Sashe 7
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Kiran sallar maghriba da akeyi neh ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula,d’aki ya shiga yayi alwala sannan yafito daga side nashi ya nufi masallacin da ke cikin masarautar,bai bar masallacin ba har akayi Isha don Sultee baya wasa da Sallah. Tare suka dawo shi da mai martaba sarkin Hamaz,dogaraye suka mara musu baya. Taku sukeyi mai burgewa,kuyi imagining sarki da yarima mai jiran gado suna tafiya a ‘kafa,kuma dai kunsan tafiya neh mai cike da charisma da ‘kasaita irin na jinin sarauta. Suna tafiya suna ta’ba hira kad’an- kad’an. Har ‘kofar side nashi mai martaba ya rakashi sannan sukayi sallama,Sultee ya shiga d’aki mai martaba kuma ya wuce sashenshi tare da mu’karrabanshi. Yana shiga parlournshi yaga kuyangi a tsattsaye awajen dinning,dukansu zubewa a’kasa sukayi suna kwasar gaisuwa gami da kirari,dinning area din yawuce,d’aya daga cikin securities nashi yaja mishi kujera ya zauna,yana zama ‘kuyangin da suka kawo mishi abincin suka zuzzuba mishi abinci kala-kala a plate daban- daban. Spoon ya d’auka ya dibi pepper soup na kayan ciki har zaikai baki wani security dinshi ya dakatar dashi yace “Sorry sir,just wait a minute” bai yi magana ba ya ajiye spoon din ya fitar da wayarshi ya fara danne-danne,securityn ya sa d’aya daga cikin ‘kuyangin tayi tasting kamin Sultee yaci don ya tabbatar ba a sa wani abu aciki ba Hakan kuwa akayi,d’aya ta zuba duk kalolin abincin a cikin ‘kananun plates,zama tayi a ‘kasa tacinye tas. Sai sannan securityn yace “It’s safe sir,zaka iya ci”,Sultee ci gaba da danna wayarshi yayi kaman baiji meh yace ba,sanin halinshi da securityn yayi yasa shi jan bakinshi yayi shiru Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bayan mintuna kusan biyar Sultee ya d’auki spoon ya dibi pepper soup din ya kai bakinshi,wani dad’i neh ya ratsashi wanda har saida ya lumshe idonshi don dadi,azuciyar shi yana rayawa “Wow!Ashe ba ‘karya bane da ake yabon ‘yan yola da kwarewa a fagen girki”,bud’e cikinshi yayi da kyau ya shanye pepper soup din dama shi yana bala’in son abun,daga baya kuma ya d’anci yam balls,juice da aka sa mishi acikin cup neh ya d’auka ya kur’bi kad’an sannan ya goge bakinshi da soviet sheet,mi’kewa yayi ya kwashe wayoyinshi yayi hanyar d’aki. ‘Kuyangi suka tattara wajen suka goge suka saka turaren wuta mai ‘kamshi,nan take wajen ya d’auki wani sabon ‘kamshi yayi clean kaman ba yanzu aka gama cin abinci a wajen ba. Sultee yana shiga d’aki yawuce toilet yayi wanka sai yayi shirin kwanciya,gado ya hau ya d’auki wayarshi da ke ta faman ringing,yana dubawa yaga Saleem neh,picking yayi suka d’an ta’ba hira sai chan Saleem yace “Ya Sultee wallahi Nabila ta matsamin wai saina bata kunyi waya”,murmushi yayi yace “Okay,bata” Nabila ta ‘karba sai washe ha’kora takeyi kamar yana ganinta,tace “Hello ya Sultee,ina yini?ya gajiyar hanya?ya ka samu su Anty Amirah?Yola da dadi?ya garin yake?ya…..” katseta yayi yace “Tambayoyin da kike jeromin nan wa zai amsa su?kin dai san banason surutu ko?” lan’kwasa murya tayi tace “Yi ha’kuri ya Sultee,amma ka taimaka ka amsa min”,ata’kaice yace “Lafiya lau” zata ‘kara magana yayi sauri yace “Malama sai anjuma”. Bai jira meh zatace ba ya katse wayar sannan yayi murmushi,afili