Sashe 17
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Hakan kuwa akayi, baba Rabi ta had’a kayanta tsaf ta saka a d’an ‘karamin jaka, tana kuka ta nufi parlourn sarki. Nan ta samesu suma sun gama shiri, shiga motar sukayi kowa da abinda yake sa’kawa a ranshi aka kama hanyar airport don sunci sa’a akwai flight na rana. Sun isa Hamaz, Ukasha ne da mai martaba suka je suka tarbesu. Nabila tana ganin baba Rabi dagudu ta rungumeta tanata kuka, baba Rabi ma ‘barkewa tayi da kuka sosai, mai martaba sarkin Hamaz da yaga kukan ba ‘karewa zaiyi ba sai yace “Kuyi ha’kuri, yanzu dai kuci abinci ku huta sai mu zauna muyi magana a nitse”. Nan fah aka bama baba Rabi d’aki ta shiga tayi Sallah aka kawo mata abinci, sam ta kasa cin abincin sabida halin da take ciki, a bangaren sarkin Yura da Yabi kuwa a daddafe suka watsa ruwa suka ci abinci don duk sun ‘kagu suji warwarewar wannan rikitaccen al’amari. Saida sukayi maghriba sannan sarkin Hamaz ya tura a kira kowannensu zuwa parlournshi don tattaunawa. Ba ‘bata lokaci kuwa Sultee, Nafisa, Amirah, Saleem, Ukasha, Hauwa, Yabi da sarkin Yura, sai mummy da ammi duk suka shigo aka zazzauna. Sarkin Yura ne yayi gyaran murya yace “Alhamdulillah yau an gane Nafisah, sai dai al’amarin akwai wani boyayyen abu a ciki wanda duk bamusan ya akayi hakan ya faru ba illa Rabi wacce yanzu zata mana bayanin abinda ta sani”. Nan fah kallo ya koma kan baba Rabi wacce take ta faman share hawaye. Murya a dishe tafara “Kaman yanda kuka sani, sunana Rabi kuma ni ‘yar Azare ce da ke jihar Bauchi, ina da ‘ya d’aya mai suna Nabilah, ita kad’ai Allah ya bani, ina matukar sonta da tausayinta wanda kuma kun san da hakan, tun da nakai ta yaye wajen mama na ban waiwayeta ba sai bayan wata shida don duk lokacin da nace zanje na dubota sai mamana tace min a’a nabari tukunna, banason mata musu sai kawai na bar maganar. Da naje gida d’aukota sai naga sun sha’ku sosai da mamana, hakan yasa na barta a Azare ni nadawo gidan sarki, bayan wata uku uku nake zuwa kuma Alhamdulillah lafiyarta lau, gata kyakkyawa abunta, sai dai duk da haka kullum kewarta nake yi, mijina yarasu lokacin tanada shekaru 2. Ahakan ne watarana lokacin tana da shekaru 4, na shirya da niyar zuwa na dubota ba tare da na sanarwa kowa a gida ba, da murna na na isa Azare, ina shiga d’akin mamana kawai sai naga abinda ya mugun firgita ni, Nabila ce kwance ba lafiya, numfashi ma da kyar take yi, aranar nayi kuka har na rasa me ke min dad’i, da dare nake tambayar mamana mesa bata gayamin Nabila batada lafiya ba, sai tacemin ai bataso ta tayarmin da hankali ne saisa kuma batayi sati da fara ciwon ba, ta ‘kara da cemin ai sunje asibiti ance wai hanjinta ne ya hahhad’u amma za’a koma nan da sati a mata operation. Tun da na isa gida ni nake jinyar ta, watarana na sata a gaba nayita kuka amma sai tacemin “Umma, kiyi ha’kuri ki bar kuka kinji?”, zan rungumeta har muyi bacci ahaka. Ana gobe zamu koma asibiti acikin dare Allah ya kar’bi rayuwarta, gashi na sata a raina sosai, bansan inda nake ba sai bayan kwana biyu. Muka cigaba da zaman makoki ‘yan uwana suna ‘kara ‘karfafamin guiwa har na samu na d’an watstsake, lokacin da Yabi ta kirani akan mesa ban dawo ba sai ban gayamata Nabila ce ta rasu ba, nace mata mamana ne batada lafiya amma dazaran ta warke zan dawo, tayimin Allah ya ‘kara sauki sannan mukayi sallama, kullum saita kirani mun gaisa kuma hakan yamin dad’i sosai. Ranar da ta cika wata d’aya da rasuwa mama na tacemin ya kamata na koma Yura, ba don naso ba haka na tattara kayana na kama hanya. Ahanyar mu ta zuwa ne mun tsaya a wani ‘kauye zamuyi Sallah, da yake mu dewa ne sai naje ta d’an bayan wani bishiya don na za ga, ina isa wajen naga yarinya sa’ar Nabila na ta had’a kai da guiwa tana kuka. Naji tausayinta sosai sai na isa wajenta nace “Yarinya me ya ajiyeki anan?, ki tashi ki tafi gida mana”. Baba Rabi ta ci gaba “Na jima ina mata magana kafin nan ta d’ago tana kallona, na tambayeta ina ne gidansu sai ta ce min cikin maganarta da bai gama fita ba “ni ban sani ba, kawai wata mata tazo ta ajiyeni tace min anjuma mama na zatazo ta tafi dani, kece mamana?”, na d’anyi jim kaman mai nazari sai namata murmushi nace eh, ni ce mamanki. Ta share hawayenta sai ta tambayeni me sunanta, ba tare da wani tunani ba nace Nabila, nan fah ta hau murna har mukayi sallah tare na siya mana abinci ma tare. Zamu shiga motar sai wasu mutane sukazo suna tambaya wai ko munga wata yarinya wacce take nuna alamun ta ‘bata, da yake babbar mota ne sai duk basusan ba da Nabila nashigo ba, masu nemantan har sukazo kaina, d’aya ya sunkuya yana tambayar Nabila ina mamarta, addu’a nafara yi Allah yasa kar tace bani bane. Da mamakina sai naga ta ‘kan’kame hannuna tace “umm umm, ni ga mamana”, murmushi suka mata sai suka ‘kara gaba, ba shiri na sauke wani ajiyar zuciya. Muka koma motar Nabila tana ma’kale da ni, ni ko dad’i ne ya cikani ganin na samu wanda zata zamarmin kaman ‘yata Nabila, nadawo Yura da yake basusan Nabila ta mutu ba sai na gabatar da sabuwar Nabila a matsayin ‘yata”. Shiru baba Rabi tayi tana kuka kad’an kad’an, gaba d’aya wajen mamaki ne ya cikasu, daga masu kuka sai masu hawaye kad’an, baba Rabi ta mai da kallonta wajen mummy sai ta sau’ko daga kan kujerar da take zaune tace “Don Allah kiyi ha’kuri, nasan ban kyauta ba da na ri’ke ‘yarki bayan agabana akazo ana nemanta amma da yake lokacin idona ya rufe akan nasamu gurbin Nabila, ban yi tunanin wani hali zaki shiga ba a matsayin uwa wanda ‘yarta ta ‘bata, wallahi ba da gayya nayi ba, dama na dad’e inama Nabila addu’ar Allah ya bayyana min iyayenta na nemi gafarar su don ni ce silar jinkirta komawarta garesu”, kuka ne yaci ‘karfinta sai tayi shiru, mummy tana hawaye ta taso ta ri’ko baba Rabi sai tace “Na yafe miki, har cikin zuciya na nayafe miki, Allah ya yafe mana baki d’aya”, kuka sukeyi dukkansu, Nabila tana kuka kaman mai neman shid’ewa, Amira ta rungumeta kaman za a ‘kwace musu ita. Bayan koke-koken ya d’an lafa ne sarkin Hamaz ya furzar da iska sai yace “Kinyi laifi babba da har lokacin da akazo nemanta kika’ki nunawa ba ‘yarki bace, wannan baida kyau, duk da nasan alokacin kina cikin zafin rashin ‘yarki”, baba Rabi ta jinjina kai