Sashe 10
Inteesar Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
safe ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba yana murmushi ya gyada mata kai kawae, ta mike xata bar dakin ya kamo hannunta yace "ina xa ki," ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba, ya saketa ta fita, falo ta sauka ta shiga mrnin duties dinta, ba ita ta koma sama ba sae kusan karfe tara,ta tarda shi kwance yana bacci, wanka ta shiga ta fito ta gama shirinta ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ba kanta wahalan hada breakfst ba don bae taba cin girkinta ba, tayi kwanciyarta a falon don neman yunwa tayi ta rasa, karfe sha daya taji mai gadi ya bude gate ta mike ta isa jikin kofa taga ko waye ya shigo, motoci biyu ne suka shigo gidan abokanansa kusan su biyar suka fito, da yake kofar a bude yake komawa kawae tayi ta kwanta, suka shigo gidan da sallamarsu duk suna sanye da fararen shaddodi, ta kara volume din Tv ta mayar da hankalinta kan TV, tsokanarta suka shiga yi suna dariya "uwar gida ke kika rike ango har ynxu yaki fitowa kuma kika sa ya kashe wayoyo ko to ayi hakuri a sakar mana shi muje gun daurin aure," bbu yabo bare fallasa tace "ku dae tambayesa wanda ya rikesa," ta mike fuskarta a daure ta haura sama ta bar su nn falo, a step duka hadu da Aliyu ya galla mata harara, don me baki tashe ni ba, ita ma ta galla masa hararan tace "sbda baka isa ba," tayi gaba ta bar sa nn tsaye, ya sauko suna ta tsokanarsa wae tsoron uwargida yasa ya makara, dole suka jirasa yyi wanka snn ya fito shima sanye da farar shaddar, ba karamin kyau yyi ba don ko hmm bari dae, ya shiga dakin Inteesar tana xaune gaban madubi, kallo daya tayi masa ta madubin ta dauke kanta yace "kinyi break," tayi bnxa da shi, ya daga kafada yace "sae na dawo kiyi mani adduar Allah yasa ayi a sa'a," ya juya xae bar dakin ta fashe da kuka ba tare da ta shirya ba, ya juyo yana kallonta, ya karaso cikin dakin yace "an maki wani abu ne ko kawae jin ddin kukan ne ke damunki," bata tanka sa ba, ya tabe baki ya juya ya fita, suka fita gaba daya da abokan nasa suna masa mitan ya bata lkci dayawa ko mantawa yyi yau ce ranar daurin aurensa da sahibarsa shi dae bae ce masu komai ba har suka shiga mota suka bar gidan, suna fita daga gate yace "kun san wani abu ku je kawae gani nn xuwa, ina son na kai fateema can gida daga can sae na wuce," namesake dinsa yace "wae meye hka kke yi ita bata san hanyar gidan ba sae an kaita baka ganin saura yan mintoci," Aliyu yace "ni dae kuje kawae ina nn xuwa, ya bude motar ya koma cikin gidan," suka yi tsaki kusan gaba dayansu suka yi gaba, yanda ya barta hka ya dawo ya tarar da ita, ya dauki hijab dinta ya mika mata yace "tashi to na kai ki gida," bata yi musu ba ta mike ta karbi hijab din tasa takalminta suka fita, motarsa ya fito da ta bude sit din baya ta shiga, bai ce mata komai ba ya ja motar suka bar gidan, suna isa gida bata jira ya gama parkin ba ta bude mota ta fice, ya dakatar da ita da sauri ko kallonsa bata yi ba ta shige gidan da gudu sae sashin inna, hkn yyi mugun bata masa rae kuma yasan da mutane cikin gidan shi yasa bae bi ta ba, ya ja motar kawae yyi gun daurin aure, mutanen dake tsakar gidan har da su Hajiya suka bi ta da kallo murna fal cikinsu, umma ko ta dinga tuntsira dariya tana guda kawayen Hajiya na taya ta. ta xube jikin inna ta fashe mata da kuka, a rude inna ta shiga tambayarta "meye faru, ke da waye," ta kasa cewa komai, inna ma ta bare baki ta fashe da kukan, Anty Nafeesa ta fito daga daki da sauri tana kallon Inteesar tace "wa ya kawoki," inteesar tayi kkrin tsayar da kukanta tace "shi ya kawo ni," Nafeesa tace "ynxu kuwa muke shirin tafiya can gidan, kukan meye hka kike yi, ke dae baki ji ddi ba wllh," a fusace cikin kuka inna tace "ban son iskanci ke uwar wa yyi maki kishiya," inna ta mike ta daga inteesar tana share hawayenta suka shiga daki tana cewa "ki rabu da shi, bbu abinda xaki koma gidan nn kiyi, kuma bbu uban da ya isa yace ki koma tunda nace baxa ki ba, ina nn ina jiransa daga shi har ubansa," Anty Nafeesa tayi murumushi ta bi su cikin dakin. Gida ya cika fal da yan uwan su Hajiya da umma da abokanan arxiki ana ta shagalin biki har da su Dj a gidan, inna na daki xaune gefen Inteesar da ta kwanta tana bacci tana mata fiffita ita ma tana gyan gyadi, jin kide kide yasa inna ta farka ta