← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da isarshi gidan ,ya sami momy ita kad'ai ce , sallama yayi ya durk'usa ya gaida momy , amsawa tayi cike da kulawa tace ”Harun ka gujemu ko ?" dariya Harun yayi yace ”momy ba haka bane , kitchen momy ta shiga ta d'ibo masa abinci da dambun nama , ta kai masa dining , tace ”masa yaje yaci ,Harun beyi musu ba ya wuce yaci ahinci ya cika cikinsa , saukowa daga dining d'in yadawo sunata hira da momy , duk rabi hirar tasu akan karatunsa ne."

*INDIA*🤟.

Da fitowar Emmanuel , daga d'akin tsafi ya nufi toilet , wanka yayi yasanya kaya da turare mai k'amshi , fitowa yayi ya nufi , d'akin Bahijja , bai lura da batanan ba ya kwanta tare da laluba hannunta , jin bai ji mutum ba ,yasashi mik'ewa zaune ,Bahijja ,yafara k'wala mata kira , babu ita babu alamrta , ko ina na gidan ya lek'a amma shiru , tunani yafara to ina yarinyar nan taje oho ,tashin hankali sosai Emmanuel yashiga zama yayi yafara kuka ,k'ara ficewa waje yayi ya zagaye ko ina na gurin bai ganta ba , nunfar fashi yake saukewa kamar mai shirin shid'ewa , ga uban k'aton ciki a gaba ,komawa gidansa yayi yana layi , rana zafi inuwa k'una wayoo , haka yayi kwanan zaune yayi ."

Bahija ta rasa inda zata dosa ga ciwon jiki ga wani zafi da cikinta ke yimata , tarasa da wanne zataji , zama tayi tana kuka gashi gobe takeson komawa Nigeria , wayo Allah na , haka gari ya waye tana zaune tana kuka ko runtsawa batayi ba gari nayi haske ta ,hau motar haya ta nufi airport domin shirin tafiyarta , ta kammala komai dan jirgin safe zatabi , tasami ragowar kud'i masu yawa , hotel ta kama na masu k'aramin kud'i , tasi abinci , washe gari wanka tayi ko kaya bata canza ba ta nufi airport , k'arfe goma na safe jirginsu ya tashi zuwa Nigeria garin Kano."

Yau Bash yakeda niyar fita wani wasa da za'ayi akan wata fitacciyar yarinya baturiya duk wanda yaci gasar to shi zai aureta , tun ana gasar saura sati Bash yaketa shiri yanata zumud'i, dan haryayi mafarki yaci gasar , wanka yayi yayi brush ya fito ya sami beauty zaune tana kallo a TV tsaki yaja yace ”kewai bakida iyaye ne ?"guntse dariya tayi inda akwai abinda yake bawa Bash dariya bai wuce dariya ba , mari ya wanka mata ,takuma tuntsurewa da dariya , d'akinsa ya wuce ya shirya koni danaga Bash sai da abin rubutu na yakusa fad'uwa , yayi kyau sosai kuma babu budurwar da zata ganshi ta kawar da kai , yana fitowa da kum na taje kai ya wurgawa beauty yace ”kaimin d'aki , dariya sata ta shige da kum d'in , ,k'arar wayarshi ce ta dakatar dashi daga bud'e k'ofar dazeyi , d'auka yayi yace ”abokina ganinan zuwa fa anfara ne ?"to ganinan , bude k'ofar yayi, yaji a rufe what ke dan ubanki zoki bud'e min k'ofa ,sama yaji anayi dashi kamar yaro kuma baiga kowa ba ,gashi yana lilo ....✍️.

Sharhi and comments👌

Please share👏
Vote me on wattpad
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 31 & 32

_____Bash ne keta ihu yana salati tabb niko nace yau wace rana , fitowa beauty tayi ,wanan karon a y'ar yarinya tafito , aikuwa Bash yakuma tsorata sosai , gashi yanzu baya iya kallon fuskarta ,wasu abubuwa yake gani wanda bazaiso k'ara kallo ba , ruwa beauty ta d'ibo a jug tadinga watsa masa , gashi bakinsa bai mutu ba , sai aika mata da zagi yakeyi , itako tana dariya , bedroom d'inshi tashiga ta bud'e bed site d'insa kud'i tagani masu yawa , fitowa tayi tana nuna masa , Bash daya zaro ido cikin masifa yace ”wlh kika fitarmin da kud'i sai naci ubanki , dariya beauty tasa ta fice da kud'in , kasancewar , garin duk ,yare ne ba kowa kejin hausa ba , yasa beauty cewa , kowa yazo tana nuni da hannu sbda ba iya turancin tayi ba , watsa musu kud'in tadingayi , mutane basu fahimceta ba , amma tana watso kud'i suka dinga d'iba , komawa gidan tayi tasamu Bash ya jigata , hannu ta d'aga sai gashi ya fad'o ."

Babu labarin zuwa gurin gasa dan haka duk wanda ya kirashi a waya baya d'agawa , washe gari da safe , Bash ya shirya muguntar da zeyiwa mutuniyar tashi , shiga d'akin da take kwanciya yayi ya hangota tana bacci fuskarta d'auke da murmishi , dariyar mugunta yayi yace ”shegiya maiyya zakisani yau , yana shirin d'aga rigarta kawai yaga batada ,k'afafu , ja da baya yayi yace ”nashiga uku wanan yarinyar dama haka take ?"kokuma yaune ta koma haka ?to babu mai bada amsa ,yasashi yin shiru ya ruga da gudu ."

