Sashe 5
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safeenah ta juya da sauri tana kallon Hajiya tace "ba nace maki tana ciki ba" Hajiya ta shiga buga kofar da sauri tana cewa "don ubanki fito ki bar gidan nn kar na kasheki shegiya munafuka, gidan da na yafi karfinki wllh" a tsorace cikin kuka ba tare da ta shirya ba tace "kiyi hkuri mumy xan....." buge mata baki Aliyu yyi da karfi ya mike tsaye yana kallonta ya sa kafa ya haureta, ta toshe bakinta ta koma baya da sauri hawaye na cigaba da bin kuncinta, safeenah tace "Hajiya kawae mu kira kafinta ne ya balla kofar don ba budewa xata yi ba," a fusace Hajiya tace "to wae ina Aliyu ne, ya xo ko xae iya ya bude don wllh wllh yau sae ta bar gidan nn don ubanta," safeena ta ciro waya tace "bari na kirasa," yana jin hka ya ciro wayarsa da sauri ya kashe, safeena tace "kinji tsiya wae a kashe yake," nn Hajiya da safeena suka dinga xaginta suna cewa ta bude kofar ta xo ta wuce gida kar su balla su kasheta, ita dae bata ce komai sae kukan da take yi a hankali, shi ko Aliyu na tsaye sae kallon kofar yake yana girgixa kai, sun kai kusan minti goma a dakin suna abu daya daga bisanni suka bar dakin Hajiya nacewa "ae yau da ta kwana gidan nn gwara gidan ya babbake, bari muje mu samo kafinta ya cire kofar kawae, shi kuma Aliyu don tsabar wlknci ficewa yyi ya bar gidan ga yar iska ta xo" Safeena tace "ni wllh Hajiya tsoro ma Aliyun nn yake bani," yana ji sun fita daga gidan gaba daya ya juya yana kallon Inteesar da ta xama kmr wata marainiya ya daga hannu xae xabga mata mari ta fasa ihu sae kuma ya fasa, ya fixgota yana mata mugun kallo yace "daga yau kika sake bara min wnn shegen bakin naki kmr na xaki a gidan nn sae na cire maki hakora wawiya kawae," yana kaiwa nn ya bude kofar ya fice ya bar ta nn durkushe tana kuka, direct gun mai gadi ya nufa yace "kar ka bude ma kowa gate ya shigo gidan nn, snn kar ka bari ta ciki ta fita" mai gadi yace "to yallabae, snn ya shiga motarsa ya bar gidan shima, hka Inteesar ta yini tana kuka ranar gashi mai gadi yaki barin ta fita, tsoranta daya kar su Hajiya su dawo, cikin ikon Allah kuwa bata ga sun dawo ba, har ta kwanta ranar Aliyu bae dawo gidan ba. Yau tana xaune ita kadae abun duniya ya isheta rabonta da Aliyu tun ranar da Hajiya ta xo gidan aka yi wnn draman gashi yau kusan kwana uku, budewar kofar dakinta yasa ta mike a raxane don ynxu ba karamin tsoron gidan take ba, Zainab ce ta karaso tana kallon Inteesar tace "wae dama ashe aure Aliyu xae yi Inteesar," jikin Inteesar yyi sanyi kmr lkcn ta fara jin xancen, tayi shiru bata ce komai ba, ganin Zainab ma tayi shiru yasa tace "wa ya gaya maki," Zainab tace "yau Abba ke gaya ma Inna wae ashe ma saura sati daya, tun safe inna ke kuka tana tsine tsine a gidan wae xamanta ya xo karshe a gidan," Inteesar ta xauna gefen gado bata sake cewa komai ba, Zainab tace "in ni ce ke Inteesar wlh baxan xauna gidan nn ba, infact na gama auren ma gaba daya, duka duka watanku nawa da auren ko three month fa bae cika ba," budewar kofar dakin yasa suka juya da sauri suna kallon waye, Aliyu ne ya shigo dakin yana ma Zainab wani irin kallo, nn da nn hanjin cikinta ya kada. . Zainab ta dauki mayafinta gabanta na faduwa ta kalli Inteesar tace "na tafi inteesar, inna tace na xo nace maki ki hada kayanki tana nn xuwa," tana kai wa nn ta juya ta dake tana kallonsa tace "ina yini yaya," bae tanka mata ba sae dae har lkcn kallonta yake, ta bi ta gefensa xata wuce ya cakumota ya watsa mata mari cikin tsawa yace "daga yau, na sake ganin shegun kafafunki cikin gidana wllh sae na ji maki," kuka ta fashe da tace "ni me nayi maka xaka mareni hka wlh sae na gaya ka da Abba," wani marin ya kai mata snn ya fixgota ya shiga janta har suka fita daga gidan, ita dae Inteesar bata ce komai ba sae kifa kanta da tayi kan gado tana kukan da bata san dalilinsa ba, suna isa gate Aliyu yace mamaigadi "kar ka sake barin yarinyar nn ta shigo gidan nn," mai gadi yace "to yallabae," snn ya jefar da ita waje ya rufe gate din ya koma cikin gida. Washegarin ranar da daddare Inteesar na gaban madubi ta fito daga wanka knn tana shafe shafenta gaban madubi wayarsa dakegunta yyi ring ta duba ta gane nmbrsa ce dayan, ta daga yace "ina jiranki downstairs," da kmraxa ta je ba sae kuma ta dauki Hijab dinta har kasa ta sa snn ta sauko downstairs yana