yace “Nabila uwar surutu kaman parrot”. Kashe wutar d’akin yayi ya tofa addu’a ya kwanta bacci Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Abangaren Nabila kuwa Sultee yana kashe wayar ta mi’ka ma Saleem wayarshi tace “Ga abunka” dariya yafara mata yace “Ya Saleem ya sallameki ko?ke din neh kin cika surutu wlh” hararshi tayi tace “Oho dai,ina ruwanka?sarkin gulma toh baza kaji ba”,da yake a kusa da d’akin su Nabila suke zaune sai ta mishi sai da safe ta wuce d’akinsu Washegari Sultee ya gama breakfast around 9 sai ya nemi amasa iso ya gaida su Sarauniya Maryam da Fatima,yashiga ya gaidasu suka amsa mishi fuska asake,s. Maryam sai janshi takeyi da hira da yake ita din gwana ce wajen hira,s. Fatima kuwa sai jifa-jifa take sa musu baki don a matsayin ta na surika bai kamata ace ta ‘bare baki tana hira da surikinta ba. Amirah ta fito cikin doguwar riga ‘ba’ki,tayi kyau sosai,zama tayi ta gaisheshi,asake ya amsa mata,s. Maryam kam ko a jikinta ta ci gaba da hiranta da Sultee wanda duk kunya ya cikashi,azuciyarshi yace “Surutu kaman Nabila”,s. Fatima da taga s. Maryam batada niyan tashi ta bar wajen sai ta mi’ke tace “Ammi’n yara ni nayi ciki,ko kuma ma muje don akwai abinda nakeso na nuna miki”,s. Maryam ba don taso ba ta mi’ke tabi bayan s. Fatima,aka bar Sultee da Amira kawai a parlourn Sama-sama sukayi hira saiya tashi tsaye yace “Ni zan fita ganin gari”,murmushi Amira tayi sannan ta mi’ke tace “Muje zan rakaka,tunda kai bakasan kan gari ba ai ba inda kasani”,guntun dariya Sultee yayi yace “Okay, muje”. Sun jera gwanin ban sha’awa don sunyi matching,suka isa wajen parking na motoci,nan securities suka tattaso,kowa sai cewa yakeyi zaiyi driving nasu,Sultee baice ko uffan ba,Amirah ne tace “Ba komai,mu biyu kawai zamu fita don ba nisa zamuyi ba” Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Wata shegiyar benz suka d’auka,Sultee neh yake driving. Ita ta dinga nuna mishi directions har sukaje San Hussain,Top 10,Tidbe,Oasis,Wetland da dai sauransu,duk inda sukaje sai sun kwashi tarkace kamar ba da kud’i suke siya ba. Sun gama yawo yawonsu sai yake tambayarta “Ba wasu shopping plazas neh?” zaro ido Amirah tayi tace “Akwai su sosai ma kuwa,naga time ya tafi neh saisa,kallonta yayi kad’an sai yace “muje ko da biyu neh saimu koma gida”,Amirah tace “Okay yalla’bai,bani da ja”. Dariya yayi ya girgiza kai,sunje Jalabu da kuma Yakubu shopping plaza ya d’ad’d’auki abubuwa dewa wai zaima su s. Fatima da s. Maryam tsaraba. Suna isa gida dogarai sukayi musu rututu,nan Sultee ya mi’ka musu leda guda uku yace d’aya na s. Fatima,d’aya na s. Maryam sai d’aya wanda shi ledan yafi girma yace su kai ma Amira d’aki. Jin yace Amira yasata juyowa tace “Wace Amira fah?” murmushi yayi yafara tafiya zuwa sashin shi yace “In akwai wata Amira a gidannan nan bayan ke sai ki min bayani”. Kasa ce mishi komai tayi sai kawai ita ma ta kama hanyar sashinta. Ammi da Mummy sun nuna jin dadinsu sosai kuma suka tura mishi da sa’kon godiyarsu. Hauwa tadawo gida daga skul tashigo parlourn sashin Amira taga Ukasha ma yana nan suna hira da Amira,idonta ya sauka kan ledan kayakin da Sultee ya bama Amirah,dasauri tace “Lahh! wa aka kai shopping ba aje dani ba?” Amira tace “Ya Sultee neh fah yakaini”,Hauwa iyayen rigima tace “Whatt?! Ai wallahi ba yanda za ayi yabar garin nan bai kaini ni da ya Ukashat ba” tasowa yayi ya rankwasheta yace “Ba na hanaki kirana Ukashat ba?in bazaki ce Ukasha ba karki kira sunana” dafe kanta tayi ta tsala ihu “Wayyo ya Ukasha,kayi ha’kuri,wlh rankwashinka da zafi”. Tsaki yaja yace “Ba zafi ba,Allah yasa rankwashin sumar da ke yayi”. Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS Dagudu Hauwa tabar parlourn taje tasamu mommy,nan ma taga leda cike da kaya,a shagwabe tace “Haba don Allah,wai ni mesa ba a sona a gidannan neh?” mummy bata gane meh take nufi ba saitace “Ana sonki mana,meh aka miki?”,cikin muryar kuka tace “Wai wai ya Sultee ya kai Ya Amira shopping kuma ya sassaya muku abubuwa amma ni ko tunawa dani ma baiyi ba” dariya mummy tayi tace “In banda abinki ai ko ke yanzu kika ce akaiki zakiyi shopping za a kaiki” d’aga kafad’a Hauwa tayi tace “Noo ni banaso,da ya Sultee nakeso naje”,nan Ammi tashigo tace “Meh kikace mara kunya?babba dake amma kina abu kaman yarinya ‘karama,in kin cika mara kunya sai kije ki sameshi ki gayamishi,fita daga d’akinnan”. Tura baki Hauwa tayi tabar d’akin. Akwana atashi yau Sultee yacika 1 week acikin masarautar Hamaz,kullum sai ‘kara missing na surutun Nabila yakeyi,da yake ta kar’bi numbanshi a hannun Saleem sai ta na kiranshi da wayarta,zasu gaisa lami lafiya amma inta soma surutu shiru zaiyi yana jinta har saiya gaji saiyace “Kingama?” in tace “Eh” sai yace “Toh sai da safe”. Ana gobe zai koma Hauwa tashigo side nashi,gaishe shi tayi saitace “Ya Sultee”,d’ago kanshi yayi yace “eh?ina jinki” tafara “Yau baza kaje shopping bane?” murmushi yayi don kuwa yagane tanaso ya kaita shopping neh don Amira tamishi hirar yanda sukayi. Yace “Zanje,je ki shirya kizo ki rakani” murmushi tayi tace “Ashirye nake,muje”. Tashi yayi,driver neh ya tu’kasu sai “San Hussain”,suna isa yace mata “Ki d’auki duk abinda kikeso,barin je ta chan ina zuwa,in kin gama ki jirani a counter”,cike da d’oki tace “Toh” Harta gama kwasan tarkacenta bata ganshi ba,bata jima da gamawa ba sai gashi yana turo troller wanda yake cike da kaya,lissafi akayi aka gayamishi kudin yabiya sannan suka juyo zuwa gida Hanee da maman Khalil [1:38pm, 21/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Motar yana tsayawa a harabar gidan ta bud’e ‘kofar motar tace “Nagode ya Sultee”,dagudu tafita daga motar tana jan ledojin ta. ‘dakin Amira ta nufa,nan ta tarar da Ukasha ma a zaune. Cike da mamaki Amirah tace “Hauwa,daga ina da wannan uban kayan?” rawa tayi sannan tace “Ya Sultee neh ya kaini shopping”,Ukasha yana kallonta yace “Yau na tabbatar baki da hankali Hauwa,yanzu ro’konshi kika je kikayi?” girgiza ‘kugu tayi tace “Ina ruwanka dani?in ma ro’ko neh sai meh?” binta yayi,ai da gudu tayi kan Amira tana ihu “Kayi ha’kuri karka ran’kwasheni,ba ro’konshi nayi ba” dariya yayi yakoma inda yake zaune yace “Mara kunya,da kin tsaya ai da sai kin daku”. Washegari Sultee ya sallami gaba daya ‘yan gidan,ya ba ma Ukasha bundle na 1000 yace “Kaine bankai shopping ba amma ga wannan”,girgiza kai Ukasha yayi yace “No ka barshi,nagode”,yayi-yayi ya kar’ba amma Ukasha ya’ki,mai martaba neh da yaga gardaman yayi yawa sai yace “Ukasha,kar’bi kud’in,ai shi yayan ka neh”. Kar’ban kudin yayi yace “Nagode ya Sultan”,murmushi yayi