← Book details Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rasa inda xata sa kanta don murna, tace "da gske bbyna, wllh sae ka biya ni," yyi hanyar stairs da ita yana cewa "naji xan biya bby nawa ne," inteesar kam na xaune ta jinginar da kanta jikin gado, ji take kmr ba ita ba duk ta rasa inda xata sa ranta taji ddi, ga alluran hana aman da yyi mata duk ya bi ya dameta, tana neman yin aman ma ko xata samu sauki amma ta kasa, yunwa take ji ssae amma bbu abinda ke ranta, ko wani abinci ta tuna sae taji amai na taso mata jikinta yyi mugun xafi ga kishin ruwa da take ji kuma tana tsoron shan ruwa, ta sauko kasa da kyar ta kwanta kan tiles din dakin ko xata ji ddin ranta, kasa daure kishin tayi ta mike xaune tana mayar da numfashi ta rarrafa ta bude fridge dinta taga ba ruwa ciki sae lemo, tana daddafa bango ta fita daga dakin ta sauka kasa da kyar ta bude fridge ta dauki ruwa ta sha, snn ta koma sama, dae dae kofar dakinta taji amai frm no where ta xube wajen ta shiga kwarara aman kmr ranta xae fita, suna daki shi da safeena duk ta gama rikitar da shi, ya turata da karfi ya mike tsaye ya karasa kofa ya bude ya fita safeena ta bi bayansa da sauri, durkusawa yyi gabanta yana kallonta, ta fashe masa da kuka abun tausayi ta xube jikinsa muryarta na rawa tace "don Allah ya Aliyu ka kai ni gida, ni wllh na gaji ko ina ciwo yake min wayyoo mutuwa xanyi," ya rungumeta cike da tausayi xae yi magana safeena tace "dear," ya juya da sauri yana kallonta, kallonsa kawae ta tsaya yi bata ce komai ba, ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Inteesar yace "ke kuma mahaukaciyar wace gari ce xakiyi ma mutane amai a nn, idan kina jin amai ba sae ki shiga bathroom din ki ba, wnn ae kaxanta ce," Inteesar ta daga kanta tana kallonsa, da kyar ta shiga kkrin mikewa daga inda take wani aman ya taso mata ta shiga kwarara sa a wajen, kuka ssae ta fashe da ta jingina jikin bango tace "wayyoo Abbana," kallonta kawae ya tsaya yi ya kasa cewa komai, ta rarrafa ta shiga dakinta ta xube kan tile tana mayar da numfashi, safeena da sae kallon inteesar take da mugun mamaki lkci daya jikinta yyi sanyi ta ma rasa tunanin da xata yi, a xuciyarta tana cewa amae kuma? to me hkn ke nufi, ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Aliyu tace "me ke damunta???? . Aliyu ya mike tsaye yana kallon safeena yace "bata jin ddi ne," bae jira me xata ce ba ya bude dakinsa ya shiga sae ga shi ya fito da mop ya gyara wajen aman, safeena ta koma daki da sauri hannunta na rawa ta shiga kiran uwarta, tana dagawa tace "momy wlh ina ga fa kmr cikine da yarinyar nn," uwar ta mike daga xaunen da take da sauri tace "mene? Ke wa ya gaya maki," a rude safeena tace "gashi nn tana ta amai," uwar tayi salati tace "bari xan kiraki," ta katse kiran. Da daddare Inteesar na kwance kan tiles ya shigo dakin ya durkusa gabanta yana kallonta yace "tashi ki sha kunu na karbo maki a gida," ta kasa dagowa ya dagota yana kallonta ya kauda kansa da sauri, ya kai mata kofin baki, ta kauda kai da sauri muryarta na rawa tace "xafi," ya girgixa mata kai yace "ba xafi," ta maido da kan jikinta na rawa ta daura hannunta kan kofin taji ba xafi ta kai bakinta yana rike da kofin ya shiga bata, da sauri ta cire bakinta tace "baxan yi amai ba? ya gyada mata kai ya ci gaba da bata, yunwa take ji ssae don hka rabi tasha ta koma tayi kwanciyarta kan tiles, yace "kin koshi ne ta gyada masa kai tace ruwa xan sha, yace "aa baxa ki sha ba," bata ce komai ba ya dago ta mayar kan gadon duk abinda suke safeena na lekensu, ta koma da sauri daki har da hawayenta ta kira uwarta tace "kai ni momy wllh na gaji, gashi can wajenta yana lallabata yana bata koko," uwar tace "yi shiru safeena, daxun nn na dawo daga wurin mutumin, ca yyi wae duk abinda xa muyi masa a kantabaxae taba tasiri ba sbda yana mugun son cikin nn dake jikinta," safeena ta dafe kirji tace "ynxu ciki ne da ita da gske ina xaune momy," uwar tace "ki tsaya ki saurareni mana," safeena na share hawaye tace "to ina ji momy," uwar tace "yauwa, to ynxu ca yyi dole sae an lalata cikin in har muna son muga aiki yyi mugun tasiri a kansa, ynxun ma ba wae bae yi tasiri bane, don xae dinga lallaba ki kuma sae abinda kika ce masa xe yi, sae dae fa hankalinsa gaba daya na gunta sbda wnn shegen cikin, kuma fa baki isa ki hanasa xuwa gunta ba amma, don hka kawae ki kwantar da hankalinki jibi ki xo mu koma