← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya yarda bazata dinga renashi ba. Thursday akayi hawa, Sultee yasa kayan sarauta, yayi kyau na fitar hankali, friday kuwa Walima akayi don Gimbiya tace itakam batason bidi’a a biki, saturday misalin ‘karfe goma sha d’aya na safe dubbannin mutane suka shaida auren Gimbiya Nafisah da Yarima Sultan akan sadaki naira dubu hamsin, daga nan kuma aka wuce reception inda akayi awani babbar restaurant mai suna “Amrah’s Restaurant”. Suna dawowa daga reception Sultee ya dau wayarshi ya kira Gimbiya, a kira na farko ta d’auka, har yaji mamaki, muryarta a dishe tace “Hello”, murmushi yayi wanda sai da ta jiyo sautinshi sannan yace “Yakike?, yanzu kam an d’aura aure, kin zama mallaki na, ina fatan dai kinsan duk abinda nace kiyi zakiyi kam ko?”, jin batayi magana ba yasa ya cigaba “Na farko dai anjuma zan turo miki da kayan da zakisa a dinner, friends nah sun had’amana”, cikin masifa tace “Ni fah ba inda zanje, gwanda ma karka turo ehen”, ya d’anyi jim sannan yace “Good, in na turo Allah yasa karki sa, by 10 zamu tafi, ko baki shirya ba wallahi dole kije”, ‘kwafa tayi tace “Ohh dole ne abun?, bazanje ba!!!”, sai ta katse wayar. Ko minti biyar baiyi da gama wayar ba Amira ta shigo da kaya ta mi’ka mata tace “Ya Sultee yace na kawo miki, anjuma mai makeup zatazo sai ta miki na dinner d’in”. Batace ma Amirah komai ba illa jinjina kai da tayi alamun “Toh”. Tun 8 Sultee yagama shirinshi tsaf ya kira Amira wacce tazama kamar itace komai na bikin a waya, asanyaye take cemishi Nafisa fah ta’ki amata make up, wai ita bazataje dinner d’in ba, tsaki Sultee yaja sai yace “Okay ba matsala, ina zuwa”. Da saurinshi ya nufi d’akin Nafisa, yana shiga yaga tana kwance akan gado ta d’aura ‘kafa d’aya kan d’aya sai rigima akeyi da ita akan ta tashi ta shirya amma tace ita ba inda zataje. Sallamar Sultee yasa ta zare ido, ganin yashigo yasa gaba d’aya aka watse aka barsu su biyu, matsowa yayi kusa da ita ya zauna sannan yafara magana “Meh kikeyi da baki shirya ba?”, yasa hannu zai jawota kawai saitayi saurin mi’kewa tanufi toilet tana in-ina tace “Umm…emm..yanzu zan shiga wanka ne dama”, yanda ta tsorata dashi har ya bashi dariya, azuciyarshi yace “Ohh ashe dai duk rashin kunyarta don ba a d’aura auren bane”, cikin hanzari tayi wanka tafito, ya kira Amira akan tashigo da masu mata make up d’in, nan take kuwa suka shigo aka gyarata tsaf, duk sunji mamaki da ta yadda suka mata. 9:45 dai an shirya amarya tayi kyau abunta, Sultee kuwa yana zaune bai bar d’akin ba, da yaga ta fara gardama da ya kira sunanta sai ta nitsu. Motar d’aya suka shiga shi da ita, Amira kuwa tuni Ahmed ya ma’kale mata, shi ya d’auketa ya kaita dinner ma, Nafisa ta sake ta cashe kaman ba ita ba, bata nuna damuwa ba sam wanda hakan yayi ma Sultee dad’i, milly balalau na hango sai cin fried rice akeyi da cikinta, daga chan kuma futha da kdeey ansha wanka amma sunata yagar nama abunsu, mutane dai tirim sunje, su Jamila da Amina sune manyar ‘kawaye, sun kafa goggoro kaman masu tashi sama. Ba atashi ba sai wajen 12am, Nafisa ta ja Amina wai su shiga motar d’aya don ita yanzu mugun tsoron Sultee takeji, suna isowa bakin motar Sultee ya kalli Amina yamata murmushi yace “Umm, sorry please ki shiga wani motar daban, inaso nayi magana da amarya na”, jikin Nafisa yafara ‘bari, cikin sad’a’karwa tace “Ayyah ya Sultee kabarta, bestfriend dina ne, kaga komai tasani akaina ai”, juyowa yayi ya kalleta yace “Harda sirrinmu?”, cikin rashin fahimta Gimbiya tace “Wani irin sirri kuma?”, dariya yayi sannan ya ‘kara bama Amina ha’kuri sai yaja hannun amaryar sa suka shiga motar. A motar duk Gimbiya a takure take, gashi Sultee ya’ki sakin hannunta har suka isa gida, tun kamin driver yagama parking ta fara kiciniyar bud’e ‘kofar motar, murmushi Sultee yayi, driver ya fita ya barsu, Sultee ya ‘kara matsowa kusa da ita, kallon fuskarta yakeyi da d’an ‘karamin bakinta tanata kumbura baki, nan take yajishi cikin wani yanayi da bai ta’ba shiga ba sai ranar, ba shiri ya kama bakinta yafara kissing nata, tureshi takeyi amma ta kasa, har ya fara fita daga hayyacinshi, gashi babba kuma sabon shiga a harkar, kuma kun san ba sauki. Da kyar yayi ‘ko’karin saketa yana maida numfashi, gimbiya kuwa dagudu ta fita daga motar, ta isa d’akinta ta kwanta tafara jan tsaki “Allah ya isar min shan bakina da yayi, sai kace yasamu sweet, lallai ya Sultee ma ba ‘karamin d’an duniya bane, taci gaba da sa’ke-sa’ke har bacci ya kwasheta. Abangaren Sultee kuwa yana isa d’aki kan gado ya fad’a yana murmushi, Abdul yashigo suka gaisa sai chan Abdul yace “Abokina ya dai kaman baka daidai!,?”, murmushi Sultee yayi yace “bari kawai, yau na mallaki Nafisa, har ina Allah-Allah wednesday yayi mukoma don gaskiya ha’kuri na yakusa ‘karewa”. Kuyi ha’kuri da wannan d’in, zamuyi ‘ko’karin gamawa kwanan nan In Sha Allaaah © Hanee da maman Khalil Posted from WordPress for Androi GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® NWA da © Khadijah maman Khalil - Wasar ‘buya gimbiya keyi da Sultee, duk yanda yaso su had’u abun ya faskara don ta bar bin hanyar da tasan zata iya cin karo dashi. Ahmed da Amira kuwa soyayya sukesha abunsu, tuni Amira ta fitar da Sultee daga zuciyarta, sai fatan Allah yasa rabon Ahmed ne. Yau ya kama tuesday, an gama had’a ma gimbiya kayakinta, jere kuwa an riga da anyi tun kamin a d’aura auren a sabon gidan da Sultee ya siya. Sultee ba abinda yakeson gani irin Nafisa amma ta’ki bari su had’u, yau dai ya ‘kudiri aniyar ko ta yaya sai ya ganta. Yamma lis mai martaba ya kira Nafisa don mata nasiha, ya fara da cewa “Mama na inaso ki sani aure da kike ganin nan ba wai ha’kuri bane zalla kamar yadda ake fad’a, yes dole a saka da ha’kuri amma dai biyayya da kuma soyayya shi ke sa zaman aure yayi tsawo, duk da nasan ba soyayya kukayi dashi kamin a d’aura muku aure ba, nasan Sultan zai kula dake kuma bazai ta’ba bari ki cutu ba, kar ki mishi rashin kunya sannan duk lokacin da ya saki abu karki kuskura kice baza kiyi ba, duk abinda zakiyi a gidan aurenki ki dinga tunatar da kanki cewa Aljannarki yana ‘kar’kashin ‘kafar Sultan”, ya d’auki lokaci yana mata nasiha wanda ba abinda gimbiya ke yi sai kuka, maganar daddy ya ratsata ‘kwarai da gaske. Baba Rabi, Ammi da mummy ma sun taru sun mata wa’azi sun kuma bata shawarwari yanda zata dauwamar da zaman lafiya a gidan aurenta, idon Nafisa yayi luhu-luhu don kukan da tasha. Bayan anci dinner duk aka watse, Hauwa, Ukasha da Amira duk suka dunguma zuwa d’akin Nafisa, tana zaune tana ta tunani, ta amsa sallamarsu sai suka zazzauna. Hira sukeyi sosai sai dariya suke kwasa gwanin sha’awa, Sultee ya zo ‘kafarshi hud’u amma basu bar d’akin ba, tsaki yaja a zuciyarshi yace “Wad’annan akwai surutu, da ina zagin Nafisa akan tacika magana ashe dai surutun a jininsu yake tunda dukkansu sai zuba sukeyi”. Ammi da tazo wucewa taga Sultee ya fito daga hanyar d’akin Nafisa yasa ta doshi d’akin, tana zuwa tace “Ohh Allah, ‘karfe sha d’aya da rabi amma ku ko bacci baku da niyyar yi, oya tashi kowa ya wuce d’akinshi”, ta ‘karasa maganar tana nuna musu ‘kofa. Ukasha da Hauwa suka tashi ba don sunso ba suka musu sai da safe suka fita, Amira kuwa gyara kwanciya tayi, Ammi ta kalleta sannan tace “Ke baza kije kiyi baccin bane?”, Amira tace “A’a Ammi, anan zan kwana kawai”, Ammi ta ja guntun tsaki tace “Don Allah ki tashi tasamu tayi bacci, kinsan fah flight nasu 8 ne, zaki zauna ki cikata da surutu har ta rasa samun isashshen bacci”, Amira ta tura baki tace “Ni ba hanata bacci zanyi ba, tunda kin kore ni shