Sashe 15
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH [3:32pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil 1st page ga abinda ke ciki “Abba ya kirani yace min nadawo gida yasamo min mata, duk da ba so nake yi ba amma sanin ladan yi ma iyaye biyayya yasa na amince”, 2nd page ya rubuta NABILAH, a ‘kasa kuma ya rubuta “It was love at first sight, ban ta’ba jin abu ya shiga min rai farat daya ba sai da na had’u da ita, she is loquacious, Ya Allah!! Kabani ikon aurenta”, 3rd page kuma “Nayi iya ‘ko’kari na na zuga abba har ya yarda Nabee zata zo Qatar tayi makaranta, nayi hakan ne don ina tsoron taje wani waje ta fara soyayya da wani, kuma na d’au ma kaina al’kawarin bazan ta’ba kusantar Amira ba har sai na auri Nabila”. ‘karfin hali Amira tayi ta bud’e next page din, ga abinda ke ciki “Ya Allah ka yafemin, nasan ina cutar Amira duk da bata ta’ba nunamin ba, watarana nasan zata iya tunani aranta ko banda lafiya ne saisa ban ta’ba nemanta ba, the truth is banaso na cuceta ne tunda nasan ba sonta nakeyi ba but ina matu’kar tausaya mata da take ha’kurin zama dani”. Tana gama page nan ta rufe takardar ta ajiye, kuka takeyi sosai, wannan shine son maso wani, azuciyarta tace “Ohh Allah!! Kabani ikon cinye jarabawar nan”, zuciyarta tafasa yakeyi ba kad’an ba, cikin zafin kishi ta kama hanyar fita daga parlourn, ta ma manta d’aukan kayan wanki ne ya kawota d’akin Sultee. Har ta kai ‘kofa sai kuma ta tsaya cak, ahankali ta fara karanta “Allahumma ajirni fi musibati wakhlifni khairan minha”, bayan ‘yan mintuna sai taji zuciyarta tayi sanyi. Gode ma Allah ta fara yi da ya halitto ta a musulma, dama ance wanda ya ri’ke Allah baya ta’bewa, gashi addu’an da tayi ya sau’ka’ka mata duk wani ‘bacin rai da takeji. Komawa d’akin tayi ta fito da kayan wankin sannan ta ‘kira driver yazo ya kai wajen laundry. ©Hanee da maman Khalil [3:46pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Tana shiga side nata ta samu Nabila ta gama shirin tafiya school, fuskar nan d’auke da murmushi tace “Anty Amira na tafi school, bari naje driver ya kaini”, ‘karfin hali Amira tayi ta ‘kwa’kulo murmushin dole sai tace “Amma fah driver ya tafi kai kayan ya Sultee laundry, sai dai in zaki jirashi ko kuma ki tari taxi”, ba tare da damuwa ba Nabila tace “Ayyah ba komai, da ba don zanyi latti ba da na jirashi amma ina sauri, barin tafi kawai”. Asanyaye Amira tace “Okay, Allah ya bada sa’a”, Nabila ta amsa “Ameen” sannan ta kama hanya sai bakin gate. Tafita tana tafiya a hankali tanata Allah yasa ta samu taxi da wuri, in ta d’anyi tafiya kad’an sai ta duba agogon hannunta. Tsaki taja afili sannan tace “Da nasan bazan samu taxi ba da na zauna jiran driver wallahi”, ta tsaya tana ‘yan dube-dube sai wani motar da gani sabuwa ce yazo ya tsaya a gabanta, cike da takaici ta d’anyi gaba da motar kad’an, nan mai motar ya sake binta yana danna horn. Gashi motar tint ne so ba halin taga wayene aciki, sau’kar da glass din motar akayi aka ‘kwala mata kira “Nabila!!!”, a d’an tsorace ta juya tana kallon motar, ita tunaninta d’aya “Ni ba ‘yar gari ba balle asan sunana, ba wanda ma nasani a garin nan tunda ba inda nake zuwa daga gida sai school, toh wayene wannan kenan?”