kauyen yace yana jiranmu, ciki kuma kmr ya bare ne," safeena ta share hawayenta xuciyarta fal murna tace "to ngdd momyna," ta katse kiran tana murmushin mugunta. Da safe Aliyu ya bae ma safeena i.v din bikin Zainab, ta tabe baki tana hararansa tace "to ca nayi maka ban sani bane," yyi shiru yana kallonta snn yyi murmushi yace "to Allah ya baki hkuri bbyna, amma ni dae ban san me nayi maki ba kika canxa min kwana biyu," ya mike ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa gashinta yace "haba yan matana," ta hararesa tare da buga masa hannu tace "ni ka rabu dani," ya rungumeta yace "haba bbyna," kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne ba baka ma damu dani da lamarina ba a gidan ba," yace "inji wa yace maki hka," kakarin Aman inteesar yaji, ya saketa da sauri ya mike tsaye ya fice daga dakin, safeena ta bi sa da kallo xuciyarta na mugun kuna, kasan dakin ya tarar da ita tana ta amai ya kamata har ta gama snn ya gyara mata jikin ya gyara dakin ya kwantar da ita kan gado, ta rikesa muryarta na rawa tace "sanyi nake ji yaya," ya lulluba mata bargo snn ya dauki I.v din da ya ajiye gaban madubinta xae fita ya juya yaga kallonsa take, ya dawo yana kallonta yyi murmushi yace "kina san wani abu ne," ta girgixa masa kai yace "kinsan bikin Zainab saura kwana goma ko," ta mike xaune da sauri tace "da gske yaya, ni ba a gaya min ba to," ya kamo hannunta yace "ae sun san baki da lfya, ki bari nxt wk sae mu tafi gidan kafin nn jikinki ya kara kwari," ta marairaice kmr xata yi kuka tace "to ba kila xuwa tayi ranan ta gaya min ba ka koreta," yace "ba ta ji ne," tace "to yaya wa xata aura" yana kallonta yace "faruuq," ta wara idonta ta fada kansa cikin jin ddi tace "don Allah da gske yaya, kai amma naji ddi wllh, ka bani nmbr ya faruuq din" yace "to anjima xan baki, xanje gida ynxu me xan ce inna ta girka maki?" tayi shiru sae kuma ta bata rae ita da ba ma son cikin take ba, yace kinyi shiru, tana hararansa tace "kace mata ina da ciki ne," ya daga hannayensa da sauri yace "A'a" yana girgixa kai, ta koma ta kwanta tace "dan wake nake so ni," yace "to, sae na dawo, kar ki sha ruwa kar amai ya takuraki," bata ce masa komai ba yayi hanyar kofa, duk wnn abinda suke safeena na labe tana jinsu, tana jin xae fito ta bar wajen da sauri ta shige dakinta tana murmushin mugunta, yana fitowa ya shiga dakin safeenar . Bayan kwana biyu safeena ta samu ta lallaba Aliyu wae xata gun wata yar uwarta, ya ko barta har da bata kudi da makullin mota dayake ta iya drivin tana ta murna a xuciyarta tana cewa lallai sae yanda tayi da Aliyu, ynxu kam ta yrda yana tafin hannunta amma dae ba duka ba, tunda bata isa ta hanasa xuwa gun Inteesar ba, amma komai ya kusan xuwa karshe, ta fada a fili tana murmushi, cikin kwanakin nn Aliyu na da aiki ssae a clinic don hka ya gwammace da ya bar Inteesar kadae a gida gwara ya dinga tafiya da ita don tana bukatar kulawa ssae, hka ko ya dinga yi kullum shi xae shiryata da safe yyi ma safeena sallama su wuce asibiti, hkn yyi mugun tada ma safeena hankali to ta ya xa'a yi ta aikata abinda suka sha wahala kafin su samu bayan baya barinta a gida., ita kam Inteesar ko kadan abinda Aliyu ke mata baya burgeta don dai dae da second daya bata son cikin jikinta, kuma tasan sbda cikin yake mata hka, wani mugun tashin hankali ke xuwa mata idan ta tuna cikin Aliyu ne jikinta, Ana saura kwana uku bikin Zainab ya kai ta gida duk da ba a son ranta ba don bata son su san tana da ciki, amma ashe duk ya gaya masu uwarsa ce kadae be gaya ma ba sae umma, inna duk ta rikice masa wae cutar jikarta kawae yake gashi duk ta fige ba kyan gani, shi dae bae tanka ma inna ba ya fice, Inteesar dae na kwance falo sae mayar da numfashi take don da kyar ta iya karasowa cikin gidan bayan sun sauka daga mota, kuma da asibiti ne baya barinta ta taka da kanshi yake daukarta su shiga ciki, inna tace "to wae wani irin jarababben cikine wnn dake neman kashe min ke," ta mike xaune tana hararan inna kmr xata yi kuka tace "wae ni nace maki ciki gareni ne," bata jira me inna xata ce ba ta shiga daki tayi kwanciyarta, inna duk ta daga hankalinta ganin irin laulayin da Inteesar take mai tsanani, bbu wanda bae san ciki ne da ita ba a gidan, ko da yaushe cikin amai da kasala take, ko maganan kirki bata son yi sae in Aliyu na yasa ta gaba ko yana tambayarta me take so, duk tausayinta
Chapter 21 · 0% Book details