← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____ Da haka dai jirginsu ya sauka a Nigeria , driver ne yazo d'aukarsa , juyawa yayi yaga baiga Beauty ba , babu wani farinciki da zaiyi tunda yasan yana shiga motar zai ganta a ciki , driver ne ya d'auki jakar kayansa yasa a Booth , ya rufe , yana tada mota sukaji alamun kamar mutum ya fad'o Beauty ce keta dariya , Bash yarasa inda zeyi kawai yafara kuka , ga wani tsoro daya ziyarci zuciyarsa , driver ganin wanan yarinyar yasashi taka burki ya fice da gudu , Bash ne yace ”Idi kazo ka tuk'amu mu wuce ,ina Idi ya bazama ko tsayawa baiyi ba ."

Bash ne yaji mota na tafiya , zaro ido yayi yana salati , kafin ya tsalako , gurin zaman driver Beauty ta zauna ,tafara driving , Bash dai yariga ya suma babu nunfashi , driving takeyi tana dariya har ta iso gidansu Bash , tana horn taji shiru , ba'a bud'e get d'inba , sauka tayi tafara bubugawa kamar ba hanun mutum ba , kowa na cikin gidan ya tsorata , haka mai gadi ya fito ya bud'e get d'in , suna had'a ido da Beauty ta sakar masa murmishi , a zabure ya juya kansa dan , gani yakeyi idanunta suna yimasa kamar na mage , parking tayi a parking spice na gidan ta fito , gyara zaman d'an karamin hijab d'inta ta nufo cikin gidan."

Kowa sai kallonta yakeyi ita ko babu wanda ta kula ta shige parlorn momyn Bash , da ganinta momy tace ah y'ata barka , da fara'arta Beauty ta zauna momy ce takawo mana ruwa da lemu , abin mamaki babu abinda Beauty tasha , ta dubi momy dake kallonta tace ”Bash na cikin mota , daga haka Beauty ta 6ace , ihu momy tasa tana salati , wanan mutum ce kuwa ?" to in mutum ce ya za'ayi ta 6ace ?"babu mai bata amsa yasata fitowa waje cikin tsoro , bataga Beauty ba , haka taje ta bud'e k'ofar motar , ganin Bash a kujerar baya jiki a sandare yasata k'wala ihu , tana kuka , hankalin su dady ne yayo gurinta mutane suka taso kowa yazo ya lek'a cikin motar , dady ne yace ”shikuma mai yasameshi , momy takasa bada labarin wacce ta shigo mata hartace Bash na mota sai dai kuka kawai , dady ne yace ” wa momy ta Shiga motar su wuce hospital , a tsorace ta shige ko mayafi babu ,dady ya tuk'a motar , da isarsu aka wuce dashi d'akin gaggawa wato emergency , aka fara bashi temako , basu sha wiya ba gurin samun dai _ dai tuwar nunfashin sa."

Yau bikin Harun saura sati uku , shiri kam anayi ta 6angaren su , Basma sosai momy ta ke gyarata kasancewar taga angon nata tsaf tsaf , magugun guna na mata itatuwa ne su kankana apple ayaba da aya da dabino da sauransu momy na bawa Basma , musamman ma dataji za'a had'a Bash da wata bayan y'arta , Basma ta k'ara k'iba tayi kyau fuskarnan sai k'yali takeyi ga wani k'amshi da inka zauna kusa da ita kokuma ta zauna kusa da kai baza kaso tashinta ba ."

Asma'u kam ita ke gyaran jikinta da kanta bata jira Umma ta temaka mata ba , sai rawar kai , gashi bata ta6a ganin angon ba lol , ko number shi batadashi bare sanin ko inane gidan su , itadai tana gyara kanta ."

Mom ce ta dawo daga kasuwa , kaya masu gadi da drivers suke shigowa dashi , akwatuna ne set goma sha biyar , palorn Hajiya sukayi dashi , oyoyo Hajiya ke yiwa mom , cikin fara'a mom ta ce ”Hajiya na gaji wlh , kayan Hajiya tafara fitowa dasu masha Allah , gaskiya koni da nake rubuto muku duk abinda nagani ,hmm zan iya mancewa da wasu , akwatunan atamfofi daban akwatin gyaluluka daban haka ma na skirt shima daban na bra daban na ves daban na turaruka daban , kai barin barku haka ,dan kayanfa sunyi babu makusa , tundaga akwatinma zakasan kayan na manya ne."

Bayan 1 hour da zuwansu ,komai ya zama normal , aka sallamesu suka dawo gida ,Bash kam yariga ya tsorata , shi besan wanan wace masifa bace , tunda ya had'u da Beauty bashida zaman lafiya kodai dama tazo ganin bayansa ne ?"oho yadinga tunaninsa barkatai ."

*INDIA*🌹

Yau alk'awarin Emmanuel da dodo zai cika , gashi wanan ne na k'arshe ,yarasa jinin wa zai bada , gashi ya bada na mamanshi da na babanshi da jinin k'anwarsa dakuma na jaririn da mamansa ta haifa duk ya badasu , ga jaririnsa na gurin Bahija , yanzu kuma bashida wanda zai bada , misalin k'arfe 2 pm na dare kowa ya hallarci d'akin tsafi , shikam yazuba uban tagumi ta kansa dodo yafara , yau mukayi dakai zaka cika mana alk'awari , Emanuel ne yace ”nace muku Ku kasheni ko nace kusha nawa , cikin masifa yake maganar , tsawa aka daka masa ,shiru yayi yana maida nunfashi , dodo ne ya d'ago ,wani k'aton k'ok'on tsafi , fuskar Bahija ce ta baiyyana , daga inda mutanen suke zaune suna hango komai na cikin k'ok'on , cikin masifa Emanuel yace ”inko kukayimin haka bakuyimin adlci ba , zan fita a wanan k'ungiyar kuma koda yin hakan zai janyo mutuwata ."

