← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa momy tayi ta zauna a parlor tana jiran dawowar Idi , agogo ta duba har k'arfe shida na yamma shiru , tagumi ta zuba tace ”to shi wanan ina ya tsaya , lol niko ina gefe ina dariya Idi ya falle da gudu , mik'ewa tayi ta d'auko wayarta a bedroom , number wani malami da yake zuwa yimusu sauka farkon tare warsu a gidan , gwada number tayi , cikin rashin sa'a akace mata number bata tafiya , tashin hankali momy ta shigeshi , babu miji babu d'a , ga Idi ma shiru , rasa wazata kira tayi kawai ta zauna tadinga cin kuka gashi babu mai rarrashi ."

Bahija ce zaune itada anty da mama ,suna hira , yanzu kam jikinta yayi kyau ,washe gari da safe ta tashi da matsanancin ciwon kai tun ana ganin abin kamar ,wasa har takai ga tafara surutai da basuda kan gado , mahaifinta suka kira , "cewa yayi su kaita ,hospital , cikin gaggawa suka , kaita hospital , temakon gaggawa doctor suka fara bata , ciwo dai kamar wasa abin ya gir mama."

Bahija batacin abinci sai ruwa shima ruwan dak'yar yake tafiya mahai fiyarta ko tana ganin kamar mutuwa zatayi , ganin wata uwar rama da tayi. "

Yau kwanansu biyu a hospital d'in ,jiki babu sauk'i sai abinda ya dad'u , Allah sarki rayuwa , mutane sai zuwa gaisheta sukeyi , y'an uwa da abokan arzik'i ,duk wanda yasan Bahija to da k'yar zai ganeta , saboda tsananin ramar da tayi ."

Tun su dady da Bash na kuka , har bacci ya d'aukesu , sai sunfara bacci sai suji dariyaku , haka dai gari ya waye da asbha momy ta fice daga gidan tayi wani gida a mak'otansu , tunda take bata ta6a shiga gidan ba yaukan dole ta janyo hakan , shiga tayi da sallama , gidane madai daici sunada rufin asirinsu dai dai gwsrgwardo , da shigarta mata gidan ta shimfid'a mata tabarma ,bayan sun gaisa ne momy take tambayar matar ko tasan gidan wani malami nan kusa , akwai matsala a gidanta, matar ce tace ”barin yiwa malam magana ,momy na zaune matar ta shige d'aki ta fito tana cewa "bari malam ya shigo kiyi masa bayani , to momy tace ”tana jin jina lamarin gidan ta , bayan 5minutes wani mutumi ya fito da malun malun , ya nemi guri a can nesa da momy ,a tabarmar da aka shimfid'a masa , momy ce tafara gaishe shi danan yace ”tafad'i abinda ke faruwa , labarin abinda yafaru tabashi , malm ya jin jina wanan lamari amma baiyi magana ba ,dan haka ya d'auki Alq'uranin sa yace ”muje , momy na gaba malm na baya , gashi garin beyi haske sosai ba, haka malm ya kunna touch light , momy kam tama mance da batun fitila , haka ta bud'e get d'in suka shige , kai tsaye parlorn suka shiga , nuni momy tayi masa da hannu kaga d'akinnan , murmishi malm yayi yace ”to , momy komawa kan kujera tayi ta zauna tana maida nunfashi ."

Da shigar malam d'akin Bash yaga mutum uku a kwance , d'aya mace akan gado biyu kuma a kafet , zama yayi a kujerar da take gefe da gadon ya bud'e Alqu'ani yafara karanta suratul bak'ara , daga dady har Bash babu wanda ya motsa sai macen da tafara motsi da jikinta cikin tuhuma malam yace ”koma waye ya fito yanzu dan zan k'onashi , shiru babu mai magana , malam ne yaciga ba da karatun yana yarfa wani ruwa na adu'ar , Beauty ce ta mik'e da bak'ar riga tana dariya , tana cewa bazamu barsu ba bazamu barsu ba."

Malamin ne ya tsaya da karatun ya dubi Beauty yace ”ke wacece? cikin dariyarta da batada dad'in sauraro tace ”nima kamarku nake , ta tuntsire da dariya , malm dayake yasan ba mutum bace "ya cigaba da adu'arsa ,hak'uri tafara bashi akan yayi hak'uri , malm ko saurararta beyi ba yacigaba , zaki fad'amin gaskiya ko bazaki fad'a ba ?" Beauty ce tace ” kabarni zan yima bayani , malm bai gamsu zata fad'a ba ya watsa mata wani ruwa ,ihu tafara tana ya k'yaleta , tambayarta ya kumayi a karo na biyu ,me bayin Allahn nan sukayi miki kike cutar dasu ?".

Yau ta kama daurin auran Sumaiya , manyan mutane da dama sun halarci bikin , kowa kagani fuskarsa cike take da farinciki , Abbi ma farincinne shimfid'e a fuskar sa , haka Ammi sai albarka suke sanya mata ,gidan ango duk da dai tuwona miyata ne ,sunyi rawar gani sosai akwatuna set goma sha biyu , kuma shak'e da kaya , masha Allah amarya tayi goshi, hango Sumaiya nayi tasha bak'in lalle fuskar nan tasha make-up ga wani tsararen kitso da aka yimata , gaskiya ta had'u abinka da farare abin ba'a cewa komai , wayarta ce tafara ring ,sunan my sweetheart ne ke yawo a screen d'in wayar ,cikin sassanyar murya ta d'aga , kunsan marubuciyar taku da son jin k'wa k'waf hhh , ango ne yace ”my honey dafatan dai baki wahalar min da kanki ba , kukan shagwa6a tayi kamar yana ganinta tace ” sweetheart , bana jin cin komai yanzu ,oh my honey kinason wahalar min da kanki , wata irin dariya tayi da nima na dara hhh my fans dariyar fa ta masoya ce."