. Sake kiran sunanta akayi amma ta’ki zuwa, tana tsaye kaman ba ita ake kira ba. Mai motar ne da yaga batada niyan zuwa sai ya fito, jin an bud’e motar yasa Nabila juyowa. 4 eyes sukayi dashi, cike da mamaki tace “laaa!! Ya Sultee, ai bansan kai bane, kayi ha’kuri don Allah”. ©Hanee da maman Khalil [9:04pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Murmushi yayi sannan ya had’e fuska yace “Zo nan”, sai ya koma cikin motar ya rufe. Ahankali ta isa wajen motar ta bude, wani sanyi ne had’e da ‘kamshi ya ziyarce ta, tada motar yayi suka bar wajen, makaranta ya wuce da ita sannan yayi parking a daidai lecture hall da zata shiga, ahankali ya juyo sai yace “Ban hanaki tsayuwa a waje ba? Mesa driver bai kawoki school din ba?”, Nabila ta amsa “Anty Amira tace ya kai kayanka laundry ne kuma bai dawo ba, in har zan jirashi zanyi latti”, ajiyar zuciya yayi sai yace “Muga wayarki”, mi’ka mishi tayi, nan ya hau danne-danne, chan sai ya ajiye shi a kan cinyarshi sai ya ce “Me kike jira?, ki tafi mana”. A rikice ta ke kallonshi sannan tace “Bangane ba, wayana nake jira ka bani”, wani kallo ya watsa mata sai yace “Nayi seizing, zan kawo miki sabo anjuma”, zata sake magana ya d’aga mata hannu yace “Don’t say anything, ba na son musu kema kin sani”, rai ‘bace ta bud’e ‘kofar ta fita. Sultee kuwa daga school nasu Nabila wajen siyan waya ya wuce, samsung galaxy edge ya sayamata sannan ya koma office. Abangaren Amira kuwa Nabila tana fita ta shige d’akinta ta zauna tana tunano abubuwan da ta karanta acikin 1-4 pages na diary d’in Sultee. A zuciyarta take magana “Amma fah kamar yasan me nake tunani, wallahi ni ina tsammanin lafiyarshi ba ‘kalau ba, ba namijin da za a aura mishi mata har tsawon wata hudu amma ba abinda ya shiga tsakaninsu, kai ko kallona ma fah bayayi mai kyau”. Chan sai ta tashi ta tsaya agaban mirror tana ‘kare ma kanta kallo, afili tace “Nafi Nabila kyau, diri, haske, hanci kawai tafini duk da nima inadashi, menene take dashi da ni bani dashi?”. ©Hanee da maman Khalil [9:19pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil Amira ta gama hasashenta gaba d’aya amma ba abinda Nabila ta fita dashi, ita ce ma ta ba ma Nabila tazara ba kad’an ba wajen fagen kyau. Sultee ne zaune a office nashi da wayar Nabila a hannunshi. Ranshi ‘bace yake karanta messages da suke exchanging ita da Saleem, tunani yakeyi “Allah yasa yaran nan ba soyayya sukeyi ba, Saleem is my only brother, zan iya ha’kura don shi”, chan kuma sai ya girgiza kai, wata zuciyar tace mishi “Ina!!! Soyayyar gaskiya fa kake mata, baza ka iya ha’kura da ita ba”. Bincike ya cigaba da yi har lokacin tashinshi yayi, ya d’auki phones nashi ya kulle office din ya sallami friends nashi da ke wajen sai ya nufi gida. Yana shiga gida lokacin driver ya sauke Nabila, har zata wuce ta’ki gaisheshi sai ya kirata, tana tuttura baki ta isa bakin motarshi tace “Gani”, bai amsa mata ba ya mi’ko mata