← Book details Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Jinin Abba Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da shigarsu ya d'auko mata Maltina , juya gwan gwanin tayi murya irin ta yara tace ”kana shan giya ne dama?"keee , Bash yace ”cikin tsawa , had'a ido sukayi yaga bazai iya yimata masifa ba , tunani yafara anya mutum ce kuwa ?"kawar da tunanin yayi ya k'aita wani bedroom da komai akwai a cikinsa harda kayan mata , kwanciya tayi tana ware ido , gani nayi ta zamo babbar budurwa tana dariya , dajin k'arar bud'e k'ofa harta koma inda take , Bash ne yashigo dagashi sai gajeren wando jikinsa babu riga , beauty ce ta k'wala ihu , da sauri ya fice , yazo fita ya sulle a k'ofar d'akin , ihu yakeyi amma baiwar Allah bata fito ba tanacan tana dariya , yayi k'ok'arin ya tashi ya kasa cikin sa sanyar murya yace ”beauty zoki temaka min , fitowa tayi tana dariya ,tana cewa am banja gala daka fati , wani uban ihu yasa yace ”wayoo Allah kardai aljana na d'auko , na d'auko ta babba d'azu ta koma k'arama ,yanzu kuma ta koma yarinya y'ar shekara goma , nashiga uku."

Da isar su Harun Basma tace ”sai yaje ya gaida iyayenta , baiyi musu ba suka shiga , momynta tasamu a parlor tana rubuce_ rubuce , durk'usawa tayi tace ”momy please afuwan ,nabiya gidansu Harun ne mom d'inshi batada lpy , momy cikin fara'a tace ”ah barka son zoka zauna ga guri , durk'usawa yayi har k'asa ya gaida momy ta sanya masa albarka , mik'ewa momy tayi ta tattara takaddunta ta shige ciki , abinci mai rai da lafiya dakuma kayan k'walama da lamu Basma ta kawowa Harun , y'ar aikin gidanne ta shigo da tirai a hanunta tare da gaishe da Harun farfesu ne a ciki sai apple da kankana da sauransu ...

Harun ya d'anci babu lefi ya yi godiya , satar kallon sa Basma takeyi ,dasun had'a ido ta sakar masa murmishi mai alamar love🤣 mik'ewa yayi yace ”to nagode nizan tafi , Basma kamar zatayi kuka tace ”sai yaushe zaka dawo ?"murmishi yayi wanda ya baiyana kyawunsa dakuma dimple d'in kumatunsa , yace "sai lokacin da Allah ya nufa , Basma ko kallon pink lips d'insa takeyi inda yake motsasu kamar bashike magana ba , rakiya tayi masa tare da k'ara jadada masa ya gaida mom."

Bash ne kejin dariyaku sunkai na mutum biyar gashi babu damar tashi kwankwaso na ciwo ,kamo jikin bango yayi ya d'ingisa ya mik'e ,yafara tafiya kamar mai aihuwa , aikuwa beautyin tasa ta shek'e da dariya , da shigarsa d'aki ya kwanta juyin da zaiyi yaji ya soke da alura ,yakuma juyawa ta d'ayan 6angaren yakumajin ya k'ara sokewa , jiki duk ciwo ya mik'e yace ”wlh gobe sai India bazan zauna a Nigeria ba , wanan yarinyar kuma ta nemi iyayenta dan temakonta nayi amma takoma min kamar aljana ."

*INDIA🤏😎*

Bahija ce a d'akin hutu anyimata duk wani temako taji sauk'i gobe za'a sallame su , iya kulawa Emmanuel yana bata musamman ma dayaga ta mugun ramewa , washe gari an basu takaddar sallama suka tattara kayan babyn da suka jido yasasu a motarshi sukayi gida , da isa rsu lokacin anyi magrib suna gama cin abincin nasu da baya wuce kayan mar mari , ta kwanta dan jiya cikinta nayi mata ciwo bata sami damar bacci sosai ba yau kuma da rana abokanansa sun zo da yawa kuma ko wanne saiya bata kud'i mai tsoka , duk ta adanasu a kayanta , bacci ne ya sureta , shiko Emmanuel yana zaune da wata takadda a hanunsa , misalin k'arfe biyu na dare baccin Bahija yayi nisa , Emmanuel yashiga d'akinsa na tsafi , mutanene zaune a ciki da yawa , kasancewar tsafin nasu duk wani mai yi to yanada d'akin sirri a gidansa kuma duk dare yashiga zai samu ana meeting , yauma kamar kullum ya shige amma saida ya duba Bahija ."

Bahija ba bacci takeyi ba saboda dama burinta tafito daga hospital ta gudu dan tasan dodo ne ya cinye mata jariri kasancewar ta ma bamai tsoro ba , jakar hannu kawai mai kud'ad'en ta ta d'auka sai hijab zumbulele da tasa tabud'e k'ofar a hankali ta fice da gudu , nidai bansan ina ta nufa ba cikin wanan dare, gudu takeyi Allah ma yasa ko ina da haske kamar rana mutane sai kallonta sukeyi , sai da tayi nisa da gidan sosai ta zauna tanata haki , tana hutawa ta d'ora da inda ta tsaya ."

Sumaiyya wato inbaku manta ba budurwar Harun ,wacce Abbin ta yakawo mata saurayi tayi masa wulak'anci .

