← Book details Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliyu bae sake ce mata komai ba sae gudun bala'in da ya dinga yi kmr xae tashi sama, hankalinta yyi mugun tashi ta ma rasa mae xata ce masa don tsoro, ta dake daga karshe da kyar Muryarta na rawa tace "wae ni ya Aliyu ina xa ka kai ni ne don Allah," ya taka brake yyi arkin da sauri yana kallonta cikin tsawa yace "kika ce me?" ta tsorata ssae ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yyi mata wani mugun kallo yace "sayar da ke xanje nayi," bata dago kai ba bare tace masa komai yyi kwafa ya ja motar suka bar wajen, lkci daya hankalinta ya kwanta ganinsu da tayi anguwansu, yana gama parkin kuwa ta bude kofa xata fita da sauri yyi hanxarin fixgota yana hararta yace "kin dae ji me na ce maki, kuma wnn hawayen bana son ganinsa a fuskarki" ta fixge hannunta ta fice da sauri daga motar snn ta watsa masa harara hade da jan tsaki tace "ban ji ba," tana fadin hka tayi cikin gidan da gudu ya bita da sauri, tana isa gate cikin rashin sa'a tayi tuntube tayi gaba xata fadi yyi saurin rikota ta fado kansa, ta marairaice fuska a tsorace tace "don Allah kayi hkuri ba da kai nake ba," bae ce mata komai ba ya shiga janta kmr wata dabba tana biye da shi a baya har suka iso falon Abba, sae a snn ya juya yana kallonta fuskarsaa murtuke yace "Allah ya baki sa'a ki ki yin abinda nace maki, wllh sae na kusan sumar dake a gida yau," bata ce komai ba ya ja ta suka shiga cikin falon, Abba na xaune remote a hannunsa yana canxa tasha, Aliyu kadae ne yyi karfin halin yin sallama ita kam inteesar kasa wa tayi ji tayi hka kawae gabanta na faduwa, ta xauna Aliyu ya xauna gefenta snn ya gaida Abban nasa ba tare da ya kallesa ba, Abba ya amsa bbu yabo bbu fallasa snn ya kalli Inteesar da ta kirkiro murmushi tana gaishesa ya amsa da fara'arsa yana tambayarta ya gidan, ta sunkuyar da kai tace lfya lau Abba, murya can kasa Aliyu yace "ga ta nn Abba na kawo ta," ko kallonsa Abba bae yi ba ya fara magana kmr hka "tambayace kawae xan maki Fateemah, amma gskya kawae nake son ki gaya min kar kiyi min karya ban san ki dakarya ba," tayi shiru gabanta na faduwa tana kalln Abban, ya dan dau lkci snn yace "wae da amincewarki Aliyu xae kara aure?" ji tayi komai nata ya tsaya ta kasa dago kai bare ayi expectn amsa daga gare ta, nn da nn taji hawaye na neman cika mata ido, Aliyu ya kamo hannunta ya hade da nasa a boye, ta gane abinda yake nufi, suka ji muryan Abba na cewa "magana nake fateema kin yi shiru, sharri yyi maki ko?" da ganin Abba kasan ransa a bace yake, da kyar ta iya bude baki ba tare da ta kalli Abban ba tace "eh hka ne Abba da sanina," Abba ya girgixa kai yace "karya kike," tayi kkrin boye hawayenta tace "da gske Abba na sani ni ce nace yyi," Abba yyi shiru yana kallonsu gaba daya daga bisanni yace "to yyi yau, baxan hanaka kara aure ba Aliyu kuma ni kam bbu abinda xan ce maka da ya wuce Allah ya taimaka, snn abu na karshe da nake son na gaya maka shine ka tabbatar kafin kayi auren naka 'ya ta ta fara karatu tayi settle dwn idan ba hka ba wllh sae na wargaxa komai, ka tashi ka ban wuri" bbu ko dar bare damuwa Aliyu ya mike yace "ngd Abba," ya sace kallonta, ita ma kallonsa take hawaye cike idonta da ganinta ta shiga wani yanayi da baxa a iya fassarawa ba ya galla mata harara snn ya fice, Abba yyi shiruyana kallonta snn a hankali ya fara magana"kiyi Hkuri fateema, nayi dana sanin hadaki daAliyu da nayi, kuma ni ban isa hana shi kara aure ba, snn baxan ce kar ki bi mijinki ba amma idan har kin ga baxa ki iya xama gidan ba bayan auren nasa ni nn nace ki tattaro ki dawo gida," kai kawae take gyada ma Abba tana hawaye yyi mata nasiha ssae yana kwantar mata da hankali daga karshe yace ta tashi tashiga cikin gida amma kar ta ce da inna komai tukun, ta mike jikinta a mace tayi masa gdya snn ta fita falon tayi bangaren inna tana kuka ssae, tsaye ta gansa alamar ita yake jira, yana ganin tayi bangaren inna ya daka mata tsawayace "c'mon gida xa mu wuce ina kike tunanin xa ki," ko kallonsa bata yi ba ta saka gudu tayi sashin inna ya bi ta shima da sauri, Kursum da ta fito daga gun inna knn ta bi su da kallo baki bude, saura kiris ya kamata ta afka falon inna tana mayar da numfashi ta fasa ihu tare da xubewa tsakiyar falon, inna dake daki ta fito da gudu tana salati tace "me ya faru?? Daga