← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

crazy dance takeyi abunta. Sultee sake baki yayi yana kallonta, ba abinda yafi damunshi ma kaman wai ga frnds nashi har biyu a tsaye suna kallonta tana rawa da black three-quarter tare da white vest. Amira ganin kallon da Sultee ke watsa mata yasa ba shiri ta ruga d’aki dagudu, Nabila ta fara kiranta “Anty, ban gama rawar ba fah, ya kika tafi”. Amira bata juyo ba balle ta tanka mata, gyaran muryan da taji ne yasa ta juyawa. Zaro ido tayi ta dafe ‘kirji ta tsala ihu, ihu takeyi kaman mahaukaciya ganin Sultee a tsaye ranshi a dagule, fuskar nan ba alamun sassautawa. Cafkota yayi ya wanka mata mari yace cikin d’aga murya “Wani irin iskanci neh wannan? An gayamiki nan gidan ‘yan giya ne da zaki kunna wa’ka kina rawa sai kace arniya? Wannan dabi’ar kuma daga ina?”. GIMBIYA NAFEESAH [3:13pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Tana ihu tana kuka ta fara magana “Wayyo ya Sultee kayi ha’kuri”, tsaki yaja yace “Wallahi in baki bar cikamin kunne da ihu ba sai na pasa bakin, ansa nake jira kibani ba ro’ko ba”, cikin kuka tace “Toh ka sake min kai na mana, akwai zafi”. Daya daga cikin abokanshi da sukazo ne yazo ya dafashi yace “Kayi ha’kuri ka saketa, bai kamata ka d’aga hannu ka mari mace ba, sam bai dace ba, ya kamata ka dinga controlling temper d’inka kar watarana ya saka da na sani”, ran Sultee sai tafarfasa yakeyi amma haka yayi ‘karfin halin sake gashin, tureta yayi har ta buga kanta a gini, yana huci yace “Bamu ‘kare magana ba, anjuma ki same ni a parlour”. Tana kuka tana matsa wajen da ta gara da bango bata tankamishi ba ta juya tayi hanyar d’aki, nan ya sake ‘kuluwa kuma, cike da masifa yace “Ba ki ji me nace bane?”, cikin murya mai nuna alamun taci kuka tace “Na…ji”. Kuka neh ya kusa ‘kwace mata, dagudu tayi d’aki ta fad’a kan gado tana cigaba da kuka, abun tausayi. A parlour kuwa friends nashi Abdul da Ahmad neh sukata bashi ha’kura tare da nuna mishi rashin dacewar marin da yayi ma Nabila, Abdul ya ‘kara da cewa “Duk da laifi tayi, kamata yayi ace ka zaunar da ita ka mata nasiha bawai duka ba, ta girme duka ai, don Allah ka gyara”, a sanyaye yace musu “Sorry dan Allah, I couldn’t control myself ne”, guntun tsaki Abdul yayi sannan yace “Ita ya kamata ka bama ha’kuri bamu ba, ni ka ‘bata min rai ma, kasa crush na kuka a banza”. ©Hanee da maman Khalil [3:27pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil A firgice Sultee ya d’ago ya kalleshi, cikin wani yanayi yace “Whatttt??!!?!, an gayama ‘kanwata kaman ko wace mace ne?, bama haka ba, tayi ‘karama da kula samari”, dariya Abdul yayi ganin yanda Sultee yayi responding, sai da yayi mai isarshi sannan yace “Ko baka bani go ahead ba I promise you sai na bi ta bayan idonka mun daidaita da ita”, “mtswwww, kai d’an iska neh wallahi, ni kar ka sake ‘bata min rai, barin shiga na kira madam d’in sai ku gaisa”, sannan ya mi’ke ya nufi d’akinta. Tun d’aga ‘kofa yake jin kukan Nabila na tashi amma sai ya fuske kawai yashiga d’akin Amira, zaune take a kan gado kaman mara gaskiya sannan tana