← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basma ce ta shirya cikin doguwar riga bak'a mai adon duwatsu da d'an k'aramin hijab fari mai kyau , jakarta ta d'auka dama tun jiya ta gayawa momynta zataje gidan su mom d'in Harun , turaruka masu k'amshi ta bata dakuma turaren wuta , kasancewar su y'an Meduguri , bata d'auki driver ba , ita da kanta take driving , super market ta nufa , siyayya tayiwa mom da Hajiya dakuma uwa uba Harun , ta sa a booth , tana cikin tafiya ne ta hango agogon hannu a wani shop , parking tayi ta shiga shagon , za6o masa wani mekyau tayi tare da zobe mai tsada da turaruka masu k'amshi , da isarta tayi horn mai gadi ya bud'e mata , get , kasancewar ya ganeta , parking tayi a parking spice na gidan , ta fito ciro kayan tayi a bayan mota , da gudu mai gadi yazo ya kar6i kayan ya shige dasu , itama shiga tayi , a parlor ta tararda mutanen gidan amma Harun bayanan ,mai gadi na shirin tafiya ta mik'a masa dubu d'aya , har k'asa ya durk'usa yana yimata godiya , hakan da Basma tayi takuma samun gurbi a zuciyar mom ...
Hajiya cikin murna tace ”wanan itace kishiyar tawa , sukasa dariya , har k'asa ta durk'usa ta gaida mom da Hajiya , Hajiya nata tsokanar ta , samun gurin zama tayi tare da , ciro wayarta ta aikawa da Harun sak'o ....✍️.

👏masu sharhi ina godiya da soyayyarku a gareni kuyimin afuwa kunsan jiki da jini kuma dai yauma banajin dad'i wlh , karkuyita jirana ne yasa nayi muku 🤙.

Comments &sharhi
Vote me on wattpad

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

*MASU SHARHI KUYI HAKURI NA JINA SHIRU INA GODIYA NAGODE DA NUNAMIN SOYAYYA NATASHI LPY NAKUMA JI SAUKI ALLAH YABAR ZUMUNCI HAKIKA KO NAYI FUSHI KUNA SANI FARINCIKI 🥰*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 33 & 34

____ Soyayya dai tayi gaba , dan tsakanin Harun da Basma babu mai bacci ba tare da yaji muryar d'an uwansa ba, soyayya sukeyi mai tsafta dakuma amana , yanzu ma Harun ya zamo d'an gida a gidan su Basma , momymta kuwa kullum yabawa takeyi da hankalinsa , gashi biki nata matsowa , komai cikin nutsuwa sukeyi , Basma kuwa tun tanzu tafara shan gyara , tayi kyau tayi haske gwanin sha'awa ."

Muhammad d'in Asma'u yayi wayo sosai dan yana koyon zama , yanzu , Umma ce ta shigo d'akin da take zaune a ciki , Asma'u ce ta canza fuska tace ” Umma gyaran kayana nakeyi , jikin Umma a sanyaye tace ”Asma'u ,waye yabaki kud'in danaga kike wadak'a dashi ?"d'an hararar Umma tayi tace ”nikuma ?"wane kud'i ?"sarai Umma ta gane so takeyi ta kawar da zancen , Umma ta dubeta tace ”wlh kibi duniya a sannu ina tausaya miki Asma'u , kullum sai naga takardar tsire da gwan gwanin madara , waye yake baki ?"nasan dai tunda kikaje kikayi abin kunya babu d'an arzik'in da yake zuwa gurinki , kuka Asma'u ta fashe dashi mai cike da munafurci , tace ”yanzu umma ni kike zargi ?"mik'ewa Umma tayi tabar d'akin , tana fad'awa d'akinta ta fashe da kuka , tana cewa "ka haifi d'a baka haifi halinsa ba yanzu rayuwar da yarinyar nan ta jefa kanta tana ganin yayi kenan ."

Zaune suke cikin wasu bak'ak'en kaya , da tsogon dare , lokacin ma k'arfe biyu dai dai , wata mahaukaciyar dariya ce ta ke tashi a fad'in gurin , ogan su dake zaune da jan kaya da bak'i yace ”kai munyi jiranka har mun fara gajiya , wai yaron yafi k'arfinku ne ?"cikin rawar jiki wanda aka yiwa magana yace ”ba haka bane ,yaron yanzu ko d'akinshi dodo baya iya zuwa , wani ihu ne ke tashi kuma duk dodon ne mai hakan , shugaban su yace ”wanan fa kawowar da zakayi bawai iya dodo ne zai amfana da abin ba kaima yazamo arzik'i a gurinka ."

Cikin sanyin jiki yace ”to zanyi k'ok'ari inga na kawo , daganan kowa ya watse .

Bahija ce zaune ita d'aya a d'akin ta , wayarta ta ciro , ta kunna dan tuda tazo bata wai wayi wayar ba , gurin sak'onni ta fara dubawa , cin karo tayi da sak'on Emmanuel bud'ewa tayi tana karantawa ,

_my Bahija meyasa kika gujeni kinsan ina sonki bazan iya rayuwa babu ke ba, kidawo gareni please mukuma gina sabuwar rayuwa tare da samo baby please_

Sak'on ma haushi yaba Bahija ta wuce gurin , kirane ta shigo wayar , number Emmanuel tagani , cikin tsoro tace ”kodai na fasa wanan wayar , karfa azo ina zaune mutumin nan ya gama shanye min jini , da haka wayar da gama ring ta gaji yayi kira yayi goma amma tak'i d'agawa ."
Momy ce zaune itada Fauziya , suna hira , gani tayi Fauziya ta mik'e tana layi , a tsorace momy ta taso ta rik'e ta , bedroom d'inta ta kaita amma kan kace me ,rai yayi halinsa ,momy ce ta rungume gawar Fauziya tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , batasan lokacin datace , mutuwa babu ciwo ba , takuma fashewa da kuka , ta mance da Allah babu ruwansa , number dady ta gwada tace ”masa yazo maza maza , Fauziya batada lafiya , cikin kid'ima dady ya shigo mota ya dawo gida , bai sami momy a parlor ba , kai tsaye d'akinta ya wuce ,acan ya sameta rungume da gawar Fauziya tana kuka , dady ko tsayawa yai kallonta cikin tuhuma , yace ”saboda batada lafiyan ne kika sata gaba kina kuka ."

Momy ta kasa magana ta d'ago Hanun Fauziya , haka ya koma yarab alamun babu rai , innalilahi anan ya tsaya yana kuma mai maita hakan , durk'usawa dady yayi a gurin yana kuka , momy ce ta tsayar da nata kukan tana bashi hak'uri , lokacin k'arfe biyu na rana , dady ya sanarwa Alhaji da abokansa na arziki , momy kuwa tanata kiran y'an uwanta da su Hajiya da mom da Harun , kowa ya jinjina mutuwar nan musamman Bash da momy takira shi yanzu take gaya masa har kuka sai da yayi."

Kan kace me gida har yacika da mutane sosai , masu zuwa gaisuwa dakuma masu shirin kaita makwancin ta , wata dattijuwa ce tayi mata wanka tare da yimata sutura aka sata a makara , maza suka nufi mak'abarta , momy kukan ma ya dena zuwa , su hajiya sunzo itada momy sunyiwa momy gaisuwar rasuwa , kirane ya shigo wayar momy , Bash ne yace ”momy gobe ina hanya , fatan alkairi tayi masa daganan suka kashe wayar ."

Washe gari kwanan Fauziya d'aya da rasuwa mutane kuwa shigowa sukeyi sosai kasancewar momy tanada mutane , wasu mata dady ya d'auko suka girka abincin sadaka haka gidan ya koma babu wata wal wala a cikinsa kullum cikin kar6ar gaisuwa suke.

*INDIA*🌹

Bash ya gama had'a kayansa guri d'aya , gashi bashida kud'i , Beauty ta sace kud'in duka , tagumi ya zuba ga jaka a gabansa , wayar dady ce ta shigo , cikin rawar jiki ya d'auka yayiwa dady gaisuwa , dady ne yace ”kanada kud'ine a gurinka ?"da sauri Bash yace ”ko sisi dady banidashi , dady ne ya turo masa kud'i mai yawa , sukayi sallama ."

Tunanin Bash ina beauty ta je gashi gobe zai tafi , d'aga kafad'a sama yayi yace ”dama ba dake na zo ba dan haka bazan koma dake ba , yacigaba da loda takalmansa a jikin jaka...

Washe gari jirgin wuri zai biyu yagama komai tun jiya , ya kulle gidan ya nufi airport , cikin ikon Allah jirgin su ya tashi zuwa Nigeria."

Sumaiya ce zaune gaban Abbi yana yimata nasiha akan rayuwa , sunkuyar da kai katsa tayi tace ”Abbi yanzu dai banida kowa amma in kana dashi ka za6omin , cikin farinciki Abbi ya sanya mata albarka , Ammi ma taji dad'in hakan , dan sun riga da sunyi mata miji , suna tsoron sanar da ita , yau gashi Allah ya amsa adu'arta , Abbi ne yace ”to y'ar albarka tashi kije ki kwanta , da komawarta d'akinta ta fashe da kuka tana tunanin anya shawarar data yanke, ta yiwu kuwa ta fashe da kuka babu inda zatayi dole ta kar6i za6in iyayenta da hanu bibiyu ."

*AIRPORT*

Zane Bash yake a cikin jirgi , ranshi fess wanan munafukar bata biyo sa ba , wani farinciki yakeshi , in ya tuno da rashin k'anwarsa da yayi sai yaji babu dad'i , yana cikin tunani ne ,yaji mutum ya fad'o cinyarsa , a zabure ya mik'e yana ihu , hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kansa , kowa sai kallonsu yakeyi , Beauty ce ta fito a zabgegiyar budurwa ,amma kamaninta basu 6ace ba , Bash besai ya zaiyi da rayuwarsa ba ,yasa hannu a ka kamar zaiyi kuka , beauty ko na cinyarsa gata k'atuwa ."

Cikin masifa ya yaye zanin daya luly6e zaninta , kofato ya hango wani ihun yakuma sawa yana cewa ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba , kiyi hak'uri ni dama nasani ina tare da Aljana ne ,babu Wandaya kuma bi takansa shi kad'ai yake shirmensa , hawaye sha6e _ sha6e a idansa yaci kuka gashi koyaya idanshi yakai kan k'afar Beauty a tsorace yake , tunanin ya fara to tayaya ta shigo jirgi batare da tagama komai ba ......✍️.

Vote me on wattpad
Please share

♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 35 & 36
Chapter 13 · 0% Book details