Sashe 13
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
dinsu da Inteesar, da yanayin da ya shiga da har yau bae ji hkn gun Safeena ba, darajar da Inteesar ke ci kadae a gunsa knn banda hka da bata isa ta taka masa matarsa da yake ji da ba, Safeena kanta na mamakin yanda Aliyu ke share Inteesar duk da iskancin da take xuba masa, ita bbu abinda yafi daga mata hankali ma irin mugun rainata da Inteesar tayi, amma tasan duk Aliyu ne ya ja mata tunda ga irin tonan asirin da yyi mata washegarin ranar da aka kawo ta gidan, wani lkcn takan yi murmshin takaici tace nasan tanadin da nayi maki yarinya kiyi yanda kike so lkcn ki ne ynxu. Ranar da ya kaita tayi registratn din jamb can ya barota ya bata kudin mota ya wuce office, bata bari adai daita sahun ya shigo da ita layinsu ba ta sauka ta basa kudin don yau tana son ta kare ma anguwar kallo tunda dae ba fita take ba, tana isa bakin gate dinsu taga wata yarinya da baxata wuce ta ba rike da wani kyakkyawan yaro a hannunta tana waya, Inteesar ta dauke kanta ganin sun hada ido, yarinyar tace "sannu fa," inteesar tace "yauwa, ngdd," ta danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga, taji yarinyar ta burgeta yar kyakkyawa da ita, safeena na kwance a falo da kawayenta ta wucesu tana yatsine fuska ta haura sama, bayan kwana biyu Aliyu ya hadata da driver taje ganin centre dinta, tana dawowa ta sake haduwa da yarinyar a bakin titi ita ma xata karasa layin da kafa tana rike da danta, bayan sun gaisa Yarinyar tace "amma aure kike a gdan nn ko," Inteesar tayi murmushi tace "eh," yarinayr tace "to ya sunanki," inteesar ta gaya mata yarinyar tace "ni kuma sunana Aneesah," Inteesar tayi murmushi tace "to yaron ki fa," yarinyar tace "sunansa Abdush-shakur," Inteesar ta karbi yaron tana murmushi tace "fyn shakur," har suka isa dai dae gidajensu, yarinyar tace "kina da kyau ssae, ina son mu xama kawaye," inteesar tayi dariya tace "to ai kema kina da kyau," Aneesah ta bata wayanta tace "sa min nmbrki to inteesar," Inteesar tace "wllh wayan mijina ne a hannu na ki bari idan na samu waya," Aneesah tace "to mu shiga kiga gidana mana" inteesar ta xaro ido tace "mai gidanki baya nn," Aneesah tace "A'a a Abuja yake aiki sae wkend yake dawo wa," inteesar ta bi ta suka shiga gidanta, gidane babba kmr nasu bbu abinda ya xama bakonta a gidan don duk suna da shi a nasu gidan, har bedroom ta shiga da Inteesar, inteesar ta shantake suka dinga hira kmr da can sun san juna, ta girka masu abinci ta kawo masu dakin suka ci suna ta hira tana ba Inteesar labarae kala kala, Inteesar taji kmr kar ta bar gidan, karfe shidda saura ta rako Inteesar har bakin gate kmr kar su rabu, har shakur ya saba da Inteesar don har da kukansa, wae sae da ta isa jikin gate tukunna gabanta ya shiga faduwa a xuciyarta tace "Allah yasa ya Aliyu bae dawo ba," mai gadi ya bude mata gate ta shiga taga motarsa a parke a garage xuciyarta yyi mugun bugawa da kyar tana jan kafa ta shiga gidan.