← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumaiya da Khalid ne suka nufi hospital , test akayi mata da saurnsu , likita ne ya mik'awa , Khalid hannu yace ” kyakyawan albishir kakusa zama baba , matarka na d'auke da cikin 2 weeks , tsalle Khae ya doka dama shida matar tashi ba baya ba gurin rawa yana yiwa doctor godiya , d'akin da ake k'ara mata ruwa ya nufa , saura kad'an ya k'are , bud'e idanta tayi tace ” Prince K nagaji da kwanciya ,ta kashe masa ido , oh pans kuzo mud'au darasi kullum canzawa kansu suna sukeyi 🤔shafo cikinta yayi yace ”baby ka huta sosai karka wahalar da momy , Sumaiya bata gane me yake nufi ba tace ”baby kuma ¿"eh a cikinki ba ,dariya tasa ta 6oye fuskarta cikin tafin hanunta , Khalid ne ya dubeta yace ”kunya ko , zaki sani ,yanzu mekikeso kici ?" cikin shagwa6a tace ”wainar fulawa ,tuntsirewa da dariya yayi yace ”to menene hakan ?".

Misalin k'arfe biyar na yamma suka bar hospital , aka dawo gida ,abu kad'an Khalid yayi Sumaiya zata shagwa6e fuska , yanzu dai tunda Sumaiya tafara laulayi , shi kad'ai ke rawarsa tana dariya , yau befita ba kasancewar lahadi ne yana kitchen gimbiya na kan doguwar kujera tana ganin girkin , awara sukayi ko ina yayi biji biji , Khalid kuwa yakoma abin tausayi dan hanunshi zuwa fuskarsa duk k'ulin awara , gashi Asma'u tak'i sa hannu sai dai tadinga cewa haka zakayi , harda aiken mai gadi aro musu abin tata ,haka dai sukayi awarar da tsami gaye hhh , a fagen suya , Khalid ya yarfe hannu yana shirin fita ,Asma'u tasa kuka tace ”wlh inbaka soya minba zanta tsalle inta tsalle kumadai kasan doctor yace ”banda aikin wahala harsai cikin ya girma ko ?"da sauri ya k'araso ya rik'eta yana am sorry my princess zanyi jeki zauna , an sa a tirai an yayyanka , aka sa mangyad'a a wuta aka zuba ruwa a roba da gishiri da maggi , ya fara d'iba yana zubawa , wani tsalle da man yayi sai a k'afar Sumaiya da gudu ta mik'e tafara kuka tana tsalle."

Hankalinshi na gurin suya yace ”dan Allah kidena tsalle kiyi hak'uri , zama tayi tana fifita k'afar ,da Khalid yazo yaga k'afar gurin ma kad'an ne babu dai halin yin dariya ne , tasa masa kuka , yana kwashe kaskon farko ta kwashe a plet , tasa yaji , Khalid ne yace ”wlh Sumaiya bakida.... bai k'arasaba Sumaiya tafara bubuga k'afa tana cewa toni ba mai ciki bace ? dole fa kadinga lalla6a ni wlh ko indinga tsalle , shidai Khalid ya gaji sosai yana kwashe kasko na biyu ya kashe gas d'in ya kwashe a plet ya fice , tana zaune , takusa cinyeta tana jiran ya kwashe yakuma zubo mata ,da sauri ta bishi ,ina harya kulle k'ofar da key , dole ta koma kitchen tacigaba da suya."

Tanayi tana dangwala da yaji , shiko Khalid wanka yayi ya canza kaya , ya shafa mai ya sanya hula da turarensa mai d'aukar hankali ,ya fito kamar bashine mai aikinnan ba , kitchen ya nufa ,samun Sumaiya ta kuk'e tana suya ,k'unshe dariya yayi yace ”mom twins ya aiki tare da sunkuyawa ya shafo cikin ,lumshe ido tayi tace ”to inakuma zakaje ?"maida mata maganar yayi kamar inda tyi masa a shagwa6e , uhm zani gurin Ammi ne da Abbi ,in gaishe su....✍️.

Please share 👏
Vote me and follow me on wattpad

[26/02, 6:13 am] Mom Islam ce💃: ♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 51 & 52

____Yau satinsu Harun biyar , Basma tayi kyau ta k'ara haske ga kumato lol , tafe suke a mota itada Harun zasuje gidansu momy , da isarsu ,yayi horn mai gadi ya bud'e musu , washe baki idi yayi yace ”kaga angon dariya Harun yasa lokacin da ,yake fitowa a mota , Basma ma tafito , tana sanye cikin shadda maroon color da wani tsararen aiki wanda rabi shine a jikin rigar , gyalen a k'afad'a ta yafa , hakama Harun shima kalar shaddar ce a jikinshi , kai tsaye part d'in momy suka nufa , tana zaune a parlor tana kallo , ganin su yasata fad'a d'a murmishinta , tace ”amare barka da zuwa , tana mik'owa Basma hannu alamar tazo , zuwa kusa da ita tayi ta zauna ,cikin girmamawa suka gaisheta , harunne yace ”dady nanan kuwa ?"eh momy tace ”lokacin da take mik'ewa , yana part d'inshi , okay Harun yace ”barin lek'ashi , please Basma ki jirani in sanarwa dady na , hanyar sashen dady ya nufa ,da isarshi d'akin , yajiyo wata mahaukaciyar dariya had'e da maganganu wanda k'wa k'walwarshi bazata d'auka ba , cikin zafin rai Harun ya fara bugun k'ofar dady yana gurnani na 6acin rai ,k'ofa dai tak'i bud'ewa dady yana surutansa da alamu waya yakeyi."

