← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa yamma Asma'u taji dad'in jikinta amma ta rame sosai , fitowa parlor tayi bayan tayi wanka ta kunna TV , Zuby ce tafito sanye da doguwar riga iya guwaiwa , ta zauna a parlor , kujerar dake kallon Asma'u ,tace ”ya jikin ?"da sauk'i Asma'u tace ”zuby ce ta mik'a mata kud'i , zaro ido Asma'u tayi tace ”wanan fa ?"karki damu dubu d'ari biyu ne karki damu yanzu kika fara kama dollars , murmishi Asma'u tayi , tace ”nagode sosai samun k'awa irinki wlh sai an tona suka tafa."

To yanzu ya maganar auran da kikace saurayinki zaiyi , yaushe zamuje gurin boka , Asma'u ce ta kalli kud'in hanunta tace ”banason ta6a wanan kud'in , dariya Zuby tasa tace ”karki damu ga 50k sai muje gobe , daganan suka sauya hirar tasu ga duniyarsu ."

Kwana uku kenan da bikin Bash ,soyayya kamar zasu cinye junansu , Basma tayi kyau a tsakanin kwanakin gashi tasami mazauni a zuciyar Bash , bata bari ranshi ya 6aci haka shima bayason 6acin ranta , da sallama ya shigo tanajin shigowarsa ta ruga da gudu ta rungumeshi juyi yafara yi da ita bai direta ko inaba sai tsararen gadonta , ya fara yimata wak'a tana dariya , zomuje muyi kallo , mik'ewa sukayi rik'e da hanun juna , Harun ya kunna TV ya rungume Basma 🙈lamarin n masoya ne lol , misalin k'arfe goma sha biyu , suka shiga kitchen sukayi girki , kowa ya shigo gidan su Harun baya fita bai d'auki wani darasi na soyayya ba."

Washe gari suka shirya zuwa gidan su Harun , siyayya sosai suka yimusu , tafiya sukeyi cikin nishad'i Bash na tuk'i hanunsa na kan na Basma idanunsa ma na kanta , a haka suka isa gidan , yana parking d'in motarsa suka fice , sukayi cikin gidan ,da shigarsu sukaci karo da mom , cikin fara'a ta tari Basma ta rungumeta , Hajiya na fitowa ta fara rawa tana cewa "ga ango ga kishiyata yau nice da ango sukasa dariya , zama sukayi aka fara gaisawa , kowa fuskarsa cike da fara'a ."

Girki na musaman aka yiwa amare ga farfesu na kifi dana kaza ga lemu da mom suka had'a itada Basma , mom taji dad'in samun suruka irin Basma batada duhun kai komai nata cikin nutsuwa takeyi , gida dai yacika da farinciki sosai ."

Da dady akayi bikin Harun sai dai bai cika shiga mutane ba sbda wani gargad'i da beauty tayi musu shida Bash , rabonshi da fita gurin aiki yayi sati biyu , kuma ya hana momy zuwa gurin bikin taci kukanta har tagaji, wanan d'akin da Harun yata6a jin dady na waya harya tsorata ,acan yake kwana yanzu baya wuni a cikin gidan gashi yanzu momy tarasa gane kan dady itadai tana ganinsa yana hidimarsa batasan me yake aikatawa ba ."

Malam ya tashi da amai da gudawa , tun ana k'irga ledar ruwa har Umma ta zubawa sarautar Allah ido , gashi duk kud'in da Asma'u ta bar mata sun k'are gurin jigilar magani , Umma tarasa wane guri zataje nemo kud'i , ga malam kwance ya kwanta a asibiti , sunfito babu kud'in magani ga yaron Asma'u na kashin hak'ori ,ya rame sosai damuwa ta taru tayuwa Umma yawa ,wani lokacin ta zauna a d'aki tayita kuka wani lokacin tai alwalah takai kukanta ga Allah."

Yau da bikin Sumaiya sati biyu kenan tayi fari tayi k'iba sosai , Khalid ne yashigo da 3 quarter yana rawa yace ”my princess tauraruwa zomuyi rawa ,d'agata yayi yana juyi yana rawa da ita ,suka hau dariya , albishirinki, sumaiya ce tace ”goro , nabiya mana makka , a zabure Zumaiya ta mik'e tace ”dan Allah fa ,suka sake kid'a suka fara rawa , hhh kowa na nuna iyawarsa , saida suka gaji sosai sanan suka baje a kan capet suna hutawa , da gudu sumaiya ta mik'e tayi bedroom d'inta , toilet ta shige rik'e da bakinta , wani amai ne ya taho mata ,Khalid ne yabiyo bayanta da sauri ya rik'eta ,meke faruwa ne ?"a wahalce tace ” amai saida tayi aman mai yawa zata zauna a toilet d'in Khalid ya wanke mata baki ya fito da ita ya kwantar da ita a gado lulu6eta yayi da blanket , ya zauna kusa da ita ya zuba tagumi kamar ba d'azu suka gama kwasar rawa ba ."

