← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 25 & 26

_____Asma'u ce ta kar6i kud'in tare da shek'ewa da dariya tace ” Bash d'an duniya , bai kalleta ba yace ”Asma'u abokiyar aiki , sukasa dariya , tsayar da dariyar Bash yayi kana ya cewa Asma'u yanzu zakizamo matar Harun kenan ko hhh ai babu matsala ,tanayi tana fifita da kud'in hanunta , ficewa tayi a motar shima ya wuce , tunda ta shiga gida Umma taga yanayin fuskarta cikin farinciki Umma tace ”meyafaru , Asma'u ce tace ”wai Abban Harun zai zo juwa jibi akan maganar , auranmu , tsaki Umma taja tace ”kun gama iskancewar ku keda Harun d'in to uban mezakuyi a gidan auran ?"6ata rai tayi tana sosa kai , mik'owa Umma dubu d'ari tayi ragowar harta je ta turasu cikin kaya , kar6a Umma tayi fuskarta babu wal wala ta fice , tsalle Asma'u ta doka tana wak'a ,juyowa tayi taga jin jirinta na kuka , hawaye ne ya zubo mata tace ”yanzu da wanan yaron zani gidan Harun d'in ?gashi ba nashi bane , share hawayen tayi tafara bashi nono."

Bash ne zaune a gefen dadynsa , dady ne yace ”my son kamar kanada abin cewa , sunkuyar da kansa yayi kamar mutumin kirki yace ”dady dama yarinyar da Harun yayiwa ciki ne ,iyayenta sukeson sa ranar auransu , dady ne ya gyara zama yace ”to su basusanni bane da saikai zasu fad'awa , a'a ba haka bane dady malm d'inne yace ”wai in gaya maka cewar Bash , to babu komai naji ance kakansa yadawo ma, yanzu zani gidan in bashi labarin abinda jikinshi ya aikata , Bash bai ce komai ba yasandai yanzu asirinsa bazai tonu ba , ficewa yayi daga d'akin dady ya koma d'akinshi ya kwanta cikinshi fal farinciki ranshi fess ."

Dady ne yai wanka a toilet d'in d'akinsa ya shafa mai ya sanya kaya ya nufi bedroom d'in momy , samunta yayi tana tsefe kanta , zama yayi kusada ita , ya kamo hanunta tare da cewa , zan fita yanzu zan dawo , momy ce ta kwanta a cinyar dady ta marai raice fauska kamar yarinya , tace ”uhm ina zaka , dady na bala'in san shago6a dan haka yake k'ara son momy , amma in bala'inshi ya tashi baya da mutunci har ita ma bai k'yaleba."

A dai _ dai saitin makaranta ta ajiyeshi , k'in fitowa Harun yayi yace ”wallahi sai kin kaini har gidan iyaye na , dama abinda Basma take sonji kenan ta juya mota ya fad'a mata anguwar suka d'auki hanya , da isarsu tayi Horn mai gadi ya bud'e suka Shiga, Harun ya rigata fitowa itama ta bud'e ta fito , mai gadi ne da drivern su suketa gaida Harun ,amsawa yayi da fara'arsa , yana gaba Basma na baya , da shigarsu parlor sukaji muryar Alhaji na cewa tunda ya zamo d'an iska ai shikenan tunda ta haihu ai babu abinda ya rage gara ya aureta kawai zai gane kuransa , Harun ne yaja ya tsaya dan ya fuskanci dady yazo gidan , tunowa yayi da sharin dasu ,Bash sukayi masa akan yayiwa wata ciki , hawaye masu zafi suka kwaranyo masa daga idanunsa , durk'usawa yayi ya d'aga hanunsa sama cikin murya mai alamun kuka , Basma na gefensa tana tsaye bata gane menene yake faruwa ba , sai dai a yanayin da taga Harun tasan ko maganar tanada alak'a dashi ne oho ."

Harun ne ya d'aga murya sama yana kuka yace ”Allah ka jarabceni da jarabawa iri iri Allah yanzu kuma ka jabceni da wata nadawo daga wata , Allah kaduba maraya Allah ya ceto rayuwata Allah kayi gagfawar baiyana gaskiya Allah narok'eka Allah kasa wanan shine k'arshe wahala ta , ya shafa adu'ar yana kuka mai cin rai , Basma itama kukan takeyi tanata share hawaye , mom da tun d'azu taga shigowar Harun tasa hanunta ta d'agoshi tana kuka tace ”nasan bakai kayi ba ,ba'a shedar d'an yau amma ni wlhi zan shedeka ,nasani ba tun yauba dadynku ba sonka yakeyiba burinshi yaga rayuwarka ta salwanta tunda yasamu ya salwantar da rayuwar mahaifinka , to wlhi wanan karon bazan lamunta ba sam."

Dady da yajiyo surutun mom ya fito yace ”wato kina nufin ni zanyiwa Haruna k'arya kenan ko ? har da yaushe kika haifi d'an da nanunawa tsana kiji tsoron Allah , momy tana kuka tace ”walhi tsakanina daku kaida yaronka da matarka Allah ya.....wani kid'ima mmen mari aka wanketa dashi , jiri na d'ibarta tana shirin fad'uwa Basma ta d'agota tare da shiga da ita ciki , batasan d'akin da zatasa mom ba yasa ta kaita wani parlor da babu komai cikinsa sai lallausan kafet ."