ina hka?" shi ko ya fixgota a fusace ya shake ta hade da hada ta da bango yana huci yace "don ubanki ina wasa da ke ne?" inna tayo waje da ido snn tayi waje da gudu ta saki kuka cikin daga murya tace "jama'a yau naga ikon Allah xae kasheta gabana, Bukar Bukar ka taho kaga abinda dan ka ke shirin yi da daddaren nn" . Haisam ya karaso da sauri yana kallon inna yace "me ya faru inna," tana kuka wiwi tace "wllh Haisam ina daki na je ajiye kayan da kursum ta gama goge min naji ihu kmr xa a xaga falona, fitowar da xanyi wae sae ganin Aliyu nayi shake da Inteesar yana duka yana buga ta da bango, duk yyi mata kaca kaca ko motsin kirki wllh bata yi yanxu ban san ya ake ciki ba ka taimaka ka kira mun Bukar don Allah," tana kai wa nn ta fashe da wani kukan har da durkushewa kasa, Haisam ya girgixa kai ya shiga falon innar da sauri dai dai bakin kofa ya hadu da Aliyun rike da hannun inteesar yana janta tana kuka tana cewa "wllh ka kyaleni bbu inda xa ni," ya buge mata baki Haisam yace "wae kai wani irin mutum ne Aliyu 4 heaven sake" Aliyu ya watsa masa wani mugun kallo yace "da'alla can get out malam kar na buge ka," inna tayi cikin gida da gudu tana rusa kuka lkci daya tana kwala ma Abba kira, da sauri Aliyu ya ja inteesar suka fice daga gidan tana nonnokewa ya bude mota ya jefata ciki snn ya shige motar ya tada ta, dae dae nn inna ta fito kofar gidan Abba na biye da ita a baya tace "maxa bi shi Bukar ya tada motar," Abba ya girgixa kai cike da takaici yace "kina ma Allah da annabi ki daina daga min hankali a gidan nn baaba wnn wani irin bala'i ne," bae jira mai xata ce ba ya koma cikin gidan ransa a bace. Suna isa gida Aliyu yyi parkin ya bude motar ya fito yana kallnta har lkcin bata daina kuka da take ba ta hade kai da gwiwa, cikin tsawa yace "ko sae na jefar dake waje," taki dago kai bare ta tanka masa, ya fixgota ta fasa masa ihu tana cewa "wllh baxan shiga gidan nn ba ka mayar dani gida," cak ya dauketa ya rufe motarsa tana dukansa bae damu da hkn ba ya shiga gida da ita ya haura sama ya bude dakinsa, nn da nn ta saita kanta cikin muryar kuka tace "ni ka ajiye ni," bae kulata ba ya isa kan gado ya kwantar da ita ta mike da sauri ya turata da karfi ta fada kan gadon snn ya fada kanta, nn da nn ta hadiye kukan da take xuciyarta na bugawa a hankali tace "kayi hkuri ya Aliyu na daina kukan" ya dago yana kallonta da ganinta kasan a tsorace take, ta fara kkrin sauka daga kan gadon ya rikota yace "bbu inda xaki yau nn xaki kwana," kanta ce komai ya kashe wutan dakin, ta fasa masa ihu ya buge mata baki da karfi, ba karamin wahala ya bata ba, don duk sae da ya jagwalgwalata, ganin irin kukan da take da kuma yanda jikinta ke bari duk da bae ma kai ga yi mata komai ba yasa ya kyaleta tare da cewa "ki rufe min baki kar na baki mamaki," ba shiri ta hadiye kukan jikinta na rawa don duk ya tsorata ta, ya rungumota ssae, snn ya dauki wayarsa yyi dialin nmbr safeenah, kmr jira take yana ringin kuwa ta daga, murya can kasa yace "bbyna," ita ma a marairaicen tace "mijina," ya sauke ajiyar xuciya ya daura bakinsa kan gashin inteesar da ta rumtse ido xuciyarta na bugawa, yace "nayi missn naki ssae fa bby, i need yhu safeena," ta danyi dariya tace "matarka fa? Kaje ka sauke need din a kanta mana," ya yamutse fuska yace "me wnn take da shi da xata bani da ya wuce wahala, naki nake so bbyna," tayi dariya ssae snn tace "ka kusa samu dear na, ina amaryartaka," yace "ga ki nn bbynah," nn suka dinga xancen yanda 1st nyt dinsu xae kasance bbu kunya bare tsoran Allah, a hankali Inteesar ta shiga xamewa daga rungumar da yyi mata, ya matseta da karfi ta shiga kokuwa da shi, ya ki sakinta, ya kunna wutan dakin yana kallonta, hawaye ne kwance fuskarta, ta boye fuskar da sauri, bbu yabo bbu fallasa yace "nayi maki wani abu ne kike min kuka don munafurci?" tayi shiru bata ce komai ba har lkcn hawayen da take yaki tsayawa, ya dada rungumeta ya kashe wutan ya ci gaba da wayarsa, suna nn a hka yana ta hirarsa da safeenah har bacci ya dauke Inteesar . Karfe sha biyu da rabi ya kwantar da ita a hankali, snn ya shiga bathroom yyi wanka ya koma wani dakin yyi kwanciyarsa. Da safe taji an watsa mata ruwan sanyi ta farka a tsorace tana kallonsa da mamaki, ya galla mata harara yace "ke kafura ce ina ga ko," bata ce masa komai ba ta sauka daga
Chapter 2 · 0% Book details