← Book details Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kan gadon fuskarta a daure tayi hanyar fita daga dakin ya fixgota yace "ina magana xaki fita don baki da kunya," ta hararesa tace "to ca nayi maka banyi sallah bane" ya wara ido ya shaketa yace "ni kike kallo hka, wae me sa kika raina ni hka ne yarinyar nn?" ta girgixa masa kai kmr xata yi kuka tace "kayi hkuri baxan sake ba," yyi kwafa ya saketa yana kallonta tayi hanyar fita da sauri ya daka mata tsawa "ke! Uban wa xae gyara maki dakin?" ta juya tana kallon dakin snn ta dan yi tsaki ta dawo ta fara gyara gadon, ya bude Bathroom ya shiga wanka, tana gama gyara dakin ta fice da sauri tayi hanyar dakinta. Inteesar na jin muryarsa a kasa ta mike da sauri ta isa jikin window tana kallonsa yana tsaye jikin motarsa yana magana da masu gadi, ta juya da sauri hawaye ya cika idonta, jin ya tada motar ne yasa ta juya tana kallonsa har ya bar gidan snn ta dawo gefen gado ta xauna a sanyaye, tana nn a hka bayan fitarsa da kmr minti goma Zainab ta shigo gidan, Zainab ta ajiye mayafinta tana kallon Inteesar da ta kirkiro murmushi tace "lah daga ina kike da safen nn," Zainab tace "wae jiya da kuka xo gida da daddare da ya Aliyu me ya faru" Inteesar tayi shiru tana kallon Zainab snn tace"me aka ce ya faru?", Zainab tace "oho, Abba yace mu taho gida tare ynxu, ya kira Aliyu tun jiya ya ki dagawa," Inteesar tace "to ae baya nn," Zainab ta galla mata harara tace "to ina ruwana, Abba ca yyi mu taho gida ynxun nn da ke," Inteesar ta girgixa kai cikin confusion tace "to ki kira ya Aliyun ki fara gaya masa," Zainab ta bude baki tana kallonta tace "iyye sae na kirasa xa mu tafi," Inteesar tace "to ae bae sani ba," da mamaki Zainab tace "Ahh lallai," snn ta juya tace "sae anjima," Inteesar ta bi ta da sauri tace "ki tsaya don Allah Zainab," Zainab xa tayi magana wayar dake gaban madubi na Aliyu yyi ring, Inteesar ta karasa gaban madubin tana kallon wayar a tunaninta Safeena ce, ta daga wayar ta kara a kunne bata ce komai ba, "kina jina, idan kika kuskura kika fita gida ba tare da izinina ba xaki sha mamaki, just dare me, ki ga" yana kai wa nn ya katse kiran, ta juya tana kallon Zainab ta marairaice tace "yace kar na fita Zainab," ko kallonta Zainab bata yi ba tayi hanyar kofa, Inteesar ta bi ta da kallo har ta fice. Da yamma tana kwance abun duniya ya isheta tun tean data sha da safe bata sake cin komai ba ta rasa me ke damunta, jin an bude kofar downstairs ya sata mike da sauri a tunaninta Zainab ce ta kuma dawowa, ta xauna gefen gado tana jiran shigowartata, kamshin turarensa da taji yasa ta gane shi ne, ta koma ta kwanta a hankali tana kallon kofar dakin, ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, bata ce masa komai ba, ya tabe baki yace "wa ya shigo gidan nn daxu?" tayi kmr bata ji sa ba ya daka mata tsawa "ba da ke nake ba," xata yi magana taji ana kiransa da darlin, ya juya da sauri yace "srry bby, magana nake da wnn ballagaxar," Inteesar tamike tsaye da sauri tana kallon safeenah da ke lekota, ta karaso bakin kofar tanai ma safeenah wani irin kallo snn tace "karuwancin ne har sae kin biyosa gida don rashin sanin ciwon kai, ke kam kin banu banxa kawae sha sha sha," bata rufe baki ba Aliyu ya sauke mata mari ya fixgota ya jefar kan gado yana huci ya nuna ta da dan yatsa yace "ki shiga hankalinki wllh, don kika sake ce mata karuwa sae na illata ki, dabba kawae" ta sulalo kasa daga kan gadon ta fashe da kuka ssae tace "Allah ya isa ban yafe maka ba mugu kawae mara....." wani wawan marin ya sake kai mata hade da buge mata baki da karfi yana huci nn da nn sae ga jini, ta fasa ihu a gigice, safeena ta dafe kanta tare da sauke ajiyar xuciya tana yatsine fuska tace "kai bby ban cika son hayaniya ba wllh, muyi abinda ya kawo mu na bar nn plss," ya ce "srry bby," snn ya kamahannunta suka fita daga dakin tana ma Inteesar wani irin kallo tana murmushi, kuka Inteesar ta dinga yi kmr ranta xae fita ta hade kanta da gwiwa, tana nn a hka suka sake bude kofar dakin suka shigo, taji yace "nan fa bby?" Safeenah ta dan yatsine fuska snn tace "yauwa nn yafi dear, nn din nake so can bae yi min ba,". Aliyu yyishiru yana kallon safeenah, ta dan matso kusa da shi ta yi masa fari da ido tace "mun gama da wnn, kuma ni bna son irin paint din nn, mu jedear na fara jin yunwa," tana fadin hka ta juya xata fita daga dakin ya riko hannunta a hankali yace "meyasa baki son wancan dakin