Sashe 9
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH
[11:21am, 24/01/2016] Haneefah :
GIMBIYA NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Kallonta yayi sannan ya d’aura ‘kafarshi d’aya
kan d’aya akan centre table da ke parlourn.
Nabilah azuciyarta tace “Wannan anyi d’an
rainin wayo,baya magana sai kace bakinshi
yana ciwo”,ashe dai maganar da tayi da
zuciyarta ya fito fili,wani kallon da ya watsa
mata yasa ta sha jinin jikinta,sai wani shan
‘kamshi yakeyi,da kyar ya bud’e baki yace “Ya
da tsayamin akai?,ki d’auki leather bag d’in kiyi
waje”. Ajiye leather din tayi a ‘kasa,cike da
tsiwa tace “Meh zanyi da shi neh wai?kace
nawa,yanzu kuma ina neman ‘karin bayani
amma ka tsaya sai wani hahhad’amin fuska
kakeyi”.
Cike da mamaki ya maida dubanshi zuwa
gareta,har zaiyi magana sai kuma ya
fasa,d’aukar wayarshi yayi ya ‘kira Amirah. Ran
Nabila yayi mugun ‘baci,afusace ta juya zata
bar d’akin,har ta kai ‘kofa sai ya dakatar da ita
yace “Umm zo ki d’auki kayan”,ba tare da ta
juyo ba tace “Banaso,nagode”,ajiyar zuciya yayi
sannan ya d’aga kafad’a alamun wannan kuma
ya rage naki sannan yace “Okay ki d’auka kije ki
kyautar amma dai karki kuskura ki bar min
leather’n nan a d’akina”. Sanin halinshi yasa ta
juyo ta d’auki leather din tana tuttura
baki,Sultee kam bai ma san lokacin da dariya ya
kubce mishi ba. Cike da mamaki da tsoro Nabila
take kallonshi,tunani takeyi “Kai!!lafiyar ya
Sultee kuwa?daman yana dariya har haka?ko
dai hauka yayi?ko yasha wani abu da ya ta’ba
mishi brain?” ta sa’ka wannan ta kunce haka ta
dinga yi.
Ganin ta tsaya kallonshi baki bud’e yasa yayi
shiru,nan take ya ‘kara had’e fuskar nan kaman
ba shi bane ya gama dariyar mahaukata yanzu.
Kallonta yayi yace “Malama ya kike kallona
haka?ko kina sona neh in taimaka miki?”. Zaro
ido tayi,mamakin kalaman shi takeyi,sai girgiza
kai takeyi,da ‘kyar ta iya furta “Ni??a’a,meh
zanyi da mutumin da yakusa haifana ko ma
ince ya haifen?ni banida ra’ayin auren sugar
daddy balle ka nemi gayamin magana”.
Murmushi yayi yace “Jeki”,murgud’a mishi baki
tayi ta tattara leather din tayi hanyar d’akinsu
Hanee da maman Khalil
[1:25pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Tana shiga d’aki baba Rabi da ke kwance ta
tashi ta zauna,cike da tambayoyi ta ke kallonta
sai chan tace “Nabilah,kayakin nan daga
ina?”,Nabila ta ajiye leather din a ‘kasa saita
zauna a kan gado tace “Hmm wlh umma ban
ro’keshi ba,da ya bani ma nace mishi yabari ni
banaso amma ya da ge saida na kar’ba,ki yarda
dani wallahi ba ro’konshi nayi ba”,jikin baba
Rabi yayi sanyi sai tace “Nasan bazaki ta’ba
ro’ko ba amma dai waye ya baki?”. Nabila ta
d’an yi jim sai tace “Ya Sultee neh”,cikin rashin
fahimta baba Rabi tace “Ya Allahu,waye kuma
ya Sultee?” Nabila tayi dariya tace “Lahh!umma
dama baki sani ba?”. Baba Rabi ta ja tsaki tace
“Ke ni banason shiririta,sunan mutum nakeso ba
sunanku na ‘yan zamani ba”,nan Nabila tace
“Ya Sultan fah nake nufi”
Baba Rabi ta fad’ad’a murmushinta tace “Allah
sarki,Allah ya sa ka da alheri,zo ki bud’e ledar
mu gani”,turo baki Nabila tayi tace “Ni fah
banason kayanshi,kawai zan mayar mishi” sai
ta tashi ta suri ledar tayi hanyar ‘kofa,sunanta
da baba Rabi ta kira shi ya sa ta tsaya
cak,cikin ‘bacin rai tafara magana “Haba
Nabila,yanzu har kyauta ya fito daga hannun
Yarima kice zaki mayar mishi?a wani dalili?ai
Yarima a matsayin ‘kanwa ya daukeki,yanzu in
da Auta neh ya baki zaki ce bakiso neh?kul
dama,karki sake wannan sakarcin” jiki ba ‘kwari
Nabila ta dawo ta zauna ‘kusa da baba Rabi
tace “Kiyi ha’kuri umma na sa ranki ya
‘baci,bazan sake ba” shafa fuskarta baba Rabi
tayi tace “Ba komai,bude ledar mugani”.
