← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau Harun yafara zuwa aiki ba laifi gurin yayi sosai kuma akwai albashi mai tsoka wanda dan danan mutum zai tara arzik'i na ban mamaki , kullum yana busy bashida lokaci , yana gurin aiki kasancewar shi mutum ne mai maida hankali a abinda yasa , a gaba wata k'ya k'yawar yarinya ce ta shigo sanye da hijab mai hannu ba k'aramin kyau tayi ba , k'are mata kallo Harun yayi zatakai shekara sha bak'wai , karo na farko daya tsaya ya k'urawa budurwa ido kenan mamakin kansa yakeyi , can kuma yaji k'irjinsa na bugu , dawowa wanan budurwa tayi , tacewa ”Harun barka ,dady na ya gayamin munsami sabon ma aikaci , washe fararen hak'waran sa yayi yace ”barka sister , dariya tayimasa tana yimasa wani irin kallo mai wuyar fassara , Harun baisan wanan budurwar ta tafi ba saboda ya fad'a kogin tunanin ta lol , kodai kodai🧏‍♀️..

*WASHE GARI*
Da safe yayi wanka sashen su momy ya nufa da sallama ya shige samunsu yayi a dining suna breakfast , momy ce ta washe baki tace ” a 'a my son zoman kaima ka karya , durk'usawa yayi ya gaida dady ciki ciki dady ya 'amsa kana ya juya ga momy , cikin fara'a ya amsa ,jiyayi ance brother barka da safiy, ywwa kintashi lpy sis cikin shagwa6a tace ”lafiya lau , a d'a rare ya zauna a dining chair d'in yayi karin kumallo ,tunda ya zauna fara'ar fuskar dady ta gushe , shigowar Bash ce yasanya Harun juyawa , sanye yake da gajeren wando iya guwai warsa sai singlet fara a , k'arasowa yayi yace ”good morning dad ,good morning mom, amsawa sukayi cike da kulawa suna yimasa ya aiki ,dady ko janyo Bash yayi kusa dashi yazuba masa farfesun kaza , Fauziya ce tace ”ya Bash inason muyi wata magana saboda is very important to me and yau lol , kashe mata ido yayi yace ”oky yanzu dai kibari na gama sai muje muyi ko , suna had'a ido da momy ta galla mata harara , Harun ne ya dubi gefen da Bash yake zaune yace ”brother babu magana ne , cikin zafin rai Bash yace ”bana magana da y'an iska irinku , yana magana yana nuna Harun , hankalin su momy ne yakoma gurinsu , yacigaba da cewa wlh dady ciki yayiwa wata yarinya yanzu gashinan iyayenta suna nemanshi ido rufe yama samu na rufa masa asiri , a razane ido yai ja Harun ya d'ago yana kallon Bash yace k'iyayyar mu harta kai ga kayimin sharin zina ?"nine fa d'an uwanka , dariyar mugunta Bash yayi yace ”a da kake d'an uwana amma yanzu an sauya bani babu abota da mazinaci !! kalmarnan ba k'aramin dukan Harun tayi ba ,har lokacin idon Momy da dady da Fauziya na kanshi ,wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo daga idonsa ya had'a hannuwansa biyu yace ”na rantse da Allah dady da momy ku yarda dani ko kula y'ammata banayi walhi , wani mari dady ya wanka masa yana cewa d'an iska dama shiyasa kake shigo mana gida ?"to kull kar in sake ganinka a ginanan kaje can 6angaren ka amma nayi maka iyaka da iyali na so get out ko bakaji ba , Harun na kuka yana cewa dan Allah ku amince da magana ta, haka ya fice zuciyarsa babu dad'i ."

Dady ne ya kalli momy yace ”kinga abinda yaronnan ze janyo mana ko ? sunkuyar da kai momy tayi hawaye na zuba a fuskarta ta d'ago ta dubi Bash tace ”Bashir kaji tsoron Allah kuma kasan zaka mutu kaje ka tarar da Allah shin gaskiya ne ko k'arya ? Bash ne yatashi yana mita , ni dama ai ba'a yarda da maganata ya fice , a hanya ya had'u da Harun ya tsuguna ya dafe kansa , dariya Bash yasa yace ”d'an samari kana lokaci , bai sami damar maidawa Bash martani ba ya mik'e jiki na rawa yanufi part d'inshi , gado ya fad'a tare da sakin kuka mai ban tausayi .