Wani jeji suka shigo mai cike da bishiyoyi iri iri bakajin k'arar komai sai na tsuntsaye , Zuby da Asma'u ne tafe sai nunfar fashi zukeyi , Asma'u da tagaji tace ”zuby nagaji mukoma zare ido Zuby tayi tace ”wlh babu inda zamu koma muzo har nan d'in kice mukoma tabb , wata tafiyar mai nisa suka kumayi ,jiyo wani irin gurnani ne zai tabbatar maka da anzo gurin hatsabibi , ya Allah ka tsare mana zuciyoyinmu, wata mahaukaciyar dariya Asma'u ta jiyo dan Zuby komai na gurin ba bak'onta bane tasaba , Asma'u ce ta k'ank'ame Zuby a haka suka k'arasa gurin , da zuwansu boka yafara yare ,Asma'u ko tana ganin kamaninsa sai da ta tsorata , kanshi gashi ne a murd'e ga wasu uban wuri daya rataya a wuyansa k'afarshi kuwa ganyene a d'aure ga layoyi , zama sukayi a gabansa Zuby tafara yimasa kirari ,washe bak'ak'en hak'waransa yayi yace ”inajinku meke tafe daku ?"dukda aljani firsus ya bani labari zanso ji daga gareku ...✍️.

Please share👏
Vote me on wattpad

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 49 & 50

___ Asma'u ce tace ”so nakeyi a hanasu zaman lafiya kuma , matarshi ta zamo kamar dodo inya kalleta , wata shu'umar dariya boka yayi yace ”karki damu komai zaiyi dai dai , kud'i Zuby ta mik'a masa ya mik'o mata wata laya bak'a , yace ”wanan ki hak'a rami ki sata a ciki , ki d'ibi tafasashen ruwa ki kwara a gurin , ya shek'e da dariya ,kana yace ”kowa bazaiga kamaninta ba sai mijinta , kutashi ku ficemin ."

Da baya suka fita har suka wuce gurin bokan suka kuma tafiya mai nisa ,sanan sukazo gurin motarsu , farinciki fal zuciyar Asma'u ,amma a k'asan zuciyarta tana tunanin , shirinta na gaba akan Bash ne , suna tafiya cike da nishad'i , suka tsaya a wani katafaren gurin abinci , I scream suka buk'ata tare da sauya salon yangarsu , wasu mazane suka taho da alama suma y'an yine , zama sukayi a nesa ta kujerunsu , suna aika musu da murmishi , Zuby ce ta kashe musu ido d'aya tare da cewa hi d'ayanne ya taso yana washe hak'ora ya kamo hanun Zuby ,shikuma d'ayan ya rungumo Asma'u , wata galleliyar mota ce tai parking a gefen titi ."

Wasu mata na hango guda biyu , sun fito daga motar ko wace da glass no respect a idanta , direct gurin su , Asma'u suka nufi gasu jibga jibga , wani wawan mari ta wankawa Zuby d'ayan ta cakume wuyan Asma'u , nanfa kokawa ta 6arke aka had'a harda mazan ana kaimusu naushi , da 'alamu dai matansu ne shiyasa sukayi muk'uss."

Zuby taja hanun Asma'u suka shige mota da uban gudu sukahau titi , sunyi tafiya mai nisa suka iso gidan , mai gadi najin k'arar motar ya mik'e da gudu ya bud'e get , a guje ta shige ciki , goshin Asma'u na tsiyayar jini , cikin tashin hankali Zuby ta kama hanunta suka shige ciki , doctor ta kirawo yace ”gashinan zuwa , bai jimaba ya iso kasancewar baya 6atawa Zuby lokaci a gunta yana samun kud'i sosai dan ha r ciki yana zubarwa hakan yasa Zuby batada wani doctor sai shi doctor Sameer kenan babanshi babban likita ne Allah ya yimusu arziki sai dai yanada auri saki , kuma duk matar da ya aura bata aihuwa , haryanxu Allah bai bashi ba , shiyasa ya d'au alwashin zubarwa da mata ciki subhanallh 😥."

Yana zuwa ya wankewa Asma'u ciwon yabata magani ,Zuby ta biyashi yai gaba , gani nayi Zuby ta mik'e a razane tana duduba jakarta , zuge zip d'in tayi naga tana zaro ido cikin firgici , kardai na yarda layar nan a gurin fad'a , nashiga uku , in Asma'u ta sani nasan bazata koma ba , tayi dube duben harta gaji bataga laya ba , hankalinta ya matuk'ar tashi ."

Malam ne ya shigo da tabarma a hanunshi Alhmdulilh yaji sauk'i sosai , yaron ma ya warware , Allah cikin ikonsa ya yalwata masa acikin almajiran da yake koyarwa wani ya bud'e masa shago a k'ofar gidansa , yana saida su shinkafa wake madara sugar da sauransu , cikin sati biyu Allah yakuma buk'asa shagon yanzu kam Umma hankalinta yafara kwanciya ba kamar da ba tayi k'iba sosai ta murmure , shima jaririn yana samun madara akan kari."

Tunda Emanuel yakai report , gurin jami'an tsaro suka kamashi suke gana masa azaba , sunyi neman abokan harkar tasu sun rasa , kasancewar suna had'awa da tsafi , shiko gashi a hanunsu bashida sukuni har sai ya fad'o musu gaskiyar inda abokansa suke , yayi kukan yayi rok'on ya rantse amma duk a banza ."

Zaune dady yake a d'akinsa na sirri ,ya rufe ko ina babu haske wani jan abu nake hangowa dishi dishi ko meye oho ...
Chapter 19 · 0% Book details