Wasu surutai mom tashiga yi hankalin Basma ya tashi sosai , kasancewar , tasan adu'oi da yawa kuma saukar alqur'anin ta biyu ,tafara yiwa mom adu'oi tana tofa mata tana yimata kabbara a kunnenta , atishwa mom tayi tare da rik'o Hanun Basma tana kuka , jijigata Basma tayi itama hawaye na zuba a fuskarta , Harun ne ya shigo fuskarsa jik'e sharab da hawaye ya durk'usa a gaban mom yana k'ara yimata wasu adu'ion ."

Alhaji da dady suka dawo parlor suka zauna , zuciyar Alhaji sam babu dad'i yana huci yana bawa dady hak'uri, cikin salon yaudara dady yace ”ka haifi d'an ne baka haifi halinsa ba , ,daganan sukayi sallama akan duk inda gidan su Asma'u sukayi dady ya gayawa Alhaji maganar auran kasancewar Hajiya batanan , Alhaji ya zartar da komai ."

Mom ce ta mik'e dan lokacin taji k'arfin jikinta dake inhar ranta ya 6aci to sai aljanunta sun motsa ,godiya Harun yayiwa Asma'u da irin temakon mom d'inshi da tayi. mom ma godiya tayi mata , ta mik' tace ”zata tafi , mik'ewa mom tayi suka fito waje dukkansu mom na cewa Harun ina yashiga ? yau kwana shida ranbonshi da gida , Harun ne ya nuna Basma , kuka Basma tasa tace ”mom ki gafarceni wlh banayi haka bane dan in cutar dashi , mom sanshi nakeyi tun tana zuwa makaranta amma yak'i saurarata cewa yakeyi shi baya soyayya , nikuma wlh shi nakeso , iyayena basu d'auki abin da muhimmanci ba shi 'isa nayi hakan ."

Murmishi mom tayi tace ”banda abinka Harun ai wanan yarinyar ta can canci ka aureta , rakata gida ka dawo inyaso mayi magana kaji , to kawai Harun yace ”ya shiga gurin driver ita kuma ta shige gaba , yacewa drivern gidansu ya biyoshi da motar Basma suka shiga tashi , Allah ya tsare mom tayi musu ta koma d'akinta dan bata sami Alhaji a parlor ba."

*INDIA*🌹

Nak'uda Bahija takeyi tun jiya amma har yau shiru , Emmanuel ne ya sanyata a mota da kayan baby suka nufi hospital , da isarsu labor room aka wuce da ita , likitoci ne suketa bata temako amma ina sunfara tunanin abin yaf'i k'arfinsu , Emmanuel kuwa har kuka saida yayi , kifa kanshi yayi yana kiran Jesus , can saiga wata nurse ta fito tace ”masa matarka ta aihu amma munsami baby ta gugutsure a cikinta dole wankin ciki za'ayi mata , Emanuel ne yace ”ya mutune ?!!eh nurse d'in tace ”wani uban ihu ya zuba yana bubuga k'afa yana surutu....✍️.

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 27 & 28

_____Hajiya ce tadawo daga tafiya , dama garinsu taje , suna za,zzaune a parlor tana kunce tsaraba ta dubi mom , data zuba uban tagumi , Hajiya ce tace ”wai ke bazaki cirewa kanki damuwa ba , banaji kince Harun yadawo ba to yanzu menene na damuwa ?"Alhaji dake gefe ko kallon mom beyi ba ya kawar da kanshi , sabda shima yafara k'aryata zancen dady to kuma yanzu ai bakin alk'alami ya bushe ,tunda ya yarda amma baze sake shed'an yayi tasiri a zuciyarshi ba ,na yarda da cewar ba Harun ne yayiwa wanan yarinyar ciki ba , dole ba'a shedar d'an yau ."

Mik'ewa mom tayi ta shige bedroom d'inta ta fad'a gado tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu , Hajiya ce ta shigo ta d'ago mom tace ”wai meke faruwa ne?" mom ce tace ”Hajiya dadyn Bashir ne ya lak'abawa son sharri , sharrin me ?"Hajiya ta tambaya "cewa yayi wai son yayiwa wata yarinya ciki , Hajiya ce ta firgita cikin tsoro tace ”yanzu me Alhaji yace ”dan beyimin maganar ba , share hawayenta mom tayi tace ”Alhaji ya yarda wlh , eh cewar Hajiya ta mik'e tayi parlor tana gyara d'aurin zaninta , cikin masifa tace ”ina Zakarin wlh bakayi wa jikinka adlci ba , Alhaji daya fito da redio a hannu yace ”to yaukuma babu girma mawa ?" harara Hajiya ta galla masa tace ”wlh Zakari garama ka k'aryata wanan sharrin da kayiwa jikanka shine kad'ai Allah yabaka , amma har za'ayi masa sharri kabasu goyon baya , mamakin masifar Hajiya Alhaji yayi dan ita ba mesan tashin hankali bace ."

Bash na isa gurin bishiyar lemon yaci karo da budurwar da yake kira da beauty , k'walo masa lemu tayi a kansa , tana daga sama tana dariya , Bash ne yace ”beauty wanan wacce irin mugunta ce kuka tasa tace ”Allah bansani ba , saukowa tayi daga bishiyar , ganin yarinyar yayi ta koma masa kamar y'ar shekara goma sha uku , zaro ido yakumayi yana dad'a k'are mata kallo wai shin itace kuwa ?"to dai itance tunda babu wanda yake shigo masa gida ,ko dama kallon tsoro yayi mata ?"bashida mai bashi amsa yasashi rik'o mata hannu sukayi parlor."
Chapter 10 · 0% Book details