Sashe 15
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tabe baki tace "aikena kayi to," bata rufe baki ba ya watsa mata mari ta fasa ihu ta durkushe wajen tana kiran Abba, safeena ta leko tace "haba cweety nace ka rabu da ita yarinya ce bata san ciwon kanta ba tukun yarinta na damunta, meye kuma na dukanta, nasiha ya kamata kayi mata dear," Inteesar ta mike tana kuka tace "don uwarki sae ki xo kiyi min nasihar munafuka kawae jaka" yyi kanta ta fasa wani ihun ta saka gudu ta bar wajen ta haura sama tana ci gaba da rusa kuka kmr xata tsaga gidan, ranar hka taci kukanta ta koshi bbu mai lallashi ta gaji ta kwanta tayi bacci ba tare da ta ci abincin dare ba, karfe goma ya shiga dakin nata, ko wanka bata yi ba bare ta canxa kayanta karewarta ma kasa tayi kwanciyarta, ya daga ta ya cire hijabin jikinta snn ya mayar da ita kan gado yana kallon fuskarta, ya lulluba mata bargo ya kashe mata wutan dakin ya fita. Washegari kin fitowa tayi daga dakinta tana ta xaune har axahar bata karya ba, ya shigo dakin ya tarar da ita xaune kan darduma ta idar da sllh, ta mike ta shige bathroom ta bar sa nn tsaye, yyi tsaki ya fice daga dakin, ranar ma hka suka fita suka barta ita kadae a gidan, taci kukanta ta fito ganin yunwa na neman hallakata ta nemi abinda xata ci, har da na dare ta tanada don ba fitowa xata sake yi ba, Ana gobe xata je ta xana jamb dinta tun safe take ta karatu har kusan sha biyu bata karya ba, ta rufe biology text book din dake hannunta ta fito xuwa falo don neman abinda xata ci a xuciyarta tana cewa inda wnn mutumin kirki ne da ba shi xae koya min abubuwan da na manta a chemistry ba, tayi tsaki ta shiga kitchen ta tarar safeena ta daura girki amma bata kitchen din littafin da take amfani da tana koyan girki na kitchen din a ajiye da alamar tuwon shinkafa da miyar egusi xata yi ganin irin kayan miyan da aka jera a kitchen din ko wanne a cikin dan plate, inteesar ta girgixa kai tace "dakikiya kawae ynxu ina dauke littafin nn bbu abinda xata iya yi a nn," xata daura indomie kawae wata xuciyar tace ta dauke littafin kawae ta boye, ba shiri ta dauke littafin ta ma fasa girkin gaba daya ta fice da sauri ta haura sama a stairs suka hadu da safeena, safeena tayi mata wani kallon banxa tana karairaya, inteesar tayi dariya can ciki ciki a xuciyarta tace "i jez dey laf," ta shige dakinta, safeena na shiga kitchen ta nemi littafi ta rasa ta fito da sauri ta koma sama ta buga kofar dakin inteesar, inteesar ta fito tana gyara daurin dankwalinta a walakance tace "lafiya," safeena tayi mata mugun kallo tace "maxa fito min da kayana kar na nakada maki shegen duka a nn," inteesar tayi dariya tace "meye kuma kayanki," safeena na huci ta kasa cewa komai don wnn ae abun kunya ne a gunta anata tunanin, inteesar tayi tsaki tana yatsine fuska xata rufe kofar safeena ta fixgota ta kai mata mari, ta fasa ihu tace "wayyoo Abbana, wlh sae na rama," safeena ta kai mata wani marin, inteesar ta fasa wani kukan tace "don uwarki me nayi maki xaki dokeni, bnxa kawae dakikiya, karuwa da ke," Safeena tayo waje da ido tace "ni kike ce ma karuwa," Inteesar tace "ance maki din karuwa yar iska, uban waye bae san kinyi karuwanci ba," tayi kan Inteesar ta rufeta da duka dai dai nn Aliyu ya shigo gidan, ya haura sama da sauri da mamaki yana kallonsu ya fixge Safeena a fusace yace "ke jakar wace gari ce" tana huci tace "karuwa fa tace min Aliyu," ya watsa mata mari yace "ta ce maki din, sharri tayi maki, ko bakiyi karuwancin bane.