Maganar Basma da Harun tayi k'arfi dan yanzu ya saki jiki da ita sosai yana zuwa hira , amma ba'a kai kud'in aure ba ."

Asma'u na shagalinta ita da kanta take tiwa kanta gyara maganin mata kuwa ta kashe kud'i sosai dakuma gyaran jiki , Umma dai ta zuba mata ido ne kawai dan rawar kan yayi yawa ."

Mota ta tara zuwa gidan su , gidane babba kai da ganin gidan kasan wanda ya mallaki gidan mai nera ne , wato mahaifin Bahija Alhaji Saminu , hamshak'in mai kud'i ne ,sai dai wata matsala itace bashida lokacin iyalin sa koda wane lokaci yana k'asar waje gurin harkar kasuwancin sa amma kud'i kam ba'a magana , kuma kaff cikin matansa babu wacce bata mallaki kadarori ba ,kasancewar yana turo musu da mak'udan kud'i tun wata na 23 , matansa biyu , Hajiya Aisha dakuma Hajiya Salma basa fad'a ko kad'an kuma ko kaga y'ay'ansu bazaka ban bance ba , kasancewar suna zaune cikin rik'on amana."

Hajiya Aisha itace babba kuma itace ”mai yara biyu Bahija da momy , duk cikinsu aure sukeso amma babu wanda ya isa ya tari mahaifinsa da zancen , a cewarsa wai sunyi yara , itakuma Hajiya Salma yarinyarta d'aya Saudat itace k'aramar cikinsu tanada shekara goma sha takwas , kowane yaro na gidan shek'e ayarsa yakeyi ,iyayen mata suna iya bakin k'ok'arinsu amma ina tsiyar d'an yau tafi gaban wasa."

Bubuga get d'in Bahija tayi , cikin sauri mai gadi ya bud'e mata tana yimata sannu da zuwa cikin mamaki , ko kulashi batayi ba ta shige ciki direct d'akin Hajiya Salma tayi , bata wuce d'akin mamanta ba , Hajiya Salma da suke kira da Anty tana kwance a d'akinta taji sallama kuma murya irinta Bahija , a zabure ta mik'e tace ”Bahija , Bahija ce ta k'araso da sauri tana kuka ta fad'a kan Anty ,itama anty kuka takeyi , babu mai rarrashin kowa sai da sukayi mai isarsu sanan Anty tafara zazzago mata fad'a kamar zata daketa ,jibeki Bahija kinyi bak'i kin rame kamar mai ciwon k'anjamau , daga ina kike ?"Bahija babu abinda ta 6oyewa Anty , wani sabon kukan anty ta kumayi tace ”to ai yanzu da kika gudo wlh baki tsiraba tashi muje , suka nufi d'akin mahaifiyar Bahijan da suke kira da mama , Bahija ce ta durk'usa tana kuka , kallon mamaki mama keyiwa Bahija sekuma ta fashe da kuka tace ”kome kukayi bazanga lefinku ba wlh lefin mahaifinku ne ,kaf cikin gidannan babu yarinyar da bata kawo wanda takeso ba amma fur yace ”sai karatu wallhi mu ya cuta."

Anty ce ta rufe mata baki suka fashe da kuka , dan duka y'a y'an idanunsu a bud'e yake. "

*INDIA🤙*

Kwanansa biyu rabansa da ganin Bahija amma ji yakeyi kamar yayi wata biyu ne , gashi yau yanada shiga gurin dodo , komai yayi masa zafi , haka ya mik'e daga kwanciyar da yayi ,ya koma bedroom d'insa yasa jajayen , kayansa ya shiga d'akin tsafi , dama shi ake jira , da shigarsa fuska babu wal wala yace ”yaza'ayi ku kashemin yaro babu sanina ?"dodo ne yayi wata mahaukaciyar dariya yace ”kana nufin kaci banza ne ?"dukiyarmu da kakeci fa ?"Emanuel zai kuma magana yaji wata firgitacciyar tsawa , akace ”yanzu ma jinin uwar yaron mukeso zamu hak'ura daga ita mungama da faninka , cikin razana ,Emmanuel ya d'ago da jajayen idansa yace ”kuyi hakuri ni ku sha jinina amma karku ta6a Bahija , yana kuka yana rok'onsu."

Babu wanda ya sake magana sai ganin kowa na watsewa yayi , fitowa yai daga d'akin tana kuka sosai , shidai damuwarsa Bahija karsu ta6a ta , yana mai maitawa ahaka bacci 6arawo ya k kwashesa,da tashinsa ya tuna basa bacci da wanan kaya cikin tsoro yahau cire kayan amma me abinda yagani ne yayi matuk'ar firgitashi yanada , bin doka amma dan rana d'aya ya mance sai ayi masa haka, su sam basa uzuri ,ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu ."

*NIGERIA*

Alhaji ne ke shirin komawa saudiya yau amma zai dawo bikin Harun , su mom da Hajiya sunyi masa soye soye dakuma abubuwan da ba'a rasa ba , cikin farinciki suka rakashi airport , tare da yimasa kyakyawar adu'a , sai da sukaga tafiyarsa sanan driver ya maidasu gida."
Chapter 12 · 0% Book details