← Book details Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta bita da sauri ta kamo hannunta tace "haba inteesar bafa kiyi kama da jahila ba," kuka inteesar ta fashe da tace "baxa ki gane ba Aneesah wllh bana sonsa bana son cikinsa, bae damu dani ba sae wahala nke ta sha," Aneesah ta xaunar da ita tana kallonta da tausayi tace "ni na tabbatar maki kina haife wnn cikin xaki ga tsantsan so gun mijinki, ni banga rashin son da mijinki yake maki ba inteesar nafa ga abinda yyi ma kishiyarki ranar sbda ke, don me xaki walakanta kyautar da Allah ya baki yar uwa," inteesar tayi shiru tana ta sauraran Aneesah tana ta wa'axinta da nasiha, har ta kai Aya snn inteesar ta kirkiro murmushi tace "to ngdd Aneesah, ta dauki shakur tana ta wasa da shi yana mata dariya, tace "amma a gida kika haife yaron nn ko Aneesah," Aneesah tace "me kika gani," inteesar tayi yake tace "aa kawae tambaya ce nayi don ni dae ina tsoran Haihuwa," Aneesah tayi dariya tace "A'a a asibiti na haifesa," inteesar tace "wani asibitn?" Aneesah tace "A'a tender care na haifesa, ai kin san asibitin bbu wani nisa," Inteesar tace "A'a" Aneesah ta gaya mata inda asibitin yake kuma dama abnda kawae take son ji knn, ta mike xuciyarta fal murna ta bar gidan. . Inteesar na fita daga gidan Aneesah ta koma gida cike da jin ddi ta shiga dakinta tana haki kmr warce tayi gudu, ta tabe baki jin wakan da ke tashi dakin safeena, sae da ta huta na kusan minti goma snn ta mike ta dauki purse dinta ta fita daga dakin, dakin Aliyu ta bude a hankali ta shiga ta bude drawer din da taji yace Safeena ta bude ta dauki kudi ranan, taji ta a kulle, tace "na shiga uku," ta mike ta fara kalle kallen cikin dakin kmr xata yi kuka, to ina xata samu kudin xuwa asibitin ynxu, drawers din dakin ta dinga bubbudewa gaba daya ko xata ga kudi amma bbu, duk ta gaji sae haki take, tuni ta fara kuka tana cewa "Allah ka taimakeni in ga kudi" ta bude lst bedside drawer din taga wani babban book an rubuta my diary a gaba, tayi tsaki ta ajiye ta mayar da drawern, ta mike ta isa wardrobe din da yake ajiye kayansa na sawa ta bude ta lumshe idonta sakamakon wani kamshi me ddi da ya bugi hancinta, ta gama bincikenta nn ma ba ta ga kudi ba ta rufe ta xube kasa ta daura hannu a ka tace "wayyoo Abbana wllh ni na gaji," ko ina ta bude daga taga Allura sae taga magunguna da dae kayan asibiti kmr tsiya wnn wace irin jaraba ce, kmr ance ta mike ta daga filo taga dubu daddaya karkashin filon har da Atm dinsa ta wara ido tace "wayyo Allahna," ta kwashi kudin ta shiga kirgasu da sauri hannunta na rawa taga dubu sha biyu ne, ta dan marairaice fuska to xae isheta taje asibitin ma kuwa, tayi tsaki ta bude purse dinta ta xuba kudin snn ta juya xata fita daga dakin taje dakinta ta sha ruwa don mugun kishi take ji don tsabar son taje ta cire cikin ta nemi xaxxabin dake tattare da ita ta rasa sae kasala kawae, har ta isa bakin kofa ta dawo da sauri tuna baxae rasa ruwa a dakinsa ba da tayi ta bude fridge dina ta ko ga ruwa ta dauka ta bude ta sha snn ta rufe fridge din ta dauki sauran ta fita daga dakin, duk wnn abinda take safeena bata sani ba, tana daki kwance tana ta shan kida cike da jin ddi, jiran jin ihun Inteesar kawae take a ko wani lkci, Inteesar kam har ta fita daga gidan rike da purse dinta cikin Hijab, mai gadi dae bae ce mata kala ba ta bude gate ta fice abinta sae da ta isa bakin titi snn ta tsayar da tricycle tayi masa kwatancan asibitin da Aneesah ta gaya mata yace ta bada dari biyu, ta shiga tace mu je. Wasa wasa asibitin shegen nisa ne da shi, yyi parkin dae dae gate din asibitin ya juyo yana kallonta yace "mun kawo Hajiya," ta fito tana kare ma asibitin da ma anguwar kallo, ta bude purse ta ciro dubu daya cikin kudin ta basa kudin ya rage dubu sha daya, ya bata canjinta ta karasa cikin asibitin gabanta na faduwa, wnn dae da ganin asibitin nn ba na talakawa bne, anya kuwa xasuyi mata abortion a dubu sha daya kuwa ta dan karyar da kanta abun tausayi, da Addu'arta ta shiga asibitin, babba ne ssae ta karasa cikin reception ta xauna ganin patients dayawa a xaune, ta shiga kare ma reception din kallo, ta kai kusan minti talatin a xaune ba a xo kanta ba duk ta gaji, taji kwanciya kawae take son yi ga amai dake taso mata, ta daura kanta a cinya taji kmr ta rusa ihu duk ta rasa ina xata sa ranta, wata nurse ce ta dafa ta ta dago da sauri tana kallonta, Nurse din tace "yhur card nmbr Madam," inteesar ta shiga kalle kalle