Su chocolates,biscuits,wafers,perfumes,jewelries
da material guda biyar hade da gelensu da
takalma,kaya kam tubarkallah. Baba Rabi dafe
‘kirji tayi tace “Yaron nan ai ba haka ake kyauta
ba,kayan yayi yawa”,saita tashi ta d’auki
mayafinta sai waje. Nabilah kam tazama
speechless don kayan har tsoro suka
bata,mamaki neh yacika ta,haka taketa bin
kayan da kallo
Hanee da maman Khalil
[1:48pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Tayi sallama a ‘kofar d’akin Sultee,amsawa yayi
sannan yace ta shigo. Ta shiga tasamu waje ta
zauna,ganin ita neh yasa Sultan sau’kar da
‘kafanshi daga kan centre table,a mutunce ya
gaisheta,ta amsa sai murmushi takeyi tana
mamakin sauyawar Sultan a lokaci d’aya.
Sultan da baya magana,ko kallon kirki baya
mata,gaisuwa ma da ‘kyar yake amsawa amma
wai yanzu shine har da gaisheta a mutunce da
girmamawa kamar uwarshi,taji dadi sosai.
Bayan ‘yan gaishe gaishe sai tace “Yarima naga
kayan da ka bama Nabila kuma mungode sai
dai gaskiya bazata iya amfani dasu ba,kayakin
sunyi yawa,ai da ko kad’an ka bata ya
wadatar”,har ranshi bai ji dad’i ba amma bai
nuna mata ba,sai ma murmushin ya’ke da yayi
yace “Umma,agaskiya ni na bata kayakin nan
neh a matsayin tsarabarta daga Yola,kuma ai
kyauta yana da kyau and ni na dauke ta neh a
matsayin ‘kanwata,kiyi ha’kuri ki d’aukeni
kaman yanda kika d’auki Saleem”,kallonshi ta
tsaya yi na d’an lokaci saitace “Ba komai,dama
ni naga kayan sunyi yawa neh amma yanzu na
fahimta,mungode sosai Allah ya ‘kara arziki”,
murmushi yayi yace “Ameen”. Sallama baba
Rabi ta mishi sannan tabar d’akin,tana fita
Sultee ya sau’ke wani ajiyar zuciya,afili yace
“Ya Allah,make my dreams come true”(Ya
Allah,kasa mafarki nah yazama gaskiya),ni da
maman K sai kallon-kallo mukeyi saitace
“Hanee kingane?wani irin mafarki”,girgiza kai
nayi nace “Wallahi bansani ba maman K,saidai
nasan watarana zamu gane”
Baba Rabi ta koma d’aki ta gayama Nabila
yanda sukayi da Sultee. Haka ta tattara kayan
ta kaishi cikin wardrobe ta rufe.
Akwana atashi yau ya kama saura kwana shida
d’aurin auren Amira da Sultee,suna waya sosai
and sun saba da juna,har cikin jijiyon Amira
Sultee neh,amma unfortunately a wajen Sultee
ba haka abun yake ba,shi kawai don biyayya
neh zai aureta ba don yana sonta ba saidai bai
ta’ba bari angane ba.
Hanee da maman Khalil
[2:05pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Saura kwana hudu bikin Sultee mai martaba
yayi shatar jirgi na tafiya Yola zuwa masarautar
Hamaz. Mutane dewa sunje ciki ko harda
Nabila,muma dai muna biye da biros namu.
Sun isa Hamaz lafiya,motoci da suka amsa
sunansu aka kawo don kwasar mutane daga
airport. Anci ansha an yi hira,abun gwanin
sha’awa,sarauniya Maryam itace kan gaba akan
komai kamar itane uwar amaryar(samun Kishiya
irin S. Maryam sai an tona,ko da yake ba abun
mamaki bane don sunada sanyin hali kamar
frndy nah Ummitah). Tunda suka isa Nabila
take ta son taga amarya,ta tambayi Hauwa
“Sister don Allah ina neh d’akin Gimbiya
Amira?”,Hauwa tayi murmushi ta kamo
hannunta tace “Taso muje na kaiki”. Sun d’anyi
tafiya kad’an sannan suka isa sashen gimbiya
Amee,ba kowa a parlour,nan sukaji kamar ana
kuka a d’aki. Dasauri suka shiga,turus sukayi
ganin Amira ta rungume hoto tanata kuka
kaman meh. Nabila ta taka zuwa bakin gadon
ta kira sunanta a hankali sai tace “Kiyi ha’kuri
anty,koma meh yake damunki kibar kuka kawai
ki mi’ka lamarinki zuwa ga Allah”,d’agowa
Amira tayi hawaye sai bin kumatunta sukeyi
sannan tayi murmushi tace “Nagode sister”.
