← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

d’oki takeyi zata je gida don rabonta da gida shekara d’aya kenan. Yau ya kama su Sultee zasu diro 9ja, tsaraba dewa Nabila ta siya ma ‘yan uwa da abokan arziki, ni da maman K ma mun siyo tsaraba ma duk masu son novel dinnan, kowa yazo ya kar’ba… lol. Da dare misalin 7:30pm jirgi ya sau’ka a airport din garin Kaduna. Motoci aka turo aka d’aukesu daga airport, Saleem yana ganin Nabila da gudu yaje ya rungume ta kaman za a kwace mishi ita, Sultee ya d’auko trolley’nshi ya fara neman Nabila, chan ya hangota rungume a jikin Saleem, nan take zuciyarshi ya shiga bugawa, bai ma jira Amira ba ya kama hanya sai wajensu Nabila. Yana isa ya fincike ta daga jikin Saleem, suna had’a ido dashi ta fara kame- kame “Ya Sultee kaga ya Saleem ashe tun dazu suka iso”, tsaki yaja sannan yace “Allah ya nunamin ranar da zaki san kin girma, wai ke bakisan kin balaga bane ko meh? Kina barin namijin da ba muharraminki ba ya rungumeki sai kace mara hankali, baki san zunubi kike kwasa ba ko?”, idanun Nabila ya ciko da ‘kwalla tace “Ya Sultee kaima kasan bana rungume maza wallahi, yanzun ma don ya Saleem ne kuma ina murnar ganinshi saisa”. Harararta yayi sai yace “Sai meh don kina murnar ganinshi? Sai akace idonki yarufe ki manta da haram da halal? Batun kina cewa don Saleem ne kuma, don yana matsayin yayanki ba shi ne ya sa ya zama yayanki ba, biological brother shi ne kad’ai aka halatta ku had’a jiki, Saleem fah ba komai naki bane karki manta”. Jinjina kai Nabila tayi tana nadamar abinda ta aikata, sannan tace “In Sha Allahu bazan sake ba”, murmushi yayi yace “Good girl”. Saleem da ranshi yayi matu’kar ‘baci yace “In tayi aure zanga iyakacin ikonka akanta”, maida dubanshi zuwa wajen Saleem yayi sai yace “hmmm, daman aure kam dole tayi ai”. Kallonta Saleem yayi sannan ya kalli Sultee saiyace “Aure kam kwanan nan ne ma don ni zata aura da yardar Allah, dama jira nakeyi ta dawo sai nayima mai martaba magana”. Daidai lokacin da Amira kuwa ta iso wajen da murmushi a fuskarta, cikin wani lion voice Sultee yace “Whattttt?!!!, Aure?, Nabila?, Da kai??” Saleem ya jinjina kai yace “Ofcourse, ni zan aureta, dama na dad’e ina DAKON SO”(Book by kausar). ©Hanee da maman Khalil [11:05pm, 06/02/2016] Haneefah Usman: GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® OHW da © Khadijah maman Khalil - Wani wawan tsaki Sultee yayi, bai ta’ba shiga tashin hankali irin wannan ba, da kyar yayi ‘ko’karin controlling na temper dinshi. Bai ce komai ba ya ja trolley’nshi ya kama hannun Nabila sai motar, bai ma jira securities sun bud’e mishi ba ya saka hannunshi ya bud’e ya turata aciki sannan shima yashiga. Yana rufe ‘kofa Saleem da Amira suna isowa wajen, nan take Sultee yace ma driver ya tada motar su tafi gida, ba musu kuwa driver ya cika aiki. Trolleys d’insu ma dogaraye ne suka saka su a sauran motocin sannan suka bi bayansu. Da suka isa gida mai martaba yaji mamaki da yaga Nabila da Sultee a motar d’aya, amma da yaga su Amira sun iso kuma ba wani matsala sai kawai ya share akan daga baya zai nemi ‘karin bayani wajen Sultan. Duk anyi murna, Nabila harda hawayenta yau ta dawo gida, baba