadda mutum ya so ta kula shi ba za ta kula ba.
Da gudu ta shallake katangar gidan Ma'u mai gyaɗa tana dariya, ganin ta nufo ta da muciya. Ma'u mai gyaɗa cikin tsananin ɓacin rai take kallonta.
"Wallahi Jimmalo, yau ni da ke ne a ƙauyen nan domin babu wanda ya isa, ya ci mini bashin gyaɗata ya zauna lafiya, ballantana ki shigo har cikin gidana ki ina ina gani ki gudu.
Jimmalo dake kallonta tana dariyar ƙeta."Kin san cewar in har kika na ce sai kin karɓi kuɗin nan, za ki ja wa kanku tashin hankali? Don na rantse yau ko Babanki Tanimu zai taso da ga ƙabari ya yi mini fatalwa ba zan bayar da kuɗin nan ba."
"Ni kuma wallahi sai kin bani, Kuma daga yau sai na kawo ƙarshen shigo mini gida da kike yi ba tare da izini ba." Ta ce tana gyara ɗanmarar da ta ji, tamkar wacce za ta yi dabbe.
"Gidan na ki ai ba aljanna bace, da sai mutum ya yi aikin lada za a barshi ya shiga. Gidan da yake wari shadda ta cika kin ƙi kwashewa. Na ci na ƙarfi na ci na tsiya da dabbe. In kina da ƙarfi ki zo ki ƙwata, kin san dai ki ba irin dolayen mazan da kike aure bane kina musu duka, domin wallahi ɗaukar ki zan yi na tula da ƙasa." Ta ce tana murguɗa mata baki, tare da harararta.
Kallon kanta ta yi, jin abin da ta ce saboda Ma'u irin matan nanne masu jiki, yayin da Jimmalo take siririya sai tsawo kamar rama.
"Ni za ki nuna wa Allah ki ƙwala da ƙasa?" Ta yi mata tambayar cikin takaici.
"Eh mana saboda ba irin mazan da kike aure bane. Ɗube ta ƙatuwa amma ta kasa zaman aure."
"Don ubanki na fi ki saboda ni ina auruwa, ke kuwa tun da kika zama 'yan mata, babu karen da ya zo gurinki. Ƙazamiya mai warin balaga."
Jin abin da ta ce kuma ta yanke ta da yawa, sai kawai ta ɗauki dutse ta ƙwala mata. Ta ci sa'a kuwa ta same ta a ƙafa.
"Kan uba! Wallahi yau sai na biki ko cikin mamanki za ki koma, na ga uban da ya tsaya miki." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka tare da kwasa da gudu.
Ganin haka itama ta ɗaga bujenta ta kwasa a gije. Gudu take yi sosai kamar wata 'yar tsuntsuwa, don tsalle take bugawa dai ta shalle guri mai nisa.
Ba ta tsaya a ko'ina ba sai da ta ga ta kai ƙofar gidan, sannan ta tsaya tare da yi mata gwalo da daƙuwa ta shige cikin gidan.
"Wallahi yau ko bayan Atine za ki shiga sai na biki, tun da ba ki da kunya, gabakiɗaya kin addabi mutanen ƙauyen nan." Ta ce cikin fushi tare da shiga cikin gidan.
Da gudu ta shallake Baba Aitine da take tsaye a bakin ƙofa, tana ƙoƙarin ɗora bushashshen tuwon da za ta shanya.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don ubanki yau wane mara haƙurin kika tono kuma, har ya ja aka yi mini asarar bushashshen tuwo?" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya.
Tura baki ta yi tana harararta, sai kuma ta kalli Ma'u mai gyaɗa da ta shigo ciki.
"Uhumh, da na na san sai ke jarababba mara haƙuri." Ta ce tana watsa mata mugun kallo wacce take tsaye tana nishi kamar ta haɗiyi kwaɗo.
