Sashe 19
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyu ya shigo dakin da sauri ya karaso bakin kofar bayin yana kallonta, har lkcn amai take ssae gashi bbu komai cikinta, ya durkusa gabanta a hankali ya dafa ta yana mata sannu, buge masa hannunsa tayi, tayi xaman dirshan a bakin kofar tana mayar da numfashi ta fashe da kuka ta jingina jikin bango duk ta rasa inda xata sa kanta, juye juyeta shiga yi a bakin kofar tana kuka tana kiran Abbanta, ya fixgota ya daka mata tsawa "kina hauka ne," ko kallonsa bata yi ba ta rarrafa jikin gado ta xauna ta jinginar da kanta tana ci gaba da kuka tana mayar da numfashi, ya mike ya dawo kusa da ita yana kallonta ya dafa ta xae yi magana ta mike da sauri ta koma bayin ta durkushe ta shiga kwararo wani aman kmr xata shide har wani rawa jikinta yake, lkci daya jikinta ya dau xafi, ya riketa yana mata sannu, ta langwabe masa ta fada kansa sae kiran Abba take tana mayar da numfashi, ta fara kkrin mikewa ya rikota yace "ina xa ki," tana girgixa masa kai ta kuma fadawa kansa tace "wayyo kwanciya xanyi na gaji," ya dago ta ya shiga da ita bayin ya wanke mata baki ya dauketa ya maidota cikin dakin ya kwantar kan gado ya rufa mata bargo yana kallonta sae rawan sanyi take, ya koma ya gyara bathroom din, snn ya dawo gefenta ya xauna yana kallonta duk ya ma rasa wani tunani xae yi, ya jinginar da kansa jikin bango a hankali ya lumshe idonsa "no! Wnn me shegen rakin baxata iya rainon ciki ba ynxu, nd bae tashi haihuwa da ita ba tukun, da ma safeena ce wnn kam takuran da yake samu a gida a kanta xae kara yawa ne ma, to ma wani moranta yyi har xata dauki ciki ynxu" yyi tsaki ya bude ido yana kallonta bacci take amma da gani ba me ddi ba sae juye juye take, ya girgixa kai ya mike ya fice daga dakin, makullin motarsa ya dauka ya sauko falo, safeena da ta fito daga kitchen knn bayan ta kashe gas din da Inteesar ta kunna tace "me ya sameta Dear," ya galla mata harara yace "ban sani ba," ya fice, ta bi sa da kallo, ita kam halin Aliyu ya isheta a gidan nn, gashi sae bata kudinsu suke a banxa a kansa, amma abu sae kara gaba yake, tayi kwafa ta haura sama, yana shiga motarsa ya kama hanyar asibiti, bae damu da gaisuwan da nurses ke masa ba har ma da patients ya haura sama kawae ya wuce office dinsa, ya bude glass din da magunguna suke ya shiga xaban wanda ya kawosa, tabs kala biyu ya dauka da ruwan allura daya ya rufe glass din ya fito ya rufe office din, ya sauko kasa xuwa reception, sae a snn ya shiga amsa gaisuwan patients din da ke gaishesa, yyi murmushi ganin matar da yyi ma theatre kwanakin baya da yaranta da babansu, ya karasa kusa dasu yana kallonsu yace "madam me ya sami twins" matartace "wllh tari suke doctor, ya aiki?," ya karbi dayan yana masa wasa yace "aiki Alhmdllh anyi attend din maku ne," tace "A'a ynxu dae xa a duba mu, madam fa," yyi murmushi yace "tana lfya," tace "to a gaida min ita, yau kana wkend ko," yace "wllh kuwa, Allah ya sauwake, i wil b on my way," ya ba mijinta hannu suka yi sllma snn ya juya, yana isa kofar fita sai da ya juya ya sake kallon kyawawan yan biyun da suka girma ssae, ya dauke kansa da sauri ya fice ya shiga motarsa ya bar asibitin. . Aliyu na shiga gida ya tarda Safeena kwance a falo tana kallo, ta bisa da kallo har ya haura sama snn ta mike xaune tana bubbuga kafa a hankali ta shiga maganar xuci "lallai its high tym she wake up frm her slumber, ya kamata ta tashi tsaye daga xaunen da take ynxu, Aliyu ya gama kawota bango, xata cire sonsa ta ajiye gefe guda tayi abinda uwarta ta dde tana son tayi taki yi sbda so ya rufe mata ido, ita kuma inteesar ynxu suka sa kafar wando da ya da ita" tayi murmushin mugunta ta mike ta haura sama xuciyarta na tafarfasa. Aliyu na shiga dakin ya tarda ta tana bacci ya xauna gefenta yana kallonta ya ciro magunguna da alluran da ya dauko a asibiti yana kallonsu, snn ya juya yana kallonta tayi wani irin haske ta kuma kara kyau, yyi murmushi ya shafi gefen fuskarta ya mike ya dauko syringe a dakinsa ya dawo ya shiga hada alluran, sunansa yaji ta kira, ya juya da sauri yana kallonta ta sake maimaitawa "ya Aliyu," sae kuma yaga tayi murmushi ta juya, ya ajiye alluran hannunsa ya dawo dab da ita ya xauna yana shafa labbanta da yatsa yace "fateema," cikin baccin ta amsa "na'am," yyi murmushi ya daura mata kiss a bakinta, murmushin yaga ita ma tayi, yyi still