Rurin dayaji wayarsa na yine yasashi cirota a cikin aljihu bai mai number ba 'amma tunda yafara zuwa sabon gurin aiki bari dai ya d'aga ,yana d'agawa yaji ance Malam Harun nine ma manjan ma aikatar ku , kasancewar baisan ko waye manaja ba yasashi gaisheshi cikin ladabi , mutumin da yakira sunanshi a matsayin manaja , yace ”inason mu had'u a gidan Zoo sabo wanda kasani ,hak'ika Harun ya firgita amma tunda umarnin manaja ne dole yabi , haka ya share hawayen fuskarshi ya mik'e yashiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shafa mayukansa masu k'amshi ga turaruka ,yasanya ya d'auki k'ananun kayansa ya sa ya d'aura agogo , ya dauki wayarsa da key d'in motarshi ya fice , yana shirin shiga motar yaji wani kiran yasake shigowa , d'agawa Harun yayi cikin rawar jiki yace ”manaja ga ninan zuwa , cikin sauri ya shige motar yatada ta yanufi titi tafiya yakeyi amma gabanshi na fad'uwa ...✍️.

Vote me on wattpad
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 9 & 10

____Bash ne shida Fauziya a bedroom d'insa kwance take yana wasa da gashin kanta ,kanta ta d'aga tayi masa rad'a a kunne , mik'ewa naga sunyi ta zura hijab suka fice , Allah ka karemu da rayuwar dabbobi🤦‍♀️,zama yayi a cikin mota yana jiran fitowar Fauziya ,bedroom d'in momy taje ta sameta a zaune tana goge mirror , gefen gadon tasamu ta zauna ta rik'o hanun momy ta shagwa6e fuskar ,momy ce tace ”to shagwa6u ,meyafaru ?" cikin shagwa6a tace ”momy zanbi ya Bash shopping , momy ce ta dubeta tace ”mezakije siyowa , turaruka cewar Fauziya , to Allah ya tsare ki kula da kanki please ,oky momy natafi , tashige mota suka wuce , suna tafiya suna hirarsu wacce ni kaina banajin abinda suke fad'a ."

Umma na fito da abin gwajin cikin taga ya zana mata layi biyu , waro ido tayi cikin tuhuma tace ”Asma'u tsiyar da zaki janyo mana kenan?"shikenan na shiga uku cewar umma ,Asma'u dake zaune ta sunkuyar da kanta k'asa ,idanunta na kan shinkafar da take tsincewa tace ”Umma dan Allah kiyi hak'uri dan girman Allah , wani wawan mari umma tabata yayi dai dai da shigowar Malam , cikin alamun tambaya ya zauna yana ”cewa meyafaru kike dukan budurwa kamar wanan gaskiya bai kamata ba , hawayen da Umma take k'ok'arin 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Malam daya kasa gane me yafaru ya dakawa Umma tsawa yace ”bana san sha shanci ina tambayar ku meya faru amma duk cikinku babu mai bani amsa ? juyawa malm baya umma tayi tare dacewa ”to cikin shege Asma'u tayo , mik'ewar da Umma zatayi ta yanke jiki ta fad'i , Asma'u dake cikin tashin hankali ta nufi d'akin umma a d'an madai_daicin fridge d'insu wanda yad'an ji jiki ta d'auko ruwa a gora ta yayafawa Umma , ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa wlh kinyi asara a rayuwarki duk tarbiyar da muka baki bin mazan waje yafi yemiki komai ko? Malam da zuciyarshi ta hassalo ya mik'e yashiga d'akinsa da yake ajiyar bulalai ya d'auko mai baki biyu yakuma d'auko mai baki d'aya ya had'asu yashiga , zabgawa Asma'u , saida yayi dukan ya gaji dan kansa yaga idanuwanta ne masu k'iftawa alamar taji jiki , zama yayi ta gefenta ya yarfe gumin goshin sa yace ”Asma'u yanzu irin tarbiyar da na baki kenan ?"sakaiyyar da zakiyimin kenan wlh bakiyi mana adlci ba kin cucemu kin 6atawa gidannan suna , saita bulalar yakumayi yana shirin zabga mata yace ”ubanwa yayi miki ciki ?" rufe bakinta tayi tana shirin yin amai , takasa mik'ewa dole ta kwararo amai a gurin , Malm ne yace ”tambayarki nakeyi kokuma kinason ink'ara miki bulalar ne , shiru tayi tak'i magana , Malam ko kamar jira yakeyi tak'iyin mgna ya zuga mata bulalar yana shirin k'ara kaimata na biyu ne tace ”malm kayi hak'uri zan fad'a maka , to ina saurarar ki cewar Malam ,Asma'u ce tayi jimm can kuma tace ”Harun ne , gyara zama Malam yayi yace waye Harun??? ,d'ane ga Alhaji Muntari yayan Alhaji Yusuf mahaifin Bashir ,Malam ne yace ”kina nufin kintsatsen yaronnan dashi kukayi watsewar ?"sunkuyar da kai k'asa tayi Malam ko saida yakuma yimata lilis sanan yafice domin yin sallah la'asr."

Da isar Harun gidan Zoo d'in ya hango wani bak'in mutumi ya rufe fuskarshi , yana shirin ciro waya yakira wanda yace ”yazo aka shak'e masa wuya aka sanyashi a mota sukabar gurin ."
Chapter 3 · 0% Book details