xaune remote a hannunsa, yana daura idonsa kanta ya daka mata tsawa "ke daga yau kika sake sa irin wa innan hijaban a gabana sae na ci ubanki daga ke har hijabin, wawuya kawae get out," ganin bbu alamar wasa tattare da shi ya sa ta koma sama ta sa kayan barcinta mai dan mutunci don dama xani kadae ne jikinta snn ta sa gashinta cikin net ta sauko kasa fuskarta a daure, kallo daya yyi mata ya dauke kansa yace "ga kayanki nn ki kwashe su gabana," ta tsura ma akwatinan da ya nuna mata ido snn ta dake tace "na me," ya galla mata harara yace "na xubar wa, c'mon kin xo kin kwashe su gabana ko sai na bata maki rae" ta girgixa kai tana kkrin mayar da hawayenta tace "na yafe bana so, ka kara mata a nata," tana fadin hka ta juya da sauri ta koma sama, ya bi ta da kallo, kan gado ta fada ta fashe da kukan takaici tana data sanin kin bin Zainab da tayi ranan, don dae ko hauka yake baxae je yace xae daukota ba, Aliyu ya cuceta ya walakantata bakin cikin ta daya ynxu ya raba ta da budurcinta, hka ta kwana ranar tana abu daya. Washegari da safe ya shigo dakin yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "ki shirya anjima xa a raka ki registration na Jamb," yana kai wa nn ya juya xae fita ta mike da sauri tace "bbu inda xa ni wllh," ya juya yana mata wani mugun kallo yace "to sae me, me xa a fasa mutuwan ko hisabi, kar Allah yasa kije din jaka kawae" ta fashe da kuka tace "ni a jaka bace wllh, ka jira jaka na nn shigowa nnba da ddewa ba," ya karaso cikin dakin ya kwashe ta da mari ta fasa ihu tana kiran Abbatace "Allah ya isana ban yafe maka ba wlh mugu kawae," juyawa yyi ya fice daga dakin da sauri ta mike jikinta na rawa ta shige bathroom ta rufe da key. Karfe sha biyu saura taji ana ring din Bell, ta sauko gabanta na faduwa don tasan Aliyu baya danna bell, ta karaso kusa da kofar tana lekan ko waye, wani mutumi ta gani tsaye, ta ki bude kofar tace "waye," yace "ina yini madam, Yusuf ne, oga Hydar ne ya aikoni waexamu je registration da ke yau, shi yana buzy," tace "kaje kace masa ban xuwa," bata jira me xae ce ba ta koma sama abunta, da daddare Aliyu ya dawo gidan direct dakinta ya nufa ta hada tea knn xata sha, duk da ba karamin tsorata tayi ba amma ta dake bata nuna ba, kuma taki dago kanta, ya karaso inda take ya fixgota cikin tsawa yace "wani sako kika bada a kawo min daxu," ta shiga kikkifta ido a tsorace tace "ni ka kyaleni wllh," ya jefar da ita ya fice daga dakin ta bi sa da harara, ko minti biyar ba ayi ba ya dawo rike da belt, ta fasa ihu a tsorace ta mike tsaye tace "na shiga uku, wayyo Abbana," ya fixgota ya shaketa yana huci yace "na rantse da Allah idan baki kama kanki a gidan nn kinsan da wanda kike xaune ba sae na sumar dake watarana" yana kai wa nn ya buga ta da bango ya fice daga dakin, hka ta kwana kuka da ciwon kai ranan, Da safe yana fita ita ma ta shirya xata bar gidan amma mai gadi yaki bude mata gate ta dinga rusa masa kuka tana rokansa ya bude mata gate amma yace "to ko yau sae da yallabae ya kara jaddada min cewar kar na bari ki fita," ta fashe da kuka abun tausayi ta kasa cewa komai, kmr daga sama taji Muryar inna da karfi tana cewa "salama alekum, kin tabbata nn ne gidan kursum" . Inteesar na jin muryar inna ta fasa kuka tana kallon gate din, inna ta shiga bubbuga gate din tana cewa "lah nn ne kursum ga muryarta nn naji, a bude mana" Mai gadin yace "waye wnn," inna ta bude baki tace "nashiga uku amar ya waye? Waye ke min wnn tambayar," Inteesar tace "malam ka bude mata kakata ce fa," mai gadi yace "ko ma wacece yallabae yace kar na bude ma kowa gate," cikin daga murya inna tace "yau naga jaraba waye wnn kuma" kursum tace "mai gadi ne," inna tace "mai gadi? To ya ci ubansa ba a gaya masa ko ni wacece bane ni da gidan jikokina xae hana ni shiga," kursum ta fashe da dariya inna tace "ke ban san shashanci fa," sae kuma ta shiga kiran Inteesar," cikin kuka inteesar tace "Na'am inna yaki bude gate din," a fusace inna tace "yau ni naga jarababben dan iska gate din ta ubanka ce ko ko, kaji min mutum," dariya ma abun yaba mai gadin inna tace "shi Aliyun yana ina," Inteesar tace "oho nima ban sani ba," inna ta shiga buga gatedin da karfi tana duddura ma mai gadi xagi,shi dae yana xaune sae shan rakensa yake inteesar tace "wae kai wani irin mutum ne baka jin ka bude mata gate ne ka maida mutane mahaukata," inna