Sashe 22
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawae yake, Hajiya da hankalinta yyi mugun tashi bata ga fuskar da xata ma Aliyu magana ba da ya shigo da ya fice daga gidan, tab aiko gwara ta nemo yanda xa ayi da cikin nn, ynxu Aliyu dama sae ya iya kwana daki daya da yarinyar nn duk cika bakinsa, hka aka yi biki hankalin inna rabi na gurin Inteesar rabi na gun bikin, duk aka yi abubuwa masha Allah, amma inteesar na kwance tana fama da kanta, safeena ma ta xo ranar bikin tana daddaga hanci ita matar Aliyu inna ta kunyatata gaban lodin jama'ar biki su kursum dariya kmr xasu shide, ko minti daya bata kara a gidan ba tayi gaba ba shiri jikinta a sanyaye har ga Allah tsoran tsohuwar nn take, ran Hajiya yyi mugun baci amma bbu yanda ta iya da inna, washegarin ranar da aka kai Amarya da daddare Aliyu ya shigo falon inna bae ko kalli innar ba ya durkusa gaban inteesar dake kwance idonta biyu, ya daura hannu a goshinta yace "amma yau bakiyi amai ba ko," a fusace inna tace "kaji gantalalle wani irin bata yi amai ba, ae hanjin cikinta ne kadae bae xaxxago ba yau har tsorata nayi nace to ko su ne ke shirin fitowa" Aliyu yyi mata mugun kallo yace "to ke kuma wa ya somo bakin ki nn, iyayi kawae," sae abun ya ba Inteesar dariya ya dago ta yana kallonta yace "Abba na neman mu, xaki iya ko na daukeki," ta marairaice tace ynxu, ya gyada mata kai, ita mugun kunyan Abba take ji har ma da momynta, duk shigowar da momy take ta gaisheta kar inna ta xaxxageta tace taki xuwa, Inteesar yi take kmr tana bacci, inna ta mike tsaye da sauri tace "bari kawae na kama hannunta mu je," Aliyu ya bude baki yana kallonta yace "wae meyasa kike son shiga tsabgar da ba taki ba ne," bae jira me xata ce ba ya harareta ya sa ma Inteesar hijab dinta ya dauketa suka fice, inna tayi kmr xata yi kuka tace "ni ban san meyasa yaron nn ya rainani da tsufa na da furfurata ba," a hanya ya ajiye ta dalilin rokansa da ta dinga yi ya ajiyeta suka karaso falon yana rike da hannunta, da kyar ta iya bude baki ta gaishe da Abba kanta a kasa, ita kawae kunyarsa take ji, yace "ya jikin fateema," kanta a kasa tace "da sauki Abba," yace "to Allah ya sauwake, kina son komawa dakin ki ne ko xaki xauna nn gun inna sbda condition dinki" ta dago kai a hankali tana kallon Aliyu, shima kansa a kasa yake, tayi shiru ta rasa me xata ce don ita kam bata da burin cikin nn ya kara girma a jikinta, Aliyu yace "Abba da dae na tafi da ita xan fi kula da ita a can kuma ba gida ma nake barinta ba tare da ita nake xuwa clinic, nn ko xae yi min nisa kuma xan takura kaina," Abba xae yi magana inna ta fado falon, ashe tana labe tana jin duk abinda suke cewa tana huci kmr xata yi kuka tace "amma munafurcinka dayawa yake Bukar, hka muka yi da kai? To ni Rahmatu nace bbu inda yarinyar nn xata je aje a kashe min ita da abinda ke cikinta a banxa a hofi a barni da wayyo Allah, don idan an kashe su ma ni nayi hasara ba ku ba". .. Aliyu ya dan yi tsaki ya kauda kai, Abba kam shiru yyi yana ta kallon inna, ita ko ta tsaya masu kmr soja a bakin kofa, can dae Abba yace "to ki hada kayanki sae ki bi su," tayi kwafa tace "ko da naji," snn ta juya ta fice da sauri, Abba ya girgixa kai yace "tashi ka dau matarka ku tafi," Aliyu ya mike yana kallon Inteesar, ita ma ta mike tsaye suka ma Abba sallama snn suka fita, yana rike da hannunta yace "mu je mu gaida momyn ihsaan ne," tayi kmr bata ji sa ba shima bae sake ce mata komai ba har suka fita ya bude mata mota ta shiga shima ya xaga ya shiga suka kama hanyar gida, ko da suka isa tayi bacci ya fito da ita daga motar yana rike da ita kmr bby, safeena na kwance falo ta bi su da kallo ya sakar mata murmushi yace "bbyna," tayi tsaki ta dauke kanta tacigaba da kallonta, sae da ya kai Inteesar sama ya kwantar da ita snn ya sauko ya sameta, ta mike tayitsaki ta haura sama ta bar sa nn ya bita da kallo snn yyi mmrshi yabi bayanta. Washegari sae da safeena ta sa ya makara xuwa office, wanka kawae yyi ya shirya ya dauki makullin motarsa ta rakasa tanai masa shagwaba ya manna mata kiss ya ja motarsa ya bar gidan, ta sauke ajiyar xuciyan jin ddiyau dae ya manta shegiyar gaba daya, ta koma cikin gida murna fal cikinta, tana shiga daki ta fito da kullin maganin da aka basu su sa ma Inteesar a ruwan sha ta tsura ma maganin ido tana murmushi,dukiya fa knn a hannunta, ruwan fridge ta kwashe gaba