Hango Bahija a cikin k'ok'on tsafi yayi ,tanata jujuya kanta tana cije baki , kuka Emmanuel yafara tare da cewa tur da wanan k'ungiya kuma sai kunyi nadamar yin hakan , babu wanda ya kulashi ,kuma duk maganarshi bazata sa su tsaida k'udirinsu ba , haka aka tashi taro ran Emmanuel babu dad'i komai ya birkice masa , direct offishin matakan tsaro ya nufa wato sojoji , yana kuka yana bada bayanin abinda ke faruwa , wani farin mutumi bature yace ”masa a inane zamu samesu , Emmanuel ne yayi musu kwatancen inda zasu had'u , sashi a motar sukayi suma suka shiga , abin mamaki da zuwansu sukaga gurin ya koma jeji."

Kallan kallo suka fara , sumadai sunsan akwai gidaje bila adadin a gurin amma gashi babu alamun anyi gini yanzu , Emmanuel ne tsoro ya kamashi yana tunanin hukuncin da zasu yanke masa."

Bikin Sumaiya da yaron k'anwar momyn ta ya matso ,yau saura kwana biyar , kyau kam amarya tasha dan kobatayi kwaliya ba tanayin kyau to inaga ranar bikin , yanzu kam ta hak'ura ta mik'awa Allah komai ta amshi za6in iyayenta , sosai suke zuba soyayya da saurayin nata mai suna Khalid , kamar masoyan da suka shekara."

Wani abin mamaki ashe beauty na d'akin Bash tana bacci tun lokacin da momy ta nemeta ta rasa , suna shirin shiga da Bash d'akinsa , suka hango Beauty na kwance tana bacci cikin nishad'i , tsabar tsoro momy sake Bash tayi a k'asa ta ruga da gudu tabarshi shi da dady , Bash ne yafara cewa "nidai nashiga uku bansan yazanyi ba ko wane lokaci aljanar nan na tare dani."

Ashe zancen zuci ya fito fili ,dady yaji duk abinda yace ”aljana ?"dady ya mai maita ,eh wlh dady , tsoro ne ya fara kama dady yace ”ai ance ljanu basuda k'afafuwa bud'e nata mugani , a tsorace Bash ya kalli dady dady ya kalli bash , dakewa Bash yayi yaje gurin bak'ar jallabiyar Beauty ya bud'e k'afarta , kofaton suka hango cikin tsoro dady zai zura da gudu k'ofa ta rufe , gashi ga Bash kuma ga Beauty aljana lol."

Bash ma neman gurin guduwa ya keyi amma babu hali k'ofa a kulle take , Beauty kuma na bacci , Bash yana tsoron yacewa "dadynsa wanan aikin ma Beauty ne ta farka tabashi horo , yaja bakinsa yayi shiru ...✍️.

Vote me on wattpad
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

*JININ ABBANA FANS GROUP*

*JININ ABBANA PANS (2)*

*WANAN PAGE 'DIN NAKUNE 🤙*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 37 & 38

____ Mutane suka gani cike a d'akin , kuma duk sa'anin Beauty ne , da bak'ak'en kaya , tsalle suketa yi suna dariya , dady da tsoro ya gama kamashi ,ya ce ” kai Bash tashi waccan mai baccin , ido Bash ya zare yace ”dady wlh itace babbar su , dady na kallon Beauty ,yace ”ke tashi , beauty ce ta mik'e tana dariya , wanan dariya ba k'aramin firgita dady tayi ba , yaran da suka zagaye dady da Bash suka fara magana wata iri , suna cewa "baku kun iya mugunta ba ?daga kai harshi bakuda tausayi ,to yau zaku gane kuranku , kowa yazo ya fad'i abinda yayi ,inhar kunaso mu bud'eku ."

Jin shiru har dare yasa momy bubuga k'ofa amma shiru , ko motsin mutane bataji , number Bash da number dady bata shiga , hankalin momy ya tashi sosai ,tarasa ina suka shiga ,gashi d'akin Bash yak'i bud'uwa , tunani tafara kodai wanan aljanar tana d'akin ne ?"toshi Bash a ina ya samota , tattara zancen zucin tayi gefe ta nufi waje , driver ta hango zaune a takure kamar mai rawar sanyi."

Cikin tashin hankali momy ta k'arasa gurinshi tace ”Idi zoka nemo min malamin ruk'iya , cikin tsoro Idi ya kalli momy yace , Hajiya karfa inje garin nemo wa a kwashe ni , tsawa momy ta daka masa , hakan yasashi ficewa da gudu , tunda ya fita yaketa gudu har ya wuce anguwarsu ,amma baisan ya zoba , mutane sai kallonsa sukeyi ."

Pans kuzo muje mu taro Idi fa🤣.
Chapter 14 · 0% Book details