← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya fuske, cikin ko-in-kula yace “And so?, macen da na ganin ai matata ce, fiye da haka ma an halarta min zan iya yi ba kallo kawai ba”, bata tanka mishi ba ta juya da niyyar komawa kan gado, ri’ko hannunta yayi, cike da tsiwa ta juyo, ta bud’e baki zatayi magana kawai taji yakai bakinshi kan nata, sai tuttureshi takeyi amma shi sai ‘kara mannata a jikinshi yakeyi, da taga yana neman wuce iyaka sai ta sa mishi kuka, ido a raunane ya saketa ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba. Kan gado ta fad’a ta fashe da kuka tana cewa “Yanzu shikenan ni duk abinda yaga daman yi dani zaiyi?, wallahi bazan yarda ba, shi kuma da yake bai da kunya har cikin d’akina a cikin gidan ubana yazo yake neman gwadamin tantirancin shi”, tsaki taja ta koma toilet tayi brush tana ta goga harshenta tana d’an hawaye. Adaren ranar Sultee ya tsokano ma kanshi tsuliyar dodo, gaba d’aya ya kasa samun nitsuwa, tsaki ya dinga ja yana da-na-sanin romancing din Nafisa da yayi don yasan hakan ne ya jefashi a halin da yake ciki, juyi ya dinga yi da ‘kyar bacci ya d’aukeshi. Yau Wednesday ranar tafiyar Sultee da Gimbiya Nafee, tun asubah da suka tashi basu koma bacci ba, shiri akayi sosai, sunci sun ‘koshi sannan aka musu rakiya zuwa airport, ciki ko harda daddy da Ammi, mummy kam tace bazata iya zuwa ba tana a matsayin uwa, baba Rabi tayi kukan rabuwa da Nafisa sosai. A airport su daddy suka musu sallama zasu juya, da gudu taje ta ‘kan’kameshi da Amira tana kuka tace “Daddy don Allah mu tafi tare, Anty Amira kinga ai kinsaba da chan din, mutafi don Allah, bazan iya zama ni kad’ai ba”, ta ‘kara fashewa da wani kukan Amira na tayata, da ‘kyar daddy ya lallasheta yace “Yi ha’kuri mamana, kinga yanzu bamuyi shirin tafiya da ku ba amma ki bari in kin kwana biyu zamuzo dukkanmu kinji?”, girgiza kai tayi tana share hawaye “Daddy kayi al’kawari?”, asanyaye yace “Zan miki ‘karya ne?, in kin kwana biyu zamuzo mu dubaki, ai ba ke kad’ai bane achan, ga yayanki Sultan zai dinga kula da ke”. Cikin dishewar murya tace “Toh daddy, kuma…..”, announcement da akayi akan duk masu tafiya suyi boarding ne ya katse mata maganarta, daddy ya dafata yace “Yi ha’kuri kije, zamu dinga waya kullum”, kama hannunta Sultee yayi suka musu sallama, Nafisa sai waigowa takeyi tana hawaye har ta bar ganinsu, ji takeyi kaman a kunce auren ta huta tunda dai tasan ba sonshi takeyi ba. Acikin jirgi seat nashi ne ata window, asanyaye tace “Ayyah ya Sultee muyi exchanging seats kaji?”, cike da tausayinta yace “Okay ba damuwa”, sun lula a sararin samaniya, chan sai ya Sultee yace mata bari yaje toilet, yana tashi wani kyakkyawan saurayi bazai wuci 27-28 ba yazo ya zauna a inda ya tashi, sallama yayi mata ta amsa mishi, yace “sunana D…..”, katseshi tayi tace “Sorry please ni matar aure ce”, ya langa’bar da kai yace “Amma nayi rashin sa’a, wayene yamin shigan sauri haka?”, murmushi ta mishi tace “Yaya na ne shi”, ya d’anyi dariya sannan yace “Ohhh ko dai shine wanda ya tashi daga nan?”, wani murmushi ta sakeyi, zata bashi amsa kenan taji muryar Sultee cike da masifa yace “Excuse me, da matar mutum fah kake magana