Momy ce ta fito a guje ta rik'e Harun tare da cewa meke faruwa ne my son naganka haka ,babu magana Harun ya ture momy gefe idanunsa sunyi jawur alamun 6acin rai , wani duka da yakaiwa k'ofar ne yasa bud'ewa , momy na gefe ta mik'e ta share hawayenta ,ta wuce parlor taja hanun Basma suka wuce bedroom d'inta , tinkarar cikin d'akin da baka ganin komai sai duhu , babu haske a parlor , haka yadinga shiga yana gurnani kamar zaki , d'akin da yakuma jiyo magana a karo na biyu ya tinkara , hango dady yayi da bak'in kaya a jikinshi da jan k'ok'o ga wani mutum ,k'waran gwal da alamu ba yaro bane ."

Harun ne ya cakumo wuyan dady , tare da buga kansa a bago yace "wlh ko ka kasheni ko in kasheka na rantse da mahalicci na sainaga bayanka ina mahaifina yake ?" Dady ya shek'e da dariya yace ”oho kabani ajiyarsa ne ?"wanka masa mari Harun yayi tare da cewa wlh yau zan kasheka kokuma na kasara ka dan bakada amfani bkada tausayi bakada imani , meyasa zaka kashemin ubana , kabarni maraya , uwata kuma ka rabata da mijinta mezakaje ka cewa Allah, yana kuka yana jijiga dady , shiko dady tsabar ya jigata layi ya fara yana cewa tsaya zan gaya maka , yayi dai _ dai da shigowar momy d'akin idanunta sun ciko da hawaye , batace komai ba itadai tana kallonsu , Harun ne yaja dady ,yace ”kai ka turo aka kashemin mahaifina ko , wani matsanancin kuka Harun yakeyi mai cike da tausayi , dady ne yace ” YUSUF!!!!....wani mahaukacin kud'i ne ke zubowa daga bakin wanan k'waran gwal d'in , zaro ido momy da Harun sukayi tare da rufe baki da hannu ."

Innalilahi wa ina ilaihirraji'un yanzu dady rashin tausayi da imaninka harya kai ka maida mahaifina dukiya , dady ko a jikinshi , kukan kura Harun yayi yafara jibgar dady yana kuka yana kalon abinda aka kira kud'i ya zubo, da sauri momy ta fito parlor ta d'auki wayarda data ajiye akan kujera tafara lalubar number mom , cikin sa'a number tashiga , as.... wani mari taji an wanketa dashi cikin kid'ima ta juya dady tagani , d'aure da hannaye ,fitowar Harun ne yasata komawa bayansa , momy ce takuma kiran wayar mom , cikin sauri tace ”wlh kuyi sauri kuzo kuga abin mamaki ,kuyi sauri ta k'arashe zancen da kuka mai cin rai , Bash ne yashigo sanye da doguwar riga jallabiya , gurin mahaifinsa ya k'arasa daya ganshi a k'ulle, wani wawan mari Harun ya kaiwa Bash , daganan fad'a ya sauya gashi dady babu halin temako duk Harun ya d'aureshi , kuka sukaji na wata murya wacce bata gidan ba , Basma ce raku6e a gefe tanata kuka ."

Momy bataso fitowar Basma ba amma aikin gama ya gama tunda taji komai kuma taga komai , shigowar mom da Hajiya da Alhaji yasa kowa maida hankalinsa gurinsu , amma banda Harun da yaketa kaiwa Bash duka ba ji babu gani ,Alhaji ne ya k'araso a fusace ya wanke Harun da mari mom ma ta k'ara masa , kukan kura Harun yakumayi a karo na biyu ya cakumo dady idanun Harun sunyi ja kamar gaushi ya turashi , d'akinsa yana cewa , ka nuna musu wulak'ancin da kayiwa mahaifina , yana kuka yake maganar , dady da zuciyarshi a halin yanzu ta bushe babu tsoro a cikinta yace ”bazan fad'a ba , Harun na marin dady Alhaji na marin Harun cikin fushi momy ta k'araso tace ”Alhaji bakasan dalilin kiranka ba ,dazakazo kana dukansa wlh MUNTARI shine abin duka."

Hanun mom momy ta kamo suka shiga d'akin dady , itadai mom na biye da momy wani d'aki suka shiga mai komai na cikinsa ja , hango k'waran gwal mom tayi ,momy ce tayi mata nuni da hannu , momy tace ” YUSUF!!! mom taga kud'i yana zubowa daga bakin abin , cikin firgici mom ta fice da gudu , Alhaji ne yayi nasarar kamota saboda yasan ,halinda zata shiga bata iya kallon 6acin rai , cikin surutanta , tace ”wlh shine ya kashemin miji kuma bazan barshi ba , gida ya kacame da tashin hankali , ga Basma na kwance zazza6i mai zafi ya rufeta , Bash tunda ya fita da gudu bai dawo ba ,ga mom tanata surutai momy kuma na kuka ,Harun na shirin kaiwa dady naushi Alhaji na tareshi ."

Hango Bash sukayi a hanun wata budurwa , dady na ganinsu ya sunkuya da niyar guduwa yaji an cafkeshi , budurwar tace ”dama nace ”saina tona asirinku ka fad'a da bakinka waye ya kashe mahaifin wanan yaron ,Bash da yasami Halin guduwa gurin momynshi yace ”BEAUTY!!! karki k'ara danganta mahaifina da wanan bak'in lamarin , yana rufe baki yaji an shak'oshi , baiga kowa ba yasashi , zaro ido tare da rik'e wuyan yasan wanan aikin na beauty ne."
Chapter 20 · 0% Book details