← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

yace “Ba komai”. Nan aka tarkata aka kai Sultee airport,muma dai mun d’ad’d’aura seat belts namu,maman Khalil kaman zatayi kuka ta kalleni tace “Shikenan mun bar Adamawa”,nace mata “Kin manta zanu dawo d’aukan rahoton biki neh?” nan ta wangale baki sai murna takeyi tace “Na manta neh ai mutumiyar,Allah dai ya kaimu” murmushi nayi nace “Ameen”. Mun sauka lafiya,motoci dewa sukazo tarbar Yarima Sultan,cikin tawagar harda Nabila,tana hangoshi ta ta’ba Saleem tace “Ya Saleem ga Ya Sultee”,sai murna takeyi,kallonta ya d’an tsaya yi kaman mai karantar abu sai chan yace “Sai akayi yaya?Allah yasa yauma ki isheshi da surutu har ya disgaki a gaban mutane” Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Murgud’a masa baki tayi tace “Ya dizga din mana,ai ni ya dizga ba kai ba” murmushi kawai Saleem yayi bai ce mata komai ba. Sultee yana isowa inda suke tsaye a bakin motar ya mi’ka ma Saleem hannu suka gaisa,yayi kaman bai ga Nabila ba. Itakuma da taga haka sai kawai ta’ki mishi magana gudun disgel irin nashi,shiko Sultee yaso ta tare shi dda surutu sai yaga bata ce uffan ba,kamar zai mata magana sai kuma ya fasa kawai ya shiga motar sai gida. Mai martaba yayi murna kwarai da gaske da yaji Sultee da Amira sun daidaita kansu,saidai muyi fatan Allah yasa ayi biki a sa’a. Yabi murna ya cikata ganin babban d’anta ya dawo,baba Rabi,Nene,Amina da Jamila duk sunzo sun mishi barka da dawowa har d’aki amma ba Nabila ba alamunta. Har dare yana zuba ido amma bai ganta ba,sai chan ya ‘kira Saleem yace “Saleem kana ina?” Saleem ya amsa “Na d’an fita neh,da wani abu neh?” dasauri yace “No”(dama ya tambayeshi ko yana gida neh gudun kar suna tare da Nabila). Sultee yaci gaba “Ina Nabila neh?”,saleem yace “Gaskiya bansani ba amma dai inaga tana d’akinsu,in kira ma ita neh?” Sultee ya d’an yi jim sai kuma yace “No barshi kawai,ba komai”,Saleem yace “Okay toh bye”,kamin ya kashe Sultee yace “Umm,bance kuma ka gaya mata na kiraka ina tambayanta ba” dariya Saleem yayi yace “Ho ya Sultee,naji bazan gaya mata ba”,nan Sultee ya katse wayar Abangaren Nabila kuwa tunda taga Sultee yana wani ciccin magani a airport sai ta ji ba dadi,sai kawai ta yanke ma kanta baza ta sake shiga harkan shi ba illa gaisuwa da inta ganshi zai had’asu Kwana biyu shiru Sultee saidai ya hangi Nabila daga nesa,da ta ganshi take chanja hanya. Yau tana zaune a lambu ita kad’ai sai kawai taji mutum yayi sallama,d’ago kan da zatayi sai taga Sultee neh. Cikin in’ina tace “ya… Sul…tee… ina…yi…ni” murmushi yayi ganin ta wani rikice,zama yayi a gefenta sannan yace “Bazan amsa gaisuwar ba,are you avoiding me?” girgiza kai ta shiga yi tace “No ya Sultee wallahi ba haka bane,kawai dai…” saitayi shiru,kallonta yayi yace “Kawai dai meh?” ajiyar zuciya tayi tace “Naga kaman in ina ma magana ranka yana ‘baci bakaso neh saisa nabari”,”hmmm” kawai yace sannan ya mi’ke yace “Biyoni”. Nan ta fara binshi har side nashi,a parlour ya barta yashiga bedroom,kaman zata juya sai kuma ta fasa,don a tunaninta yace ta biyoshi kuma zai barta a tsaye shi ya wuce bedroom. Bai dade ba ya fito da wani ‘katon leather ya mi’ka mata,’kar’ba tayi tace “wa zan kai ma?” zama yayi akan kujera,ba tare da ya kalleta ba yace “Naki neh?”,cikin kidimewa tace “Nawa? nawa?nawa fah kace?” Gaisuwa zuwa gareki Amrah Auwal Muhd,nagode sosai. And to my sisi Faty Axland,Allah yabar zumunci,na rasa da wani baki zan nuna godiya ta,thanks alot kuma Allah ya baki lafiya. Sumayya Girei,Aseem,Milly my mamahh da Maryam miss purple kunfi kowa son book nan,i dey greet u all:D
Chapter 8 · 0% Book details