Rabi murna kaman ta zuba ruwa a ‘kasa tasha, dukkansu hudun ba wanda ya bari aka gane me ya faru a airport. Anci ansha anyi hira sannan kowa ya nufi d’aki don hutawa. Bayan Nabila ta rarraba ma kowa tsarabarshi sai ta je ta watsa ruwa, ta gama komai sai tayi sallolinta tabi lafiyar gado. Washegari bayan anyi breakfast sai baba Rabi ta jata suka koma d’aki, nan Nabila ta hau bata labarin school nasu da friends nata na chan, har da wayar da Sultee ya siya mata. Baba Rabi taji dad’i da taji Sultee da Nabila sun shirya, sun dad’e suna hira sai tace “Amma meke tsakaninki da Yarima?”, murmushi Nabila tayi sannan tace “Bakomai fah umma, me kika gani?”. Ajiyar zuciya baba Rabi tayi sannan tace “ke dashi a motar d’aya kuka dawo sannan matarshi tana motar daban, ana cin abinci ma ina lura dashi sosai, duk motsinki akan idonshi ne, inaga yama manta Amira ce matarshi ba ke ba, ya ta’ba gayamiki yana sonki ko makamancin haka?”, zaro ido Nabila tayi jin inda zancen baba Rabi ya dosa, a rikice ta ce “A’a wallahi, ni fah ba komai, kawai dai inaga baki lura bane, bani yake kallo ba wata’kila”, kallonta baba Rabi tayi sannan tace “Allah ya kyauta”, suka cigaba da hirarsu cike da nishad’i tana ‘kara jaddada ma Nabila akan karta kuskura ta butulce ma su Sultee don su suka mata gata a duniyar nan. Bayan kwana biyu da dawowarsu gaba d’aya Nabila a d’aki take yini, watarana ta zauna tayi tagumi tana tunanin ya Sultee da kuma maganganun baba Rabi na cewar yana sonta, haka zata yita dariya ita kad’ai tace ai wannan yafi ‘karfina, ina ma zai kalleni bayan yanada kamar anty Amira wacce ta fini da komai. Sun huta na sati d’aya sai mai martaba yace su shirya suje garin Hamaz, hakan kuwa akayi, Amira ta dage sai ta tafi da Nabila don tana bama su Ammi da mummy labarinta, da ‘kyar dai Nabila ta yarda zasuje tare. Sun sau’ka Hamaz lafiya lau, murna wajen familyn Amira ba kama hannun yaro, shekara d’aya ba wasa ba. Hauwa har ta gama secondary school yanzu tana jiran admission, Ukasha kuwa yana part 3 ya ‘kara girma yayi kyau abunshi, dama fulani ba dai kyau ba. Bayan maghriba aka zauna sai hira akeyi abun dai gwanin sha’awa, chan sai Amira ta fashe da kuka, duk parlourn sun rikice suka fara tambayarta “Lafiya?, me ya saki kuka?”, Nabila ta taso ta rungumeta tana bubbuga mata bayanta, da kyar dai Amira ta tsagaita kukan da takeyi, cikin muryar kuka tace “I miss her, da tananan da gidanmu ya zama full house, yanzu wayasan ko tana ina? Ko tana shan wahala?”, nan jikin kowa yayi sanyi jin ta ambaci Gimbiya Nafeesah, gaba d’aya parlourn rashin Nafeesah yadawo musu sabo fil, ‘karfin hali kawai sukeyi na ganin basuyi kuka ba amma duk sai da suka zubda hawaye. Nabila ta share hawayenta tace “Anty Amira kiyi ha’kuri, In Sha Allahu tana cikin ‘koshin lafiya, aci gaba da addu’a zata bayyana da yardar Allah”, girgiza kai kawai Amira tayi. Basu wani jima a parlourn ba kowa ya kama hanyar d’akinshi, Sultee ma dai ya musu fatan Allah yasa aganeta. Ana gobe zasu koma Yura Nabila ta fito daga wanka d’aure da towel sai Mummy tashigo d’akin don ta kirata suyi breakfast, turus ta tsaya ganin tabon da ke bayan wuyanta. Cikin hanzari ta nufi