yana kallonta, to wae meyasa yake son xubar da cikin nn, shi dae yana son yara kuma xae so yaga kyakkyawan bbyn da xata haifa masa mai kama da ita, ya dauke kansa ya daura hannu a goshinsa kan na juya masa, y? Meyasa yake son xubar da bbynsa gudan jininsa, ya girgixa kai yace "No," da sauri yaga ta mike xaune ya kamo ta ta fara turasa xata sauka yaki sakinta yana tambayarta mene, amai ta shiga kwarara masa a jiki yana rike da ita har lkcn, sae da ta gama snn ya dauketa ya shiga da ita bayi, sae kuka take tana cewa ita ya kaita gida, wanka yyi mata ya nannadeta cikin towel ya fito da ita ya cire xanin gadon snn ya kwantar da ita, shima wankan yyi don duk ta bata masa jiki ya saka xanin gadon cikin washn machine da shirt din jikinsa snn ya fito daure da towel, ranar ce rana ta farko da ta taba ganinsa daure da towel don ko singlet Aliyu bae yrda ta gansa da shi bare short nicker, ta rufe idonta da sauri, shima bae ce mata komai ba ya kwashi magunguna da alluran da ya hada ya fita da su, dai dai lkcn da Safeena ta fito daga dakinta, ta bi sa da kallon mmki shi kam ko kallonta bae yi ba shiga dakinsa. Alluran da yyi mata bayan ya tilasta ta sha tea ne ya tsayar mata da aman, amma duk da hka sae da ta gwammace dama aman ta dinga yi taji ddi, don rasa inda xata sa ranta tayi sae kuka take tana juye juye, ya rungumota cike da tausayinta yana lallabata tayi bacci, da kyar ta samu baccin ya dauketa, yyi shiru yana kallonta duk ta rame lkci daya, da yamma wajajen karfe biyar ya fita pharmacy siyo mata magunguna da drips din da xae sa mata.Yana fita ko minti goma ba ayi ba Zainab ta shigo gidan ko kallon safeena dake ta busar da gashinta da hand dryer bata yi ba ta wuce sama, safeena ta bi ta da kallo snn ta ja dogon tsaki, bacci ta tarar Inteesar ke yi ta shiga tashinta da xolaya tana cewa "ke kasa kinyi bakuwa maxa tashi" inteesar ta shiga juye juye ta mike xaune da kyar tana kallon Zainab, Zainab tace "hmm lbri na xo maki da mai ban kunya," inteesar xata yi magana taji yawu cike bakinta, ta mike tsaye da kyar ta shiga bayi ta xubar da yawun ta dauraye bakinta da freshner ta dawo, Zainab tace "meye hka," Inteesar ta langwabe da kyar tace "bana jin ddi ne," Zainab ta bude baki "iyye kar dae bby xa a samo mana," inteesar tayi shiru da mamaki tana kallonta snn tace "bby kuma, wani bby," Zainab tayi dariya tace "lalala kinga yanda kka yi wani irin haske da kyau kuwa, shknn xa a sama ma yayana bby," inteesar ta hade rae xata yi magana taji yawu kuma a bakinta ta mike da sauri taje ta tofar wnn wani irin jaraba ce, ta tambayi kanta, kuka ta fashe ma Zainab ganin Zainab ta kuke sae murna take xa su samu bby, tace "ni fa bana son hka Zainab wllh bani da komai," Zainab tace "ki daina wllh, ga signs a jikinki," kuka ssae take tana cewa na shiga uku ni Zainab ki bari bani da komai yarinya da ni xaki ce ina da ciki, Zainab tayi dariya ssae tace "tunda ko kina kwana daki daya da yayana ai ke ba yarinya bace," dai dai nn Aliyu ya shigo yana ma Zainab mugun kallo yace "ke wae wace irin mutum ce, ban hanaki shigowa gidana ba, xo ki fita," cikin daga murya ya karasa maganar ta mike da sauri tana xumburo baki ta dauki mayafinta ta bi ta gefensa ta fice ya kai mata rankwashi, inteesar ta hade kanta da gwiwa tana kuka, ynxu ciki ne da ita yar yarinya da ita, to da wani ido ma xata kalli su inna, ae Allah ma ya kyauta kuma ya rabata da haihuwa ynxu kuma ma wae dan Aliyu. Ta mike da sauri tun kan ya shigo dakin xata yi hanyar bathroom jiri ya debeta ya shigo dakin da sauri ya kamota ta fada kansa suka xube kan gado, ya fada gefenta da sauri ganin ynda take mayar da numfashi ya dagota ya rungumeta yana mata sannu, cikin kuka tace "wllh ka cire min cikin nn bana so," ya toshe bakinta da sauri yana kallon cikin idonta yace "ni ina son abu na . Kuka ssae Inteesar ta shiga rera masa, shi kam saekallonta yake yana murmushi, ta fara kkrin mikewa xata sauka daga kan gadon ya riketa da sauri yace "ina xaki," cikin kuka tace "wllh sae ka cire min cikin nn bana so," ya rufe bakinta ya hade rae yace "kar ki sake cewa na cire maki bbyna, sae kace wani kaya," ta buge masa hannu, ya harde kafarsa cikin nata tayi yar kara, ya rungumota yana kallonta ya shiga shafa mata cikinta yace "me xaki ci, dubi fa yanda kika rame tun kan ba mu je ko ina ba, a hka xa muyi rainon cikin kika san ma ko yan biyu ne