← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harun ne kwance a hospital likitoci sun rasa gane kan ciwon sa anyi gwajin anyi amma duk shiru babu sakamako , kuma har yanzu jini zuba yakeyi kuma ana k'ara masa jini , mom tayi kukan harta gaji , hajiya ko kullum adu'a take kwara rowa Harun na Allah yabashi lafiya , suna zaune a kan tabarma sukaji sallamar momyn Bash cikin fara'a Hajiya da mom suka tareta ,ledace k'atuwa a hanunta cike da kayan mar mari , gakuma food flaks na abinci na farfesun kifi , gaisawa sukayi momy ta tambayi jikin Harun suka cemata da sauk'i , kasancewar doctors sunrufe k'afarsa babu wanda zai gane sai an gaya masa , momy ta d'an dad'e a hospital d'in daganan tayi musu sallama tare da ajiye musu ledoji ."

Kwance take tana bacci ,wani gun guni da taji ne yasata yin azamar mik'ewa da tsohon cikinta , agogo ta duba k'arfe 3pm na dare ,duba gefenta tayi babu Emanuel , a tsorace ta mik'e saboda jin wani gurnani dake tashi a gidan , wata k'ofa da tunda tazo gidan bata ta6a shigarta ba anan tajiyo gurnanin , tafiya yakeyi sad'af sad'af har ta iso k'ofar ,ta jikin wani huji na k'ofar ta lek'a , hango Emanuel da jajayen kaya tayi da wani k'o k'o a hanunsa bakinsa duk jini , jin kanta tayi yana juyawa saboda tsabar firgici , da sauri ta dawo ta kwanta cike da firgici ."

*GIDAN BASH*

Ya watsake sosai ,wanka yayi yasa kayansa masu kyau ya fito parlor ganin baiga budurwar tashi bane yasashi k'wala mata kira , ko ina ya duba babu ita babu alamar ta , wayarshi ce tafara ring ganin number Asma'u yasashi jan tsaki yace ”to kuma menene ?"cikin shagwa6a tace ”na haihu ina asibiti kuma gobe za'a sallamemu babu kud'i , Bash da yanzu haushinta yakeji , yashi cewa nawane kud'in ,dubu d'ari biyu cewar ,Asma'u , kan uba ubanwa kika mayar mai gonar kud'i bakida hankali ne baki da tunani ne , kokuma wani naki ya ta6a ciyar dani ? Asma'u da muryarta bata fita sosai tace ” Bash ,wlh kayi yunk'urin wula k'antani wlhi zan tona asiri , cikin zafin rai yace ”ki tona mana , y'ar talakawa kawai , wanan furucin ba k'aramin k'onawa Asma'u rai yayi ba , cikin hassala tace "wulak'ancin ya isa haka whattt, ki san dawa kike magana ,inace dai kud'i ne to zan turo turomin account , hmm (halinka da babu zuciya) tace ”toh ."

*NIGERIA*

Zaune suke su biyar kowa da bak'in kaya a jikinshi , wanan budurwar da sukayi sex da ita , duban wani mutumi tayi tace ”oga yakamata a kawo min wanan saurayin , wata muguwar dariya sukasa cike da jin dad'i oga yace ”lokaci muke jira karki damu nan bada jimawa ba ,wani mutum ne yashigo da jar hula yana tafiya yana dariya yace ”nifa na matsu nima yaron make jira , suka kuma shek'ewa da dariya tare da nuna video d'in da sukayi masa lokacin da suke sex ,fuskar Harun tafi fitowa sosai , oga ne yace ”duk da wanan videon da mukeda shi zamu k'ara had'awa da namu ."

Sumaiya ce zaune a parlor tana kallo a TV , Abbi ne yafito daga d'akin momy yace ”daughter ya kukayi da Mubin ?"sunkuyar da kai tayi k'asa tace ”Abbi yace ”baya sona, ehe shida bakinsa ya gaya miki hakan ?"eh Sumaiya tace ”tana girgiza kai alamun tabbatarwa , Ammi ce ta fito sanye da wani dakakken less mai adon duwatsu , zama tayi gefen Abbi tace ”ni a ganina yakamata mu bata za6i ko ?"Abbi ne yace ”tunda wancan yaron ya watsa mana k'asa a ido ai ba naman kai mukeyi da ita ba , ita dai Sumaiya na zaune bata k'ara magana ba , Abbi ne yace ”daughter ya kamata acikin mane manki ki fitoda mijin aure , Sumaiya ce ta shagwa6e fuska tace ”Abbi wlh sekuma ta mik'e ta ruga da gudu tana dariya , suma su Abbin dariya sukeyi ."

Momy ce zaune ita da dadyn Bash suna hira , kwanciya tayi a kan cinyarsa tace ”dan Allah kaje ka gaida Harun a hospital bashida lafiya , wata uwar harara ya daka mata tare da cewa shid'in kun had'a dangi ne dashi , kokuma ,yaron d'an uwanki ne ?"momy da ranta ya 6aci tace ”koba yaron d'an uwana bane ai mahaifinsa amana yabar maka , cikin fusata dady yace ”to bazan jeba ya mutu ,wayasani ma ko a yawon zinace zinace ya kwaso cutar , momy da hawaye ke ambaliya a fuskarta tace ”yakamata kasani Allah ne yayi mutuwar Muntari kuma kai.....wani mahaukacin mari dady ya wankawa momy tare da k'ara mata wani , da gudu ta shige bedroom d'inta tasa key ,takifa kai a gado tana kuka ,mai tsuma zuciyar mai sauraro ."