Ki fito please muje kici abinci , uhm uhm nikam bazan iya ciba ,okay to bari in aiko Shamsu ya kawo miki ,cewar Khalid salama sukayi kowa ya ajiye waya, k'awayen ta ne keta yimata tsiya wai tafiya shagwa6a Khalid zaiyi , fama ,lol niko nace ai mace babu shagwa6a to ai babu kanta 🙈 kuka tasa tana shure shure , tin tsirewa da dariya suka tafa."...✍️.

👏👏👏👏👏👏👏👏

*GASKIYA MASOYANA*

ina alfahari daku da kuma soyayyar da kuke nunamin wlh ina gani kuyi hakuri yanzu aiyuka ne sukayimin yawa , ina neman Adu'arku please kuyimin adu'a Allah ya rabani da abinda nake tare dashi lpy , kuna rai na, nagode da nuna soyayyar.

Please share👏
Vote me on wattpad

♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 39 & 40

____ Mama da Anty na hango a hospital , suna fitowa daga d'akin da aka kwantar da Bahija , kuka Anty takeyi sosai , juya kai mama tayi tana adu'a a hankali doctors ne suka shigo cikin rashin walwala suka rufe gawar Bahija , kulli nafsin za'ikatul maut Allah ka kar6i tubanmu , Allah yayiwa Bahija rasuwa , da dawowarta daga India , ba k'aramin aikin alkhairi tadinga yiba , itace sadaka dakuma ibada , Allah kaji k'an musulmai Allah ka gafartawa wanda suka rigamu gidan gaskiya ."

Babbar k'awarta ce wacce sukayi primary tare , idanunta a bud'e suke dan haka kowa ke tsoron ta ra6i yaronsa, Umma tayi iya yinta amma abin ya fi k'arfinta , kasancewar yanzu Asma'u tanason fin k'arfin Umma , kusan kullum Umma sai tayi kuka gashi malam ya kwanta ciwo na bak'in cikin Asma'u , Umma takoma abin tausayi ."

K'awar tata mai suna Zubby , duban Asma'u tayi tace ”my sis mai yasa kika bari kika d'auki ciki ,gaskiya bakida wayo sekace bakiyi karatun boko ba , shiru Asma'u tayi tace ”ke nifa ban ma san na sami ciki ba , kawai gani nayi ina amai, Asma'u ce tabawa zubby labarin , abinda ya faru tsakaninta da Bash har lamarin auransu da Harun da za'ayi nanda kwana biyar , Zubby ce ta bugi cinyar , Asma'u tace ”kee!!, kud'in banza , kud'in hofi , ke baki iya bariki bane ?"yanzu fa ragamar komai a hannunki take , dan haka ki janye maganar aure kizo mu fasa bariki , ita kuma , Basma da kikace , Harun zai aura , to inada mafita wlh ,mu watsa musu bala'i kuma mubari sai sunyi auran sanan , zaki godemin k'awata , Asma'u ce ta dubi jaririn hanunta tace ”to wanan yaron ya zanyi dashi , Zubby ce ta karkace ,d'aurin d'an kwali tace ”tambaya ma kikeyi ?"to tsaya tambaya wlh garama ki bud'e idonki , ita wanan tsohuwar aikin me rakeyi ki jefa mata shi kizo muyi tafiyarmu , Asma'u kallon Zubby takeyi , a can k'asan zuciyarta tana tunanin , inhar ta tafi to mahaifinta fa gashi babu lpy baima san waye a kanshi ba ."

Maganar Zubby ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take , maiyasa zaki tsaya watsar da damar da Allah ya baki , just ki share tausayi da wani abu , kizo mu fasa , zan baki kud'in siyan atamfofi da lass da duk wani kaya na yayi , kingafa harkar nan , wlh bazaki dingayi da k'ananan mutane ba , zaki waye kiyi fresh hmm ,sai kin shigo zaki gane manufata beb , hud'ubar Zubby tasami gurin zama a zuciyar Asma'u , sun shirya nanda kwana biyu zata bar gida , Zubby ko tanata k'ara jaddada mata abubuwa na more rayuwa dakuma wanda zata k'ara fasowa gari. "

Sallama sukayi , Zubby tazo fita sukayi kaci6us da Umma , Allah yasa yanzu ta dawo daga anguwa , har k'asa Zubby ta durk'usa ta gaida Umma , cikin sakin fuska Umma ta amsa ,ta fice , Umma ce ta shige d'akin Asma'u , tafara zuba mata masifa , tace ”wlh Allah ki kiyayeni ke bakida hankali ne , wanan shed'aniyar yarinyar kika k'ulla k'awance da ita , to kifita harkar ta kokuwa ranki ya 6aci dan wlh zakisha mamaki tunda bakida hankali , kukan k'arya da munafurci Asma'u tafara , tace ”umma ba k'awata bace fad'a ma mukayi da ita yanzu , Umma ki yarda dani insha Allah nakoma Asma'un da kika sani a da wlh na tuba Umma."
Chapter 15 · 0% Book details