Sashe 14
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kai ‘kofa sannan yace “Ameen”. Yana fita ta kira Saleem ta gayamishi akan yau kam ta shirya da Sultee, shima d’in yaji dad’i don Nabila ta gayamishi duk takurata da yakeyi, sun dad’e suna hiransu sannan sukayi sallama. Da safe Amira taji mamaki ganin Nabila ta watsake sai fara’a takeyi kaman ba ita bane take kuka jiya tana cewa ta ha’kura da karatun zata koma 9ja. Bata ‘kara mamaki ba saida taga Sultee ma yafito yanata murmushi fuskar shin nan ya ‘kara kyau, Nabila ta gaisheshi ya amsa fuska asake har yana tsokanarta, abun dai gwanin sha’awa sunata hira har suka kammala breakfast sannan yace “Ni na tafi office, kaya na yana parlour ki bama driver ya kaimin laundry”, Amira ta amsa a sanyaye “Toh”. Su Nabila yau har da rakiya tayi mishi, da Amira taga haka sai ta ‘kara shiga duhu, gashi da ta tambayi Nabila sai tace mata “Kawai mun shirya ne”, bata yarda ba don tasan da wani abu a ‘kasa amma dai taja bakinta tayi shiru ta kama hanyar d’akin Sultee. Ta d’auki kayan ta juya zata fita sai idonta ya sauka akan wani takarda mai d’an girma, har ta share sai kuma wani abu yace mata ta duba taga mene aciki. Ajiye kayan tayi taje ta d’auki takardan sai ta zauna ta fara bud’ewa, first page taga anyi rubutu da capital letters “MY DIARY, MY BOOK OF SECRET THOUGHTS”, da sauri ta ajiye don tasan ba kyau le’ken asirin wani amma kuma kaman an mitsileta sai ta sake d’auka. Abun da tagani neh ya mugun tsorata ta, kuka ne ya kubce mata, tana dana sanin bud’ewar da tayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ta fara karantowa, third page yafi komai d’aga mata hankali, da kyar ta karanta sannan ta bud’e next page, ganin in ta cigaba da karantawa zuciyarta zata iya bugawa yasa ta ajiye. Kuka takeyi kaman an aiko mata da sa’kon mutuwa. Anty Jamcy mun gaisheki sosai, Allah yabarmin ke. Amrah Allah ya ‘kara basira my dear, Allah yabar zumunci. Ummitah me luv u wujiga wujiga…. Sisi Faty Axland ke ta daban ce, Allah ya ‘kara soyayya tsakaninki da Lamido, Rabi’atu S K/mashi na jinjina miki sosai. Dukkanku masu son novel nan mungode kuma muna gaisheku, ku cigaba da ha’kuri damu akan rashin typing kullum, we’re both busy saisa but zamuyi ‘ko’karin kammalawa dawuri. ©Hanee da maman Khalil SHARE THIS: Twitter Facebook Google LIKE THIS: Like Be the first to like this. RELATED GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH FEBRUARY 3, 2016 ⁄ Advertisements