wanda hakan bai dace ba”, guy din ya tashi tsaye, ganin yanda Sultee ya wani had’e rai yasa yace “Sorry bro, wallahi bansan matar aure bace saida ta gayamin, I’m so sorry”, bai jira meh zaice ba ya koma seat nashi. Sultee iya ‘kuluwa ya ‘kulu, kishi ne yake cinshi, “wai matata tana ma wani murmushi har suna hira?, meh ma ya gayamata da ta ji dad’i haka?”, baisan sanda yayi tsaki a fili ba, Nafisa ta kalleshi sai taga sam bata kyauta ba, ahankali tace “Sorry ya Sultee, naga kaman ranka ya ‘baci”, afusace ya kalleta sannan yace “Wai ma meh had’inki dashi da zaki wage baki kina dariya dashi?”, kallonshi takeyi cike da mamaki, ita dai tasan ba tayi dariya da guy din ba. Shareshi tayi, haka yayita masifarshi har ya gaji yayi shiru, ita ba abinda takeyi sai dariya ‘kasa-‘kasa, da taga ya saka earpiece ya rufe ido sai ta tsamman yayi bacci, shafa fuskarshi tayi afili tace “In yana bacci zaka ganshi kaman wani silent guy amma masifar shi yafishi tsawo”, bud’e ido yayi ya harareta, da sauri ta cire hannunta daga fuskarshi, cike da kunya ta sunkuyar da kai, tsaki yaja yace “Ni ne masifaffe ko?, wai nikam mesa kika raina ni ne?, don kina ganin ina sassauta miki ko?, wallahi zan iya ajiye aure a gefe na yi maganinki, kema kinsan ‘karamin aiki na ne”, ‘kwafa tayi ta tura mishi ‘keya tace “Ahaka zaka ‘kare, mutum kullum cikin masifa sai kace a kanshi aka saukeshi”, juyo da kanta yayi yace “Da waye kikeyi?”, taji tsoro amma sai ta dake tace “Haa, na ‘kira suna ne?, mutum nace, ko kai sunanka mutum ne?, A’uzubillah!!, na tsani masifa wallahi”, ganin in ya biye mata zasu tara ‘yan kallo yasa ya tura kanta har ta kusa gara kanta, bai ce mata komai ba yaci gaba da jin ‘kira’ar Sudais da ke tashi a earpiece nashi. Kusan awa biyu Nafisa tanaso ta mishi magana amma tana tsoro, gaba d’aya sai taji tanason tayi magana, shirun ya isheta gashi ta kasa bacci, chan sai ta d’anyi innocent face, ta matso daf da Sultee ta kwanta a kan kafad’arshi, bai tanka mata ba yaci gaba da game nashi a waya, da taga baiyi magana ba sai ta sakala hannunta ta cikinshi, yaji yarrr amma dai ya fuske, chan sai Nafisa tace “Ya Sultee ayyah muyi surutu mana, wallahi na gaji da zama shiru, duk sainaji kaman baki na zaiyi ciwo don banyi magana ba, kaji?”, dariya ya kusa ‘kubce mishi amma sai ya gintse dariyar, a zuciyarshi yace “Ohh Nafisa akwai surutu, shi ne in batayi ba bakinta zaiyi ciwo” amma a fili sai yace “Ni banason surutunkin nan, nagaji”, shiru tayi na d’an seconds sai kuma tace “Ya Sultee, meh kakeji a earpiece din ne?”, ba tare da ya kalleta ba yace “Kira’a nakeji”, tashi daga jikinshi tayi tace “Laa!!, ya Sultee ayyah tsammin ear piece d’aya nima bari naji”, ajiyar zuciya yayi sannan yace “Don Allah ki ‘kyaleni, banson takura, ina wayarki da baza kiji dashi ba?” Fuskar tausayi tayi tace “Na manta dashi a gida, saidai in mun isa ka siyamin wani”, dariya yayi yace “Allah ya ‘kara, wazai saya miki wani?”, tayi murmushi tace “Kai mana”, Sultee yace “Lallai kam, ai kin ‘kare ri’ke waya kenan inaga don bazan saya miki wani ba”, kuka tasa mishi sosai hakan yasa ya jawota jikinshi ya fara lallashinta yace “Shhh, ni wasa nake miki, zan sayamiki