Hauwa ta gayama Amira akan wannan neh
Nabila,Amira ta rungumeta tace “Allah sarki,naji
labarinki wajen ya Sultee”. Zaro.ido Nabila tayi
tace “Nashiga uku,zagina yayi ko?ko yace na
cika surutu?”. Amira ta share hawayenta tace
“A’a ko d’aya”, saita chanja topic din. Hira
sukeyi kaman dama sunsan juna,a d’akin Amira
ma ta kwana.
Washegari yakama thursday kuma yau neh
akayi mothers’ day,iyaye sun je,duk kowa
‘ya’yan sarauta,abun ya ‘kayatar sosai.
Washegari akayi Walima wanda malama Jamila
Moh Ali da malama Shukurah suka
gabatar,gaskiya malaman akwai ilimi.
Hanee da maman Khalil
[2:43pm, 24/01/2016] Haneefah : GIMBIYA
NAFEESAH
Na Haneefah Usman
®ONLINE HAUSA WRITERS da
Khadijah maman Khalil
Washegari asabar da misalin ‘karfe goma aka
d’aura auren Yarima Sultan Mu’awiya da
Gimbiya Amira Ibrahim akan sadaki naira dubu
hamsin,d’aurin auren da ya samu halartar
sarakunan Nigeria da ma ‘kasashen da ke
kewaye,shugaban ‘kasa ma yaje,’kusoshin
gwamnati da dai sauransu. Sarki Mu’awiya baki
ya kasa rufuwa,murna yakeyi da Allah ya nuna
mishi auren Sultan,haka ma sarki Ibrahim.
Da daddare wajen 9 aka tafi dinner a hall din
AMA,anyi decoration pink and white,amarya
tasaka pink material mai uban wal’kiya ango
kuma yasaka Blue anmishi aiki a rigan sosai
yayi bala’in kyau,hannun rigan irin meh lynx
dinnan.
Nabilah kuma wani material tasaka itama
blue,coincidentally kuma Sultee blue
yasaka,daga cikin wanda Sultee ya bata neh ta
d’auki d’aya ta d’inka,a table d’aya ta zauna da
Saleem sunata hira. Ana cikin program Saleem
ya d’an fita answering call sai wani yazo ya
zauna a ‘kusa da Nabila,mai da hankalinta tayi
zuwa amarya da ake ma spray,Sultee kuwa
gaba d’aya hankalinshi yana kanta. Mutumin ya
gabatar da kanshi as Nafi’u amma Naf ake
kiranshi,shi d’an sarkin Katsina neh,kyakkyawa
neh ba laifi saidai bai kai Sultee ba,da farko ta
shareshi amma daga baya saita fara amsa
mishi,suna cikin hira sai dariya sukeyi sai
wayarta ya fara ringing,tana dubawa taga Sultee
neh,maida kanta wajen zamanshi tayi saita ga
yananan amma ba ita yake kallo ba,atunaninta
maybe mistake yayi ba ita yakeson kira ba.
Mayar da wayar cikin purse tayi saita cigaba da
hirarta,chan wani call ya sake shigowa still
Sultee neh,tsaki taja azuciyarta tace “Ko meh
matsalarshi dani oho,watakila ma yanaso ya
dizgani a gaban mutane neh”.
Saka wayar tayi a silent sai ta mayar cikin
purse,bayan kaman minti goma sai wani waiter
(masu raba abinci a wajen) yazo yace
“Ma’am,yayanki yana kiranki a waje wai kije ta
bayan hall” tace “Okay ina zuwa”. Tajuya wajen
Naf tace “Ya Saleem yana ‘kirana awaje,bari
naje”,tami’ke ta fita ta hall din tabi ta hanyar
da zai sada ta da bayan hall din. Tun kafin ta
isa ta fara kwala mishi ‘kira “Ya Saleem!ina
kake neh?ni fah banganka ba”,gyaran murya taji
ta bayanta,tana juyawa ta zaro ido ta dafe
‘kirji,cikin rikicewa tace “Ya……”
Toh jama’a,ku dai cigaba da ha’kuri damu. We
love you all