Nabila ta d’an ja towel d’in ‘kasa, kuka ta fashe dashi tana rungume da Nabila, Nabila da bata san meke faruwa ba ta hau tambayar me ya faru, Mummy ta kasa magana sai kuka takeyi. Da kyar ta samu tasa kaya sannan mummy tace “Don Allah ki kiramin ‘yan gidan gaba d’aya yanzun nan”, dasauri Nabila ta fita don sanar dasu sa’kon mummy, duk sunji mamaki da sukaga Nabila a birkice, jiki ba ‘kwari tace “Mummy tana kiranku gaba d’aya wai a sameta a d’akin da na sau’ka”, har rige-rigen zuwa d’akin suka shiga yi kowa da abinda yake sa’kawa a ranshi. Ammi ta rungumeta tace “Meh yasaki kuka anty?, in har akan Nafeesah ne In Sha Allahu zamu ganeta in har munada rabon sake ganinta”, nan mummy tafara dube-dube tace “Ina Nabila?, ku kiramin ita, karku barta ta sake barinmu don Allah”, nan aka tura akazo da Nabila. Tazauna a ‘kasa tana jiran ‘karin bayani, rungumeta mummy ta sakeyi sannan ta fashe da wani sabon kuka, acikin kukan take cewa “Yau Allah ya amsa addu’ar mu, wallahi Nafeesah ce wannan, wallahi itace, ga tabon da ke bayanta, Nafeesah nah ne”, ba ita kad’ai ba, dukkansu kuka sukasa in banda Sultee da yake tsaye yana ganin ikon Allah, Amira harda sheshsheka takeyi, awannan ranar sunyi kukan murna ba kad’an ba. Bayan kukan ya tsagaita ne Nabila tace “Noo bani bace Nafeesah, ni fah uwata jakadiya ce sunanta baba Rabi, kuma mu ‘yan Bauchi ne, ba abinda ya had’amu da Yola, kumin bayani, ni fah kaina yana neman fashewa, wallahi ina rikice, umma ce mamana, ni ba ‘yar sarauta bace, ni ba kowa bace illa yarinya talaka mai wadatar zuci har Allah ya kaini matsayin da nake ciki a yanzu”, nan ta fashe da kuka. Atake mai martaba ya ‘kira sarkin Yura ya shaidamishi abinda ke faruwa kuma yace suyi ‘kokarin zuwa da baba Rabi a ranar tunda akwai flight na yamma, sukayi sallama. Mai martaba ya ‘kira Yabi da baba Rabi ya musu bayani kaman yanda Sarkin Hamaz ya mishi, kuka baba Rabi tafara tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, shikenan, dama nasan wannan ranar dole yazo”, duk suka bita da kallon tuhuma, Yabi tace “Bamu gane ba, yi mana bayani”, baba Rabi tana kuka ta ‘kara cewa “Tabbas Nabila ba ‘yata bace, labari ne mai tsawo amma muje Hamaz din zan warware muku komai”, tana kaiwa nan ta tashi tana kuka ta tafi had’a kayanta. Ba shiri mai martaba ya kira sarkin Hamaz ya gayamishi ai baba Rabi tace ba ita bace mahaifiyar Nabila. Fashewa da kuka Nabila tayi tana karanto “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, dukkansu suna so suji ya abin ya kasance, Sultee da yaji abinda baba Rabi tace ba ‘karamin tashin hankali ya shiga ba, dafe kanshi da yaji yana sara mishi yayi, azuciyarshi yana cewa “Me ke shirin faruwa dani?, kar dai ‘kanwar matata uwa d’aya uba d’aya nake DAKON SO?, shikenan aure ya haramta a tsakaninmu?, nashiga uku, ya Allah gani gareka ka fitar dani daga wannan bala’i da na jefa kaina aciki, ina son ‘kanwar matata uwa d’aya uba d’aya acikin rashin sani, kai amma rashin sani YAFI DARE DUHU”. Sorry for the delay, yau dai munyi mai yawa. Sai kun sake jinmu ko gobe ko jibi, duk yanda Allah yayi dai kawai, we love you all, Allah yabar zumunci. ©Hanee da mama
Chapter 16 · 0% Book details