tsorace. Taka wa yayi zuwa cikin d’akin, d’agowa tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kanta, a hankali tace “Ina yini? Don Allah kayi ha’kuri, baza…..”, girgiza kai kawai yayi sannan yace “Ban nemi wani explanation daga wajenki ba, duk da kema kina da naki laifin tun da kin kasa aiwatar da abinda nace, it’s okay by me, nadawo ai, yanzu ki tashi friends nah sunaso ku gaisa”. Bai jira meh zata ce ba yafita daga d’akin, mi’kewa Amira tayi tabi bayanshi zuwa parlourn. Zama tayi akan kujera sannan suka gaisa da friends nashin, Ahmad sai ‘kare mata kallo yakeyi da yake riga da skirt neh tasaka kuma sun kama jikinta. (Don Allah mata a kula, in abokin miji yazo kuma zaki fita ku gaisa toh yazama dole ki saka hijabi a jikinki, haramun neh yaga jikinki, ko baida niyyan kallonki toh fah shaidan yana iya rinjiyarsa har ya fara tunanin wani abu daban, Allah yasa agyara). Sun d’anyi barkwanci sannan ta tashi ta d’auko musu drinks suka sha, ta ma kasa had’a ido da Sultee, zaman da tayi a parlourn ma ‘karfin hali neh kawai da kuma gudun kar su gane yanda zamansun yake. ©Hanee da maman Khalil [4:34pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Sun d’an ta’ba hira kadan sannan suka mata sallama, Abdul yace “Madam mungode fah, ki kular min da ‘yar waje na”, murmushi Amira tayi sannan tace “Zan kula ma da ita In Sha Allahu”, kasake Sultee ya tsaya yana kallonsu, cike da ‘kosawa yace “Nikam muje na rakaku, nagaji inaso na huta”. Dariya dukkansu suka yi banda Sultee da ya wani had’e rai. Suna fita Amira tayi d’akin Nabila, tayita lallashinta da kyar dai tayi shiru sannan Amira taje fridge ta d’auko Ice ta saka a ‘karamin towel tana matsa ma Nabila goshinta da ya kumbura. Sai wash wash Nabila take tayi, daga baya suka je kitchen tare sukayi girki sannan kowa ya tafi d’akinshi. Sultee ne zaune a parlournshi da daddare yana zaune a kan kujera yana jujjuya tumbler da ke hannunshi, amma a zahirin gaskiya hankalinshi ba akan tumbler din yake ba. Tunani yakeyi ko wani hali Nabila take ciki yanzu, yayi nadamar marinta har cikin ranshi, da yaga tunanin ba mafita zai samo mishi ba sai kawai ya d’auki wayarshi ya ‘kira Nabila, lokacin ita kuma tana kwance a d’aki tana chatting kuma ba abinda tafi tsana kaman a kirata in tana chatting, tsaki taja afili tace “Ko meh mugun nan yake nema a wajena oho”, batayi picking ba har ya tsinke. Ya kirata yakai sau biyar amma batayi picking ba, a na shidan neh ta d’auka tana mai jin takaicin katse mata chatting da yayi. Batayi magana ba, shima kuma baiyi ba, sun dad’e a haka sai chan Sultee ya bud’e bakinshi da kyar yace “Where are you?”, cike da mamakin jin baiyi masifa ba tace a ta’kaice “My room”, ya d’anyi shiru sannan yace “Ba nace kizo ki sameni a parlour ba?”, ta’be baki tayi sannan tace “Na manta neh kuma ni kaina yana ciwo”. ©Hanee da maman Khalil [4:54pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Ajiyar zuciya yayi sannan yace “So bazaki zo din ba kenan ko?”, Nabila tace “Bazan iya ba gaskiya”, baice komai ba ya katse wayar. Nabila tayi wani dariya, a fili