Harun dai na nanan inda yake sauk'i sai na Allah , dare babu bacci sai da rana amma daga Hajiya har momy babu mai bacci da daddare , adu'oi kan ana yinsu sai dai har yanzu Allah bai nufa yasami lafiya ba amma akace mai rai baya fidda rabo da samun rahamar ubangiji."

Alert ne ya shigo wayarta na dubu d'ari , tana dubawa ta buga tsaki umma dake gefe tace ”keda waye ?"Asma'u tace ”nida wancan shegen ne , Bash , umma ce tasa dariya da alamu dariyar takaici ce tace ”ai tare kuke kuma wlh Allah ki kiyayi had'uwarki da ubangiji ,nidai nayimiki tarbiyar iya iyawata amma dare d'aya kin watsar da komai , umma ta fashe da kuka , Asma'u ko ta6e baki tayi ta kawar da kanta gefe ....✍️.

Vote me on wattpad

Please share👏
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

My whtsapp group
https://chat.whatsapp.com/J7cmS5wP5fBHAnF0ut8905

Bakandamiya Mom Islam Habib

Facebook Mom Islam

*✨GODIYA TA MUSAMAN GA YAR MALAM NAGODE DA NUNA SOYAYYAR HAK'IK'A INA YINKI OVER WANAN SHAFIN NAKINE NABAKI SHI KYAUTA ✨*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 19 & 20

____Emanuel ne zaune da jayen kaya yana kur6ar abu wani jan abu , ya dubi shugaban su yace ”nidai ayimin rai kar a kashe ni ,zanyi k'ok'ari inga na kashe jaririn da Bahijja zata haifa ,shugaba ne ya shek'e da dariya yace ”kasan yanzu saura mutum uku ka gama koh ?" cikin rawar jiki Emanuel yace ”haba kuyimin rai a ina zan sami mutane kuma na jikina guda biyu yanzu , banida uwa banida uba duk nabawa dodo jinin su yanzu kuma kuce sai na k'ara muku ina , wata tsawa da shugaba ya daka masa ne yasashi tsorata , shugaba yace ”kasani kafin ka shiga k'ungiyar mu sai da kayi mana alk'awarin bada jinin mutum biyar yanzu kana so kace ,zaka yiwa dodo k'arya ko kuwa , a tsorace , Emanuel ya ce ”a 'a zan baku nayi alk'awari ."

Fans jinin wa Emanuel zai bada bayan jinjirin Bahija da yace ”zai bada muje zuwa.

Anbiya kud'in hospital dubi goma , su Asma'u sun dawo gida cikin k'oshin lafiya itada jaririn ta , ranar suna malm ya rasa wane suna zai sanya masa kwai ya Sanya masa Muhammad ,ranar suna mai jego ta tara k'awayenta , umma ko rasa wazata gayyata tayi sbda bata gaiyaci kowa ba kuma babu wanda ya lek'o gidan haka akayi sunan babu wani kaya da Asma'u tasamu dama umma tace ”mata duk mai cikin shege bazai ga dai_dai ba ."

Hutun Bash ya k'are yau jirginsu ya d'aga zuwa Nigeria , babu wanda ya gayawa gashinan zuwa kawar surprise ya shirya yiwa su dady , da saukar su ya trolley d'insa ya ya fita daga airport d'in ya nufi titi , motar haya ya hau ya nufi gidan su , mai gadi najin k'arar mota ya wangale get ya d'auka ko anyi bak'i ne , hango Bash yayi ya fito daga mota yana mik'awa mai mota kud'i , gyara zaman jakar dake rataye a bayansa yayi ya nufi cikin gidan , mai gadi ne yaketa jera masa sannu amma ko kallonsa bai yi ba ya shige ciki , da shigarsa ya bud'e k'ofar d'akinsa da take waje nesa da ta momy , samun d'akin yayi fess dashi babu datti kasancewar momy ba mace mai son k'azanta bace , kayan jikinsa ya fara cirewa yana gamawa ya shige toilet bayan yayi brush ya kunna ruwan d'umi yayi wanka , ya fito d'aure da tawul a jikinsa , yafara rawa , mayukansa masu k'amshi ya sa sanan ya fesa turarukansa had'i da ciro kayansa a drowa , riga da wando tsadaddu masu kyau , taje gashin kansa yayi ya sa takalmi ya fito zuwa part d'in momy ."

Samunta yayi zaune ita k'ad'ai a parlor tana kallo ta zuba tagumi , k'arasawa yayi babu salama yace ”my momy oyoyo ya rungumeta , momy ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata , Bash sam bai lura da halin da momy ke ciki ba , bubuga bayansa momy tayi tace ”my son babu sanarwa ?"dariya yayi yace ”momy surprise nayi muku , murmishi momy tayi tace ”kazo lafiya ya karatu , alhmdulilh my momy nasha karatu bakiga na rame ba ? kallonsa momy tayi tace ”naga dai kayi k'iba kuma ka k'ara fresh sosai , dariya yasa yace ”momy yunwa nakeji sosai , mik'ewa momy tayi ta je kitchen tasami y'ar aikinta na soya doya ,tace ”please had'awa son shayi karkisa madara , kasancewar bayaso , to Hajiya ,cewar y'ar aikin , dafa shayin tayi da citta da kaninfari da na'ana da lemon grass ,da lemon tsami kad'an ta d'auki jug da tirai da small spoon ta nufi parlor , samun Bash tayi a zaune kansa na kwance a jikin momy tayi sallama ta ajiye a dining , mik'ewa yayi ya nufi dining d'in yasa zuma yafara sha ."
Chapter 7 · 0% Book details