tace “Kuyi ha’kuri, nasan nayi laifi babba kuma ashirye nake da na kar’bi duk hukuncin da zaku min”. Jikin kowa yayi sanyi a parlourn, Nabila ta fashe da wani sabon kuka tace “Haba haba haba umma, bai kamata hakan yafito daga bakinki ba, tun kamin nasan kaina kike kula dani, baki ta’ba nunamin ba kece uwata ba, duk abinda nake bu’kata kina bakin ‘ko’karinki kiga kin bani duk da kema kina da abubuwan yi da kud’in amma haka zaki ha’kura ki hana kanki don ni ki bani, kin bani tarbiya daidai gwargwado wanda ko da a gaban iyaye na neh iyakacin abinda zasumin kenan”, ta tashi ta rungumeta dukkansu biyu suna hawaye. Sarkin Hamaz ya sauke ajiyar zuciya sai yace “Tabbas kin kula min da ‘yata kuma mungode, yanzu abinda nake son na sani shine wayene ya zo har cikin gida ya d’auketa har ya kaita ‘kauye agaba da Bauchi sannan ya mantar da ita duk abinda tasani akan rayuwarta na baya?”. Nan fah kowa ‘kwa’kwalwarshi ta fara chaji, duk tunaninsu sun rasa wayene ya musu hakan tunda dai basu san wani ma’kiyinsu wanda yakeson ganin bayan d’aya daga cikinsu ba. Suna cikin tunanin abun sai wata tsohuwar baiwa tashigo tana share ‘kwalla, duk suka juyo suna kallonta, Ammi ne tayi magana tace “Dudu ya dai?, mesa kika shigo ba ko sallama?”, dudu tasa ihu ta zu’be a ‘kasa tace “Wallahi ni na saceta, wallahi ni ce, duk sharrin shaid’an ne”, afusace Ukasha ya nufeta zai wanketa da mari amma daddy(sarkin Hamaz) yayi saurin ri’keshi, idonshi a rufe ya fara magana “Daddy ka sakeni na daketa, tsohuwar banza tsohuwar wofi, mesa ta sacemin ‘kanwa?, yau sai kin san kin ta’bo ni”, da daddy yaga Ukasha yana neman fita daga hayyacinshi sai yayi magana a hankali “Ka nitsu banason zuciyarkan nan”, a hankali ya koma ya zauna a kan kujera yana bubbuga ‘kafa. Abba(sarkin Yura) ya watsa ma dudu wani shegen kallo yace “Gayamana, mesa kika saceta?, aikoki akayi?, wa ya saki?”, dudu ta tsorata sai zazzare ido takeyi, ba acikin hayyacinta ba ta fara surutu “Shi ne ai ya’ki ya aureni”, cike da mamaki daddy yace “wa?”. Dudu tayi wani dariyan hauka sai tace “Kai mana, nikuma shine na ‘kudiri aniyar sai na saka maka ba’kin cikin da har ka mutu bazaka daina ji ba, da yake na lura duk cikin ‘ya’yanka kafi son Nafisah saisa na kai sunanta wajen boka akan ya mata asiri ta tafi chan uwa duniya kuma ta manta komai akan rayuwarta na da kuma har abada karta dawo, boka ya kar’bi kud’ina yacemin aiki zaiyi kyau amma da sharad’in duk ranar da ta dawo nan har aka gane itace Nafisah toh fah ni fa hauka mun ‘kulla ‘kawance, banyi wata-wata ba nace naji na amince don ban ta’ba tsammanin zaku ganeta ba”. Cikin ‘bacin rai da daddy bai ta’ba shiga ba yatashi ya wanka mata mari lafiyayyu sannan ya fara dukanta yana ball da ita, da ‘kyar Sultee da Saleem suka rirri’keshi suna bashi ha’kuri, sai huci yakeyi kaman zaki, ‘kwala ma dogarin ‘kofa kira yayi, dagudu ya shigo ya rusuna kaman daman jira yakeyi a kirashi, cikin ‘bacin rai daddy yace “Ku dauki wannan tsohuwar banzar ku kullemin ita ku kuma azabtar da ita iya son ranku, banga amfaninta a nan ba, take her out!!!!!”, da sauri dogari ya nufi