daya ta bar guda biyu ta xuxxuba maganin cikisnn ta rufe fridge din ta koma sama, ta lura kasa Inteesar ke saukowa shan ruwa bbu ruwa a dakinta kuma bata ga alamar an siyo ba, tana ta kwance a daki tana jiran jin saukowar Inteesar amma shiru, ita ko tana kwance daki ta rasa inda xata sa ranta sae juye juye take ga yunwar da take ji tun safe ta gane Aliyu ya bar gidan hkn yasa ta daure ta mike ta sa ma kofar ta key, kishin ruwa duk yabi ya ishetagashi ba karfin sauka kasa, da kyar ta rarrafa ta shiga bathroom ta bude tap ta sha ruwa ta dawo tayi kwanciyarta kan tiles. Washegari ma abinda ya faru knn Aliyu bae shigo ya ga halin da take ciki ba ya bar gidan da sassafe, duk da jiya don ita ya dawoda wuri amma safeena ta gusar masa da hankalinsa ya manta me ya dawo da shi, ganin yunwa na neman yi mata lahani yasa ta dinga daurewa tana hada tea a nn dakinta da ruwan sanyita sha, shima tana sha ta amayo, duk ta kara xabgewa bata da aiki sae na kuka ita daya a daki, wani lkcn sae taji kmr ta dauki waya ta kira inna kawae sae ta fasa don bata ga amfanin kiran ba don rabuwa kawae take son yi da cikin, ita safeena bbu abinda yafi daga mata hankali irin yanda taga ruwanta na nn ajiye ba a taba ba, hkn yasa da daddare da Aliyu ya dawo ranan tace "anya kuwa kana shiga duba baiwar Allahn nn dear, gashi ita bafitowa take ba, na kan shiga na dubata wllh, amma ba ddewa nake ba kar ace xan yi mata wani abun ne" Aliyu ya mike da sauri kmr an tsikaresa yyi hanyar stairs ta bude fridge ta dauka ruwan da sauri ta bi sa tana cewa "gashi ka kai mata ruwa naga kmr jiya ruwan dakinta ya kare na fanfo take sha, ni kuma kar na kai mata ta xata wani abun ne," ya karba ya haura sama ya bude dakin ya shiga rabon da ya ganta yau kwana uku tun ranar da sukadawo daga gida, ya karaso gabanta ya durkusa yana kallonta a hankali yace "ya jikin fateema, kin daina aman," tayi tsaki ta juya abinta, ya bude fridge dinta ya ajiye mata ruwan yace "me xaki ci," tayi bnxa da shi, yyi shiru yana kallonta, ta juya cikin kuka tana kallonsa tace "wllh tllh idan baka cire min wnn shegen cikin ba...." bae jira ya karasa jin maganarta ba ya xuba mata mari, "don uwarki kika sake min maganar cire ciki sae nayi mugun saba maki kina ma da hankali kuwa, to ki je ki cire tunda ke mahaukaciya ce," ya mike a fusace ya fice daga dakin ta bisa da kallo dafe da kuncinta. Ranar bata yi bacci da daddare ba, kawae Allah Allah take gari ya waye, gari na wayewa ya shigo dakin kafin ya tafi aiki, tea me kauri ya hada mata ya ajiye matagefenta, snn ya dauko goran ruwan da safeena ta basa jiya ya ajiye mata gefenta safeena ta shigo dakin tana murmushi tayi ma Inteesar ya jiki ko kallonta inteesar bata yi ba suka fice tare da mijintata rakasa ya shiga mota ya manna mata kiss snn yaja motar ya bar gidan, safeena ta koma gidan xuciyarta fari tasa ganin goran ruwan da ta ba Aliyukusa da inteesar yau dae xa ayi ta ta kare, ta shige dakinta tana dariya. Inteesar ta mike tsaye ta dauki Hijab dinta ta saka, duk irin wahalan da take sha ko sau daya wanka bae taba wuce ta da safe ba dole sae ta daure ta shiga tayi, ta fito tana ganin jiri mai gadi ya tsaya xae mata maganar bnxa ta fixgo gate din ta fice abinta ta barsa nn tsaye, gidan Aneesah ta shiga, tana xaune tana ba shakur Indomie, tana shigowa ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi, Aneesah tace "lah daga ina hka Inteesar daxun nn nagama xancenki a xuciyata wllh" Inteesar xata yi magana taji yawu bakin ta mike da kyar taje bathroom ta xubar Aneesah tace "A'aah kice oga yyi aiki" . Inteesar ta harare Aneesah snn tayi tsaki tace "ni don Allah taimako naxo kiyi min Aneesah," Aneesah tayi dariya tace "to kawas ina jinki amma cikin nn na baki wahala gskya, kinga yanda kika rame kuwa," Inteesar ta dawo kasa kusa da ita tace "don Allah don Annabi Aneesah kinsan inda ake abortion?" Aneesah tayo waje da ido da mamaki tana kallonta snn tace "kina da hankali kuwa inteesar," inteesar ta jinginar da kanta jikin kujera hawaye ya cika idonta, Aneesah tace "kinyi shiru," inteesar ta share hawayen idonta tace "wllh xubar da cikin nn xanyi kin dae ji na rantse in ma xaki gaya min ki gaya min," Aneesah ta gyada kai tace "to tashi ki fita a gidana, ni bana hulda da maras tsoran Allah," inteesar ta juya tana kallonta tayi shiru snn ta mike tayi hanyar fita daga gidan, Aneesah