fito da gudu har Anty Nafeesa da wa inda ke falonta suka tsorata suka dinga tambayar lfya, ko kallonsu bata yi ba ta fita xuwa tsakar gida da gudu, Anty Nafeesa ta ma xaci abu ne ya sami Inteesar suka shiga dakin da sauri suka tarar baccinta take, wasu kuma suka bi inna da sauri a baya suna tambayar wae Hajiya mai ya faru, inna na isa tsakar gidan cikin daga murya tace "nashiga uku uban wa ya gayyato wa innan shaidanun gidan nn" ta fadi hkn a fusace tana nuna masu Dj da kayan kide kiden nasu, aka kashe wakar dake tashi, Umma tace "to naga dae yau ranar farin ciki ne inna kuma dae daga yau ba sake ganinsu xa ayi ba," inna tace "kin ci ubanki mai dattin hula, kaji min rubabbiyar yarinya," ta karasa kusa da masu dj tana huci ta shiga bubbuga speakers din tana cewa "ku fitar min dasu kar na babbake su, gidan da na ba gidan yan iska da shaidanu bane" ba shiri Hajiya tasa aka shiga kwashe su a barrow ana fita dasu, hka ma canopies din duk sae da tasa suka fita dasu tana jaraba an cika gidan dan'ta da tarkace, hka mutane suka dinga kallon inna wasu na dariya can ciki ciki, "kuma duk shegen da ya xauna kusa da flawowin da na ban yafe masa ba duniya da lahira tunda dae ba shi ya dasa masa ba, ko tsinke kuma kar a wurgar a tsakar gidan nn," ta fadi tana huci kmr kirjinta xae fashe, Hajiya dae shigewa daki tayi kunya kmr ta nutse, wae juyawar da inna xata yi sae ganin momy tayi xaune suna hada salad, ta saka salati kmr xata yi kuka tace "Allah ya wadaranki Zainabu, ynxu uban me ya kawo ki cikinsu idan ba shisshigi da neman suna ba, ca suka yi maki yi suke dake mara xuciya kawae wahalalliya, ni dama nasan tun ba yau ba kika tsani yarinyar nn kike son ganin karshenta, idan ba hka ba taya xaki kwaso kafafuwa ki taho nn cikinsu, wllh daga yau kar ki sake nuna kin san Inteesar, ita ma bata sanki ba wllh, shi yasa ma da ta xo daxu bata nufi inda kike ba dan tasan ba sonta kike ba" ta karashe maganar da kuka ssae har da tari, ta bar wajen tana cewa "kuma yau bbu ubanda ya isa ya bar min tsakar gidan da' na hka, duk sae an wanke shi an goge wllh," dariya wasu har da xubewa kasa, ranar dae a dari dari su Hajiya suka yi shagalin bikinsu, jefi jefi inna kan fito taga ko an xauna kusa da flowern da tace kar a xauna, bbu wanda yyi gigin xama kuwa. Da Magrib bayan kowa ya watse inna ta tasa su Hajiya gaba sae da suka wanke tsakar gidan su Zainab da kursum da Maryam din Anty Nafeesa dariya kmr cikinsu xae fashe, dama momy tun daxu ta shiga ciki amma sae da inna taje ta fito da ita wae har da ita yar bakin ciki maxa su gyara ma dan ta tsakar gidansa, sae da taga sun kusa gamawa snn ta koma sashinta tana cewa "wahalallun bnxa kawae" karfe takwas abba yyi kiran Inteesar falonsa, ta karasa falon a sanyaye tayi sallama ta shiga, Zaune ta tarda Aliyu a falon yana sanye da shadda brown colour, ta nemi gefe ta xauna tana kallon Abba tace "ina yini Abba," Abba ya amsa yana kallonta yace "ya gidan," ta sunkuyar da kai tace "lfya Abba," Abba ya nisa yace "ranar da nace ku taho da Zainab don me kika ki bin ta," ta daga kai tana kallon Aliyu dake kallonta, Abba ya gyada kai yace "to yyi kyau, kuma har ynxu baki fara karatun ba ko?" a hankali tace "Abba na kusan farawa," Abba yyi shiru yana kallonta snn yace "to Allah yasa, ki tashi ki bi mijinki, a cigaba da hakuri, Allah yyi maku albarka" Aliyu ya mike yana kallon Abba yace "nagode Abba," ko kallonsa Abba bae yi ba, Inteesar ta yi shiru kmr xata yi kuka tace "Abba inna tace ba ynxu......." Abba ya hade rae yace "inna tace me, tashi maxa ki koma dakin ki, kuma bance ki shiga cikin gida ba," bata san tayi mugun ba Abba haushi ranar da ya aika Zainab kiranta taki xuwa ba, a sanyaye Hawaye na kkrin sauko mata ta mike tace "Abba sae da safe," yace "Allah ya tashe mu lfya," Aliyu ma yyi masa sai da safe ya bi bayanta suka bar falon . .. Suna fita Aliyu ya kamo hannun Inteesar da sauri ganin bata son jerawa da shi, ta juya tana kallonsa yace "mu fara shiga na gaida momynki," tayi masa mugun kallo tace "ae ko baka fada ba dama momyta ce bance taka ba," bai ce mata komai ba yana rike da hannunta suka isa sashinsu, shi yyi sallama ganin tsaya kawae tayi ta rike kugu, duk da ita yaso tayi sallamar, Ihsaan ce ta amsa ya shiga falon tana biye da shi a baya, suna hada ido da momy ya kauda kai da sauri ya nemi kujera ya xauna, ita