Sashe 25
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ni ka kai ni dakinka, xafi nake ji," duk ta rikitasa ya dauketa da sauri ya bude dakin ya fita, sae kuka kuwa take jikinta na rawa, safeena dake fitowa daga dakinta knn ta bisuda kallo xuciyarta na bugawa "kai wayyoo ddi, ta sha ruwan," ko kallonta Aliyu bae yi ba, ita ko inteesar sae kuka take kmrgske, ya kwantar da ita kan gado bayan ya kunna AC yana kallonta yace "ina kika ce ke maki ciwo," a hankali tace "ya daina, wanka kawae xanyi da ruwan xafi," ya shiga bayinsa da sauri ya hada mata ruwan, yana shiga ta mike har tana tuntube ta fice daga dakin da sauri suka kusan cikin karo da safeena dake labe bakin kofa, safeena ta koma baya a tsorace tayi xaton Aliyu ne, inteesar ta watsa mata harara tace "an dae ji kunya," tayi tsaki ta bude kofar dakinta da sauri ta kwashe magungunan kan gadon ta xuba su cikin handbag dinta jikinta na rawa, tana xuba su ta fice da sauri taga safeena tsaye har lkcn kwakwalwarta a jagule to ko bashi tasha bane, inteesar ta wuce ta ta shige dakin Aliyu, dae dae nn ya fito ya tsaya kallonta da mamaki, xae yi magana ta rigasa "ruwa, amm ruwa naje sha," yana mata mugun kallo yace "get out," ta yi kmr xata yi kuka ya daka mata tsawa "ni kike raina ma hankali ko, fitar min a daki munafuka," tayi tsaki ta juya ta fice daga dakin tare da sauke ajiyar xuciya. Bata samu shan maganin ba ranar da daddare har tayi bacci don ido Aliyu ya sa mata, washegari sunday yana gida yana xaune dakinsa na'ura gabansa, safeena ko na daki kwance abun duniya ya isheta, inteesar ta gama duk abinda xata yi da kyar don xaxxabi ne ssae tare da ita, ta rufe dakinta da makulli ta ciro maganin da likitan ya bata jiya ta debo ruwa a bathroom don har lkcn ba ruwa a dakinta, ta xauna kusa da gado, ta fiffito da magungunan daga kwalayensu ta daddauki yanda yace mata, ta tsura ma kwayoyi shiddan dake hannunta ido, ita bata ma taba ganin irinsu ba, ta rumtse idonta ta xuba su a bakinta ta kora da ruwa da sauri ta hadiye su. TAMMAT ALHAMDULILLAHI.