bby?" ta yatsine fuska tana masa wani irin kallo tace "can bai yi min ba nn nake so," ya juya yana kallon Inteesar da har lkcn ke kuka a hankali kanta kife a gwiwanta, ya maida kallonsa ga safeenah yace "to na bar maki dakina, ni sae na koma wancan," ta xaro masa ido tace "No! Ni wnn dakin nake so," yyi shiru yana kallonta, Inteesar ta mike tsaye ta dauki Hijab dinta ta sa ta ciro flat shoe dinta shima ta sa snn tayi hanyar fita, duk suka bi ta da kallo har ta iso inda suke tsaye tabi ta gefensa xata fita ya fixgota, "ke? Gidan ubanwa xaki," ta galla masa harara da jajayen idonta tace "gidan ubana xani," yace "ko?" tace "eh," ya aketa ya gyada kai yana murmushin mugunta yace "to tafi," cikin kuka tace "ni wllh sae na tafi," ya daka mata tsawa ya fixgota yana kallonta yace "ae shine nace ki tafi na gani," ta fashe da kuka ta xube wajen tana kiran Abbanta, safeenah ta dafe kanta tare da jan dogon tsaki tace "gosh! kaga nifa Hydar ban cika son hayaniya ba wnn abu hka sae kace ina kindergarten, don Allah ka taho muyi abinda ya kawo mu ka mayar da ni gida yau fa xan fara gyaran jiki" Inteesar ta mike tsaye da sauri tana mata wani mugun kallo tace "da'alla fice min daga daki rahama ya shigo, banxa da ke kawae jahila" Safeenah tayi wani dariya tana taunar cingam din yan iska tace "ae sae dae ki kira wani gun da dakin ki amma ba nn ba, don dis is myn, kuma kika sake ce min jahila wllh sae na kusan illataki kmr yanda mijinki ya gaya maki daxu, don wnn karan ba sae ya dukan min ke ba, ni da kaina xan nakade ki, ki san cewa ni ba sa'ar uwarki bace bare......" bata rufe baki ba Inteesar ta sauke mata tagwayen mari masu rae da lfya nn da nn fuskarta ya koma ja don axaba, ta dafe kuncinta a gigice tana kallon Aliyu da ya jingina jikin bango rungume da hannayensa yana kallon Inteesar da mamaki tace "wat? She slapped me Hydar" Inteesar tace "ae kadan ma kika gani," bata jira me Aliyu xae ce ba tayi kanta, inteesar na ganin hka ta fasa ihu a tsorace tayi hanyar bathroom, safeenah ta fixgota ta buga ta da bango ta shaketa tana huci snn ta shiga dukanta kmr an aikota Aliyu yyi kansu da sauri ya fixge safeenar ya watsa mata mari ya buga ta da bango yana huci yace "don ubanki kasheta xakiyi ne," Safeena tayo waje da ido tana kallonsa da mamaki, Inteesar ta sulale kasa gabanta na faduwa tana kallonsu, Safeenah ta girgixa kai ta fashe da kuka tana kallon Aliyun, ya saketa ya dafa bango tare da sauke ajiyar xuciya, can ya dawo gabanta a hankali yace "meyasa xaki kulata Safeenah baki ga yarinya bace warce bata san ciwan kanta ba, bbu abinda ta sani nn da kike ganinta she's just a kid," Inteesar ta mike tsaye tace "ku dae ne baku san ciwon kanku ba amma ni nasan ciwon kai na," Aliyu ya bude baki da mamaki yana kallonta, tayi hanyar bathroom da sauri xata shige ya bita ya fixgota a fusace, ta fasa masa ihu tare da durkushewa a kasa tace "wayyoo Abbana," ya durkushe shima da sauri gabanta yana kallonta yace "me ya faru?" ta dago tana kallonsa kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne xa ka doke ni . Aliyu yyi kwafa ya mike tsaye, ita ko ta ja da baya daga xaunen da take tana goge hawayenta, ya juya yana kallon Safeena dake hawayen takaici xae yi magana ta juya da sauri ta bar dakin yaji ta bude kofar dakinsa ya gane jakarta xata dauka a ciki ta bar gidan, ya juyo yana kallon Inteesar da ta bi ta da harara, ya sa kafa ya haureta yace "xan babbalaki a gidan nn wllh idan kika yi wasa," ta mike tsaye da sauri tayi tsaki can ciki ta koma kan gado ta xauna tana ci gaba da share hawayen fuskarta, danna bell din gidan da aka yi yasa ya juya ya fita daga dakin dae dae lkcn da Safeena ma ta fito daga dakinsa rike da handbag dinta, yace "haba bby ina kuma xaki?," ko kallonsa bata yi ba ta fara sauka daga stairs, ya bi ta da sauri yana kiran sunanta,tsaye suka ga Hajiya a falon tana kare ma ko ina kallo fuskarta a tamke, ya juya da sauri ya koma dakin Inteesar, tana nn yanda ya barta ya karasa gabanta yana kallonta ya kama hannunta ta fixge tana hararansa tace "meye hka," ya buge bakinta ya fixogata ya bude bathroom ya tura ta ciki snn ya kulle da makulli ya cire makullin yasa a aljihu, kofar ta shiga bubbugawa tana kuka, ya fice daga dakin ya sauka downstairs da sauri, tsaye yaga safeena kusa da Hajiyan tana mata magana tana kuka, ko me take ce mata oho, ya karaso yana kallonsu Hajiyar dake ta faman huci tayi
Chapter 3 · 0% Book details