wayar da ya sayamata. Kar’ba tayi nan take ta nemi haushin shi da take ji ta rasa, ihun dad’i tayi tana tsalle kaman zata rungumeshi ta fara kwararo godiya, bai ce mata komai ba illa murmushi da yayi ya kama hanya sai d’akinshi. Dagudu ta shiga side nasu ta fad’a kujeran da ke kusa da Amira, cike da murna Nabila tace “Anty kalli sabon wayana”, ta mi’ka mata wayar. Amira ta kalleta tace “Waiwai!! Sabuwar fitowa ce fah wannan, wa ya sayamiki haka?, ko dai mun kusa shan biki ne?” ta ‘karasa maganar tana dariya. Murmushi Nabila tayi sai tace “Haba aure, ni fah bazan yi aure ba sai naga ‘karshen biro”. Dariya Amira tayi tace “Kai Nabila, yanzu waya baki?”, tana murmushi tace “Ya Sultee ne ya kwace nawa dazu da ya kaini school, yanzu kuma muka had’u a parking space shine ya bani wannan”. A firgice Amira tace “Wani ya Sultee??, shi ya kaiki makaranta?, me ke tsakaninku?”, duk wad’annan tambayoyin kusan lokaci d’aya tayi su, bata ma san time da suka fito ba. ©Hanee da maman Khalil [10:12pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Nabila baki bud’e take kallonta, da ‘kyar ta iya furta “A’uzubillahi, haba anty Amira, zargi na kikeyi ne? Wallahi ba abinda ke tsakaninmu illa zumunci da kuma dauka na da yayi a matsayin ‘kanwarshi nima kuwa a matsayin yaya na d’aukeshi, bai kamata ki yanke hukunci haka ba”, sai sannan Amira ta gane tayi su’bucewar baki, ‘ko’karin saita kanta tayi sannan ta kama hannun Nabila tace “I’m so sorry sis, ba wai ina zarginki bane, nasan ba abinda ke tsakaninku, amma ko akwai ma ni ban damu ba, dama shi mijin mace hud’u ne, sannan in har Allah ya ‘kaddara abu zai faru toh fah dole ne sai ya faru, amma kiyi ha’kuri in har na ‘bata miki rai”. Hawaye Nabila ta share sannan tace “Kiyi ha’kuri, in har baki yadda ba wallahi zan maida mishi da wayarshi ince nagode”, tana gama fad’in haka ta d’auki wayar tayi hanyar ‘kofar parlour. Da sauri Amira ta tsaidata tace “Noo karki mayar mishi, zai ga kaman kin raina ne, kiyi ha’kuri ki ri’ke wayar, na tayaki murna sosai wallahi, akashe lafiya”, tayi wani fake murmushi. Nabila ta juyo tana kallon Amira tace “ba kiyi fushi ba?”, Amira ta girgiza kai tace “Not at all sis, ba komai”. Murmushi Nabila tayi sai tace “Thank you, barin je nasa a chaji”, sai ta d’auki hand bag nata da ke kan kujera ta wuce d’akinta. Da Sultee yazo cin abinci sam bai nuna wani abu ba, sama sama dai yana hira da Nabila, Amira kuwa saidai tayi murmushi ta bisu da ido, jifa-jifa take sa musu baki. Kwanaki suna tafiya, rayuwa yana ‘karewa, abu buwa dewa suna faruwa masu dad’i da mara dad’i, tsakanin Nabila da Sultee kuwa sun sha’ku sosai, kullum Amira addu’a takeyi akan Allah ya rage mata zafin kishin da takeji akan Sultee, cikin ikon Allah kuwa ahankali ta bar damuwa, gaba d’aya ta bar jin wani abu in taga Sultee da Nabila suna zaune suna hira sunata dariya. Saleem da Nabila kuwa kullum suna waya, yana jira ne ma tazo hutu don ya amayar mata da abinda ke zuciyarshi. Nabila ta gama exams nata, ya Sultee ma yasamu hutu, duk suka shirya don zuwa hutu 9ja, Nabila sai