"Wannan mara haƙurin ne daga na ci bashin gyaɗa, na ce mata ranar da jakin baba ya yi ƙaho zan ba ta, shi ne ta yi mini duka kuma ta biyo ni." Ta ƙarashe maganar tana ƙaƙalo hawayen ƙarya.
"Da ma na san sai ita ai, sam ba ta da haƙuri sam, duk ƙauye nan ita ce kawai za ta biyo ki har cikin gida, tun da ba ta da ido. Ai ko mutuwa na kunyar idon mahaifi. Haka kawai kin kashe auren ki kin addabi jakalle ta."
"Kin san abin da ta yi mini ne? Don ta gaya miki ƙarya sai ki kama? Ina cikin ɗaurin gyaɗata yarinyar nan, ta shiga har ɗakina ta iba gyaɗar ina jiran ta huce na ƙulla."
"Au Ashe ma ba bashi ta ci ba, Allah ya ba da kasuwa ta yi miki?" Kaka Tani ta furta cikin zallar mamaki tana kallonta.
"Kuma ba ki ga gyaɗar ba kaɗan na iba, domin da na san ba za ta haƙura ba, sai na ibo mana da yawa musha koko da safe da ita, amma ba ta iya suyan gyaɗata ba, duk ta ƙone ta yi baƙi." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ma kanta rankwashi.
"Ai da kin sani da kin ibo da yawa, tun da hakan bai hana ta biyo ki ba ." Ta ce tana kallonta.
"Yanzu abin da kike yi a Ƙauyen nan kuma kyautawa kuwa? Jikarki ta hana kowa saƙat kuma ba za ki iya tsawata mata ba? A yadda kike ba ta tarbiya, sai dai ta mutu a ƙauye nan, babu aure, domin babu wanda zai iya kwasar ma kansa bala'i."
"Au ke ma rashin tarbiyyar ya sanya ki gagara zama? Alhamdulillah tun da ba ita ta share fagen ba." Kaka Tani ta furta mata cikin gatsali.
"Sai aka ce miki zan yi aure? Ai ni da aure sai dai in ana yi a ƙiyama, saboda ba zan ɗauki wulakanci ba. Ke kanki kin san ɓalla mutum zan yi in har ya kawo mini raini."
"A'a Jimmalo, jikalle ta! Za ki aure kafin na mutu sai kin haifa yara na gani..."
"Allah Ubangiji ya kyauta! Ke ma kin san ba zan iya ɗaukar raini ba. Kina ganin Hamasiya da ta yi aure mijinta ya zane ta? Na rantse da ace nice sai na fitar masa da haƙarƙari."
"Ni fa ba wannan maganar na zo ji ba, a biyani kuɗin gyaɗata ko jiki ya yi tsami." Ma'u ta ƙarashe maganar tana jijjiga ƙugu.
"Na gaya miki ƙarfi ya ce daru ya hana." Ta ce cikin gatsali.
"Kina ganin rashin kunyar da jikarki take mini ko?"
"To so kike na daki marainiyar Allah? Yarinyar da aka mutu aka bar mini tana tsumma."
"Wallahi sai kin biyani kuɗin gyaɗata." Ta ce tare da cakumarta.
Ba tare da tunanin Ma'u mai gyaɗa ta girme ta ba, kawai ta daka tsalle ta wanka mata mari.
Ƙara ta saki cikin gigita ta fara dukanta. Taron dangi suka yi mata. Suka rinƙa dukanta tana ihu. Jin ihu ta ya sanya maƙota suka rugo da gudu.
A lokacin sun yi mata liƙis sai huci suke yi sun haɗa zufa." Nan gaba karya miki ƙafafun zan yi, kika ƙara gigin shgo mana gida."
Kowa ya kasa cewa komai, sai kallon Ma'u suke yi cikin tausaya wa, tare da ganin wutarta da ta shigo musu har gida, domin ta san cewa ko a waje suka yi ba ƙyale ta za su yi. Duk garin waye ba su takurawa ba.
"Wallahi sai na kai ƙarar ku gurin maigari, don ba zan haƙura ba."