← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Masoya bazan gaji da mik'a sak'on gaisuwata a gareku ba sbda soyayyar da kuke nunamin nida kowane littafi nawa nagode🥰👏_

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 15 & 16

____Mutumin d'azu ne yakuma kiransa , k'in d'agawa yayi yana tsoron abinda zai biyo baya , wata zuciyar tace ”ka d'aga man , amsa kiran yayi yana salati a cikin zuciyarsa, he he he Harun yaji daga can 6angaren ,yaro yaro ne ,wato kana nufin mu bamuda wayo ko ,ha ha ha kayi blocking d'inmu a watsapp bakasan gidan da kake muna bibiyarsa ba hhhh , innalilahi wa inna ilahairraji'un na shiga uku ,cewar Harun , jiyayi kansa na juyawa ya fad'i a gun sumamme , k'arar buguwar abu momy taji ,hakan yasa ta nufi d'akin , Harun da sauri , samunsa tayi kwance a sume ko nunfashi bayayi , abinka da mai ara har hawaye , momy tafara kuka ta nufo d'akin Hajiya da gudu tana cewa ”son _son Hajiya tace ”meyayi ?"kuka yaci k'arfin momy takasa magana , Hajiya ce ta mik'e ta biyo momy suka nufi d'akin Harun , samunshi sukayi kwance ya mirgina gefe can kuma y'an yatsun k'afarsa jini ne ke fita a kowane farce na k'afarsa , ganin haka yasa momy k'ara kid'imewa ta rusa ihu ta fad'i sumammiya , Hajiya tarasa wazata kama wa kuma zata bari kawai tazauna ta zuba uban tagumi tana kuka , tana cewa "Allah ka duba lamuran mu Allah ka sauk'ak'a mana wanan matsala , wasu hawaye masu zafi suka zubo mata , jiki babu k'wari tayi bakin get kasancewar mijinta yatafi Dubai , driver da mai gadi takira da gudu sukazo suka tsuguna , Hajiya dake share hawaye tace ”temako zakuyi min ,cikin rawar jiki sukace " to Hajiya , kubiyoni ciki ,tana gaba suna binta a baya haka suka shigo d'akin , da shigarsu sukaji mom nata wasu surutai ,sosai Hajiya takuma tsorata dan mom bata ta6a yimata haka ba ,mai gadi da driver ne sukayo kan mom k'o k'arin dagota sukeyi amma sun kasa ,Hajiya ce ta taho tace ”kuzo mu kamata ina ko k'afafuwanta babu wanda ya iya d'auka , rud'ani tashin hankali firgici duk Hajiya ta shiga ."

Waya ta d'auka takira wasu y'an uwanta ,basu d'au dogon lokaci ba sai gasu sun iso su uku ne samari ,d'akin da mom da Harun suke ciki Hajiya tayi musu bayani , shigowa sukayi suka fara aikin temako , da mai gadi da driver da Hajiya da y'an uwanta guda uku mutum shida ,dak'yar suka d'aga momy , suna nishi adu'oi Hajiya tadinga kwararowa mom tare da yayyafa mata ruwan adu'a atishawa mom tayi tana farkawa tace ”ina son , dagudu ta fice ,zuwa gurin Harun dake kwance kamar gawa jijigashi takeyi iya k'arfinta amma shiru ga jini yana fita ta farcen k'afarsa kad'an k'adan....

Cikin Asma'u yashiga wata takwas ,Bash ya turo mata kud'i masu yawa , tayiwa jinjiri siyayya , wanan lokacin Asma'u na cikin farinciki da nishad'i kasancewar sai abinda ranta keso takeci , bata nunawa umma iya adadin kud'in ba dan a k'alla kud'in zasuyi dubu d'ari , dubu hamsin taba umma , abinci sai wanda ranta keso ,rubutu ko da adu'oi duk malam nayi mata a cewarsa hanunka baze ri6e ba ka yanke ka yar, tana cewa Bash batada kud'i yake turo mata baya yimata musu ,kasancewar tace ”zata tona masa asiri ,dakuma gidansa da babu wanda yasani , sunyi siyayya sosai itama tayi d'inkuna dan burin Asma'u taganta tana shiga wancan tana fita wanan ."

Sumaiya ce tabada cigiyar Harun da a cewarta indai ba Harun ta aura ba to bazatayi aure ba har abada , wata rana suna zaune a dining itada momman ta da Abbi wato (babanta)suna breakfast , ya dubeta yace ”daughter na'am tace ” tana karkad'a cokalin hanunta , inason zamuyi wata magana , to Abbi ,momma dai na jinsu batace k'ala ba , yau zakiyi bak'o , cewar Abbi zaro ido Sumaiya tayi tace ”Abbi bak'o kuma?" eh yace mata ina fatan dai bazaki bani kunya ba ko?"uhm insha Allah , fuskarta babu wal wala , bayan sun gama abinda zasuyi ta shige bedroom d'inta ta shiga gallery gurin pics d'in Harun wanda tayi masa besani ba tadinga kissing d'insu tanaji kamar tana tare da Harun ne , kira ne yashigo wayarta , rashin gane ko waye yasata danna busy ,sai da akayi sau uku sanan ta d'aga , batayi magana ba , tayi shiru , mai kiranne yace ”barka da wanan lokaci sarauniyar kyawawa , ya jindad'i wata uwar harara ta zabga kamar yana kallon ta tace ”kai malam bansan ko kai waye ba kuma bansan daga ina kake ba zakazo kana yimin wata magana kamar ta y'an koyo."