kinji?”, tureshi tayi tace “Gwanda da ka gyara magana”, mi’ka mata earpiece d’aya yayi suka cigaba da jin ‘kira’ar suna d’an hira sama sama wanda rabi masifa ne. Sun sauka Qatar lami lafiya, driver yazo ya d’aukesu suka nufi gida. Agajiye suka shiga parlour, gidan upstairs ne, parlourn ‘katon gaske ne, Nafisa ko zama batayi ba tace a gajiye “Ya Sultee ina ne d’akina, inaso naje na huta”, bai mata magana ba ya fara hawa sama, ganin haka yasa tabi bayanshi, wani d’aki ya nuna mata yace “Nan ne naki”, sai ya juya ya tafi. Da yake da dare suka iso kuma duk sunci abinci so sai kawai kowa yabi lafiyar gado. Washegari bata tashi ba har wajen 10am, da wurwuri tashiga tayi wanka, tana ta Allah yasa Ya Sultee kar ya hauta da masifar tayi bacci dewa, doguwar riga tasaka sannan ta tsaya ‘kare ma d’akin kallo, d’aki ne had’ad’d’e da royal bed aciki, ga kujeru guda uku a ta gefe, da d’an ‘karamin carpet had’e da centre table, d’akin dai ya tsaru gaskiya. Takalmi flat shoe ta saka ta sauko ‘kasa, anan ta tarar dashi zaune a parlour yana kallon tv yana shan tea, tun da ta shigo yake binta da kallo kaman maye, zama tayi a kan kujera tace “Ina kwana ya Sultee?”, murmushi ya mata sannan yamata alamun tazo, cike da fargaba ta nufi kujerar da yake zaune, ajiye cup din yayi sai ya jawota ta fad’o jikinshi, acikin kunnenta ya rad’a mata “Haka ake gaisuwar?”, gyara zama tayi tana sunkuyar da kai tace “Eh mana”, kallonta yayi yaga ta mishi kyau, a hankali yace “Ni banason irin wannan gaskiya”, d’agowa tayi tace “irin wanne kakeso?”, murmushi ya mata ya ‘kura mata ido, yayi kissing nata na minti biyu sai ya saketa yace “Irin wannan”, cike da kunya ta fara ‘ko’karin tashi daga jikinshi, jawota ya ‘kara yi yace “Sarkin kunya, ina zakije?”, kanta a sunkuye tace “Breakfast zan d’aura mana”, tashi yayi cikin sauri yace “Sorry babyna, na saya ai tun dazu but kina bacci saisa ban tasheki ba”, wasa da yatsun hannunta tafara tana mamaki wai yau ya Sultee ne ke mata abubuwan nan, har yana kiranta “babyna”, dawowarshi ne ya katse mata tunaninta. Feeding nata yayi, tun tana tutturjewa har ta d’an saki jiki ya bata tayi nak, kwanto da ita yayi jikinsa suna kallon tv, Nafisa duk sai taji ta a takure, ahankali ta fara zamewa, ri’kota yayi yace “Yadai?”, a hankali tace “Girki zan mana”, girgiza kai yayi yace “Noo jiya fah muka iso, ki huta tukunna sai bayan 2days sai ki fara mana girkin, zan dinga siyo mana a restaurant”, ba don taso ba tace “Toh”, chan kuma kamar an mitsileta ta tashi tace “Ya Sultee ayyah kiramin su daddy muyi magana”, Sultee ya ‘kara janyota ya d’aurata akan cinyarshi yace “Okay” sannan ya ciro wayarshi daga aljihu. Kira d’aya biyu daddy ya d’aga, gaishe shi yayi tukunna yaba ma Nafisa, cike da d’oki ta kar’ba suka gaisa, sun d’anyi hira sannan sukayi sallama, saida tasa ya kira mata su Amira, Ammi, Mummy, Hauwa, Ukasha, sannan ta ‘kyaleshi. Sunacin abincin rana sai Saleem ya kirashi, sun gaisa normal, Nafisa ta fara jijjigashi “Ya Sultee zanyi magana dashi, ka bani”, Saleem daga d’ayan ‘bangaren yaji muryar Nafisa tana magiya kuma yasan ya Sultee ba bata zaiyi ba, dariya yayi yace “Ya Sultee bata
Chapter 21 · 0% Book details