Zaune suke a dining suna dinner rabonta da zaman hira da iyayenta harta manta , kullum cikin silent take daga d'aki sai wanka ko cin abinci , Ammi tun tana damuwa harta dena kulla ramuranta , gashi yau har wata d'aya komai bai sauya ba, Abbi ne yadu beta da farin gilashi a idansa yace ”daughter wato mu bamu isa dakeba kenan ko , damuwarki kinfi k'arfin sanar damu ...✍️.

Please share
Vote me on wattpad

♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.

_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_

*Story and writing*
*By*

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

Zainabhabibu713 @gmail.com

Wattpad momislam2020

Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk

Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 29 & 30

_____Washe gari ya shirya kayansa , ya nufi parlorn momy , samunsu yayi itada dady suna kallo , gaishesu yayi yace ” yau zan wuce , dady cikin tuhuma yace ”ina zakaje ?"Bash ne ya mik'e tare da duba agogon hanunsa yace ”india zan tafi ancemin za'ayi wata gasa , momy ce tace ”kabari a koma hutu , yana shirin kuka yace ”ni wlh an takuramin , banida ikon yin komai , dady ne ya mik'e ya zo gurinshi yana bashi hak'uri yace ”to ya maganar plane d'in ?" Bash ne yace ”dady komai ya kammalu ,ya yiwa momy sallama zuciyarta babu dad'i , bataso tafiyar Bash ba amma dole tayi masa adu'a kuma tadena fushi dashi tunda hanyar mota zai bi , dady ne ya ce " masa ya shiga mota ya rakashi ."

Tunda gari ya waye ya fito da beauty da jakar tafiyarsa , ya turota waje , dariya beauty da kamayi tana nuna Bash , zagunta yashiga yi yana cewa ko dai aljana kokuma wata halittar da ban dan banyarda dake ba , dahaka yabarta a gurin ."

Tunda ya shiga jirgi gabansa ke fad'uwa , tuno beauty yayi cikin zuciyarsa yace ”ko tana ina oho , jiyayi mutum ya d'anne kan cinyar sa , zaro ido yayi yace ”dan ubanki waya kawoki cikin jirgi , lokacin jirginsu ya tashi , Bash kukane kawai be zo masa ba gashi ,be isa ya hanata abu ba , to wai shin mutum ce ko aljan?"babu amsa kuma babu mai bada amsa ."

Dady ne yakira Alhaji a waya , akan maganar zuwa gidansu , Asma'u ,cikin sanyin jiki alhaji yace ”gashinan zuwa , Alhaji ne yafito ba tare da ya gayawa su Hajiya ga inda zai je ba , had'uwa sukayi a bakin titi a motar dady ,suka nufi anguwarsu Asma'u ,da zuwansu suka aika yaro yayi sallama da malam ,cikin sa'a suka sameshi yace ”su shigo , tabarma malam ya shimfid'a musu a d'akinsa kasancewar Umma da Asma'u basanan malam ne yace ”musu ina zuwa , fita yayi waje ya aiki wani yaro ya siyo musu ruwa da lemu ,ya dawo ciki suka gaisa , bayan sun gaisa ne ,Alhaji yace ”munzo akan maganar auran Asma'u ne da d'an wajen mu , malm ne yace ”ai basanan ma ni da naso abari yaron yayi wayo sosai , zuwa nand a wata uku ko hud'u se ayi bikin , yaro ne ya shigo rik'e da kayanda malam ya aikeshi , ajiyewa yayi a gabansu Alhaji , ruwa suka d'auka sukayiwa malm godiya suka fice ".

Da saukar Bash ya rik'o hanun Beauty yace ”k'ila ubanki ya ta6a zuwa k'asar waje ko ?" beauty na kallon shi batayi magana ba , janyo hanunta yayi ta k'arfi ya sa6a jakar bayansa suka shiga mota , a anguwar da yake da zama suka sauka , gidan yashige da beauty , suna shiga yaga beauty tazama k'atuwar budurwa , mamaki da tsoro ne suka dira a zuciyar Bash ya finciko gashinta had'e da hijab d'in jikinta yafara kifa mata mari , saida yayi mata mai isarshi sanan ya turata , duk wanan marin da gabjenen hanunsa ,batayi kuka ba sai dariya da takeyi da muryoyi da dama."

Mom ce tabawa Hajiya labarin Basma , dukda bata ganta ba tasan duk abinda mom ta yaba to lallai mai kyau ne , Alhaji na shigowa Hajiya ta labarta masa , yayi na'am amma da sharad'in Harun zai auri Asma'u , babu inda suka iya kuma babu mai war ware komai sai Allah , haka Alhaji ya sanarwa da dady a waya kasancewar , shima yanada hak'i a kansa , dady dayaji wanan zance baiyi farinciki ba , amma yasan koba komai kuma koshi yayiwa yarinyar ciki ko bashi bane duniya zata dinga yimasa kallon mazinaci ."

Yau Harun yayi shirin zuwa gurin aikinsu , an sami nasarori da dama kuma ansami sauyi a gurin , zaune suke shida wani abokinsa wanda jininsu ya had'i , tambayarshi Harun yayi yace ”ina wanan yarinyar , dariya abokin nasa yayi yace ”ai tayi aure sati uku da suka wuce , shafa sajensa Harun yayi yace ”ashe tayi aure , dariya abokin yakuma sawa yace ”yadai aboki ?"wani ya rigaka ko ?"Harun ne yakama murmishi yana basarwa ,daganan ya wuce gidan su momy ."
Chapter 11 · 0% Book details