Daurewa yayi yace ”wato bakisan ko waye ba ?to nine yaron wanda mahaifinki ke aiki a company d'inshi , da alamu bakisan koni waye ba ,karkiga na tsaya ina yimiki magana kiyi tunanin ina barar soyayyarki ne no , kema in tursasaki akayi to ki gayawa mahaifin naki bakya sona so nima na fad'awa dad d'ina bana sanki kinga munsamo wa kanmu mafita , hak'ik'a wanan maganar ta 6atawa Sumaiya rai sosai zuciyarta kamar zata fashe ta wurga wayar kan gado tana huci ."

Yau kwanan Bahijja biyar a gidan wanan k'aton mai suna Emanuel , soyayya yake nuna mata sosai yanzu ma bata fita bare ta kula kowa ,shiko Bash bai damu da rashin Bahija ba tunda dama ance barki ... wata rana suna zaune itada Emanuel take gaya masa maganin planing d'inta ya k'are , janyota yayi ya d'orata a kan cinyar sa yana wasa da gashin dokin , datasa a kanta , yace ”beb karki damu da hausarshi da bata game bakinshi ba , a zabure Bahija ta mik'e tace ”ban gane ba shiii yace ”mata alamar tayi shiru don't worry just ki manta kawai , cikin fushi ta mik'e zata fice ,ya janyota yafara yimata nasa salon mancewa tayi da maganar magani suka fad'a duniyarsu ta shed'anu."

Shiko Bash ya had'u da wata yarinya wace ake yayi y'ar India samari ke rubibi a kanta , kasancewar ta lula a soyayyar Bash yasata dena kula kowa sai shi gida ya kama musu mai kyau amma madai daici , sunkoma kamar mata da miji sosai suke k'aunar junan su ."

Yau watan bash uku yana cikin na hud'u ,a India , zaune suke shida baturiyar sa suna holewa a wani katafaren gurin wasa , daga shi sai gajeren wando iya cinyarsa babu riga , lol baturiya kuwa skirt ne dashi da babu duk d'aya sai wata riga mai shara_shara , Bash ne ya janyo hanunta tare da cewa "zomuje mu huta , bai gama rufe baki ba , abinda ya hango ne yasashi mutsike idanunsa ....

Asma'u tashiga watan aihuwa umma ce da malm a asbitin, dan babu wanda ya rako su , mutane sai tsegumi sukeyi , umma dai bata kula kowa ba ta me aihuwa takeyi , tun karfe takwas na safe Asma'au ke nak'uda gashi yanzu k'arfe hud'u na yamma shiru wuya kam Asma'u tasha , doctors ne suka cewa su umma inhar Asma'u ta wuce biyar na yamma to tiyata zasuyi mata , cikin tashin hankali malm yace ” wa umma to yanzu a ina zamu samo kud'in tiyatar nan , umma dake share hawaye tace ”wanan yarinya ta janyo mana abinda yafi k'arfinmu wlh...✍️.

Wow my pans mom Islam tana yinku kamar inda kuke yinta wlh kuna matuk'ar ji dani to nagode 🥰Allah yabar love muje zuwa 🤙.

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 17 & 18

____Bahijja Bash ya hango ita da Emanuel ga k'aton ciki a gaba , rik'e suke da hannun juna suna tafiya suna dariya , daka gansu zakasan suna cikin farinciki , kasa kawar da fuska Bash yayi yana dad's k'arewa Bahijja kallo ,shin ta yarda ta d'auki ciki da wanan k'aton arnen tabb Bash yace ”yayinda ya mik'e ya nufi gurinsu , da zuwanshi yace ”Bahijja ?"ko kallon sa Bahijja batayi ba ta maida kai gefe tana rik'e da hanun Emanuel , Emanuel da hankalinshi yayi gaba ya sunkuceta suka bar gurin , Bash kuwa yashiga tashin hankali , sosai ,a ranshi yana cewa tare mukazo ta gujeni taje ta d'auki ciki da k'aton arne , budurwar shi ce ta matso kusa dashi tana shafa masa kai tace ”meya faru ne my man , idanunsa da sukayi Ja jawur yace ”bb komai zomutafi , after dree budurawar tasa suka wuce gidan nasu , da shigarsu bashi ya bud'e kwalbar beer sha yakeyi kamar an aikosa , sanda ya cika cikinsa tabb da giya sanan ya kwanta yafara surutai marasa kan gado ,budurwar sa ce ta rungumo shi tana tambayarshi meyasa zesha over ?"ina Bash yayi nisa bayajin kira ,wata gyatsa yake fitarwa mai wari sosai , da haka ta gyara masa gurin kwanciya ta barshi a gurin ."

Ana shirin shiga da Asma'u d'akin tiyata ,tafara yunk'urin aihuwa , malm da umma ko sai adu'oi suke jero mata suna daga waje dan ba'a barsu sun shiga ba , cikin ikon Allah ta haihu nurses ne suka gyra jaririn tare da yimasa wanka , jin kukan jin jiri yasa umma nufo d'akin ,lokacinma angama gyara komai saura mai jego tayi wanka ."

Malam ne zaune a masallaci yana adu'ar Allah yabasu kud'in biyan asibiti , ya shafa adu'ar gami da mik'ewa , ya nufi cikin asibitin , samun Asma'u yayi tana kwance ,lokacin tayi wanka ."
Chapter 6 · 0% Book details