xata yi magana taji yawu ya cika bakinta, nurse din ta lura da hka ta nuna mata bayin dake kasan reception ta karasa ta xubda yawun ta kora ruwa snn ta dawo, nurse din ta debo vitamin c ta mika mata ta sa a baki tayi mata gdya ta karba, tana kallon Nurse din tace "i dnt have a card in here," Nurse din tace "to dole sae kin yanki kati," Inteesar tayi shiru snn tace "nawa ake yankan katin," nurse din tace "family card dubu biyar, na mutum daya dubu 2 da dari 5," inteesar tayo waje da ido tana kallonta, ganin xata bata ma nurse din lkci ga kuma patients dayawa suna jira yasa tace "to ki yankar min na mutum daya," nurse din tace "ok" snn tayi gaba, a hankali inteesar tace "na shiga uku, to ai kudin ya kare," ba ajima ba nurse din ta fito daga wani dan daki ta mika mata katin snn wata nurse ta daddubata ta duba har da weight dinta tayi rubutu a file tasa nurse ta rakata bayi aka xuba mata ruwa a kanta don temperature dinta yyi sama, ita dae binsu kawae take, a xuciyarta tace ko da yake basu san me ya kawota ba shiyasa suke bata lkcnsu, ita dae ynxu likita kawae take son gani, wata nurse ce ta gwada mata office din doctor din da xata shiga a sama, tana rike da file dinta ta haura sama da kyar ta karasa office din tayi knock. A hankali Inteesar ta tura kofar bayan an mata ixinin shigowa office din, cak ta tsaya daga bakin kofa tana kallon likitar, doctor din ma ta mike tsaye tana kallon Inteesar da mamaki tace "fateema," inteesar ta kirkiro murmushi gabanta na faduwa ta karaso office din a sanyaye, ta nuna mata kujera ta xauna, doctor din tace "daga ina kike hka fateema, me ya kawo ki nn," ta rasa karyan da xata mata, da kyar bakinta na rawa ta ce"banda lfya ne," doctor din ta hade rae tace "shi Aliyun fa," inteesar ta rasa me xata ce ga xuciyarta sae tashi yake, likitan ta dawo kusa da ita tana kallonta ta dago kanta tana kallon cikin idonta tace "ciki gare ki fateema," inteesar tayi shiru bata ce komai ba, doctor din ta ciro wayarta ranta a bace ta shiga neman layin Aliyu, da sauri inteesar ta dakatar da ita gabanta na faduwa tace "A'a don Allah doctor kar ki kirasa wllh ya sani kuma yana dubani nice dai bana son shi ya duba ni, Allah yana kula dani doctor kawae ni ce bana so, idan yaji na xo nn xae bata min rae don bae sani ba," doctor din tace "haba fateema, to ma don me xaki fita ba tare da ixinin mijinki ba, kuma meyasa baki son ya duba ki," inteesar ta fashe da kuka tace "wllh ni bana sonsa doctor," doctor din ta tsaya da mamaki tana kallonta snn tace "sbda me fateema, gashi har rabo ya shigo kice baki son mijinki," Inteesar ta sunkuyar da kai tana hawaye, doctor din tayi shiru tana kallonta, can ta koma sit dinta ta xauna ta shiga yi mata nasiha kan cewar ta rungumi mijinta ta cire duk wani rashin sonsa a ranta, ita dae bata ce komai ba sae kukan da take a hankali, Doctor din tace "yyi maki scan ne?" inteesar ta girgixa kanta tace "A'a nace masa bana so," doctor din ta harareta tace "to karki sake yi ma mijinki musu baki san aljanarki na karkashin kafarsa ba," inteesar ta dan tabe baki kanta a kasa ba tare da ta bari doctor din ta lura ba, doctor din ta yagi wani takarda ta danyi rubuce rubuce snn ta danna bell wata nurse ta xo da sauri, ta mika mata takardar tace "scan xa ayi yi mata sisterna ce," doctor din ta kalli Inteesar tace "tashi ki bita," inteesar ta mike a sanyaye ta bi bayan nurse din har sun kai bakin kofa ta juya tana kallon doctor Maryam tace "don Allah doctor kar ki kirasa wlh xae bata min rae,"doctorn tayi murmushi tace "baxan kirasa ba ki kwantar da hankalinki" bayan kusan awa daya inteesar da nurse din suka shigo da sakamakon a hannun nurse din, ta mika ma doctor maryam ta fita, doctorn ta bude takardar tana dubawa, inteesar dae kallonta kawae take ranta a hade, ba shiri taga doctor maryam ta mike tsaye da sauri tace "waw Ahmdllh, twins 4 Aliyu, Allahu akbar," ta rungume inteesar tace "Allah ya raba lfya kanwata, kinga ma yan biyu ne" inteesar ta sunkuyar da kanta da sauri hawaye ya cika idonta, hka doctorn ta dinga mata surutu cike da murna kmr ita xata haifa ma cikin, ita dae bata ce mata komai ba daga karshe ta hada mata magunguna, da allurori a office dinta ta xuba mata su a leda da takardar scan din tace "to maxa tashi ki koma gida sae ki kai masa takardar scan din, sae ya fada maki yanda xaki sha magungunan yyi maki alluran," Inteesar ta mike da sauri kmr jira take tace "ngdd
Chapter 23 · 0% Book details