tace “Zai maida ni jaka, inje daga ni sai shi achan ya jibgeni ba mai ‘kwata na”. Cigaba da chatting nata tayi hankali kwance, nan take labarta ma Anty jamcy wacce take kaman sistanta amma abun mamaki a groupchat suka had’u har suka saba, ta gayamata yanda sukayi da Sultee yau, anty Jamcy ta ‘kara bata shawarwari masu kyaun gaske. Ummitah neh ta tura mata wani comedy video, Nabila dariya takeyi har da hawaye, videon ya mugun bata dariya, jin kaman mutum a tsaye a kanta yasa ta d’ago da sauri. Wa zata gani?? Sultee neh. Ba shiri dariyan ya tsaya, tashi zaune tayi tana tsoron kar ya dakata. Zama yayi a kujeran da ke cikin bedroom din yana fuskantarta, a hankali ya soma magana “Dama ‘karya kikamin da kikace kanki yana ciwo?”, nan ne ta tuna da ta mishi ‘karyan kanta yana ciwo gashi yazo ya sameta garau sai dariya takeyi, murya na rawa tace “Eh, A’a, yana ciwo, nasha magani shine yatafi”, kallonta yayi irin kin rainamin wayon nan, murmushi yayi yace “Ki chanja ‘karyar, wannan baiyi ba, ko minti talatin baiyi ba kice ya tafi?”. Ta wani dafa kanta kaman tana jin ciwo sai tace “Kaga ya dawo ba?, inaga bacci yakeso, sai da safe”, kwanciya tayi a kan gadon, tana faman jan bargo yace “Ciwon kan naki ma mai ra’ayi ne, tunda ya iya barinki ki ‘bare baki kina dariya ai sai ya jira na gama maganar da ya kawoni”. Ahankali ta mi’ke zaune tace “Yi ha’kuri ya Sultee, kaga wallahi dazun kamin ka dawon nan neh kawai na kunna wa’ka, tunda ka tafi ko gate bana fita sai in skul zanje kuma ko……”. ©Hanee da maman Khalil [5:32pm, 02/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Hannunshi yasa a baki alamun tayi shiru, ai kuwa ta kama bakinta gum. Murmushi yayi yace “Hmmm, duk abinda kikayi da bananan nasani duk da bakisan waya gayamin ba”, ras! gabanta ya fad’i, a zuciyanta tace “Nashiga uku, anda wani munafukin ne ya gayamishi, ko da yake ina ganin driver neh ko gate man don su kad’ai ne zasu iya gayamishi tunda nasan Anty Amira kam bazata fad’a mishi ba”. Gudun kar ya ramfota yasa ta wayance tace “Amma mutane basu tsoron Allah, har da ‘kullamin sharri, Allah zai sakamin”. Kallonta ya tsaya yi cike da mamakin denying da tayi amma sai ya fuske yace “Ni ba wannan bane ma yasa nace kizo”, ya d’an yi jim sai yace “I’m really sorry about today, na mareki ba tare da nasani ba don raina ne yayi mugun ‘baci”, mamaki neh ya cika Nabila tana tunani “Anya ya Sultee lafiyarshi lau?, wai ni yau yake bama ha’kuri?” wani zuciyarta kuwa dad’i neh acike, ganin taji mamaki yasa yayi murmushi yace “Ki bar mamaki, kyaun d’an Adam daman in yayi kuskure toh ya nemi gafara, ko da kuwa ma wanda ya girma neh”. Murmushi tayi wanda bata san lokacin da ya fito ba, ga hawayen farinciki da ya zubo mata tayi saurin sharewa, cike da farin ciki tace “Ba komai ya Sultee, ni har ga Allah ban ri’keka ba, nasan duk abinda kayimin ni na jawo da na kauce ma umurninka, I’m so sorry, In Sha Allahu bazan sake ba”. Tashi tsaye yayi yamata wani smile sannan yace “Ba komai, sai da safe”, tanata murmushi tace “Allah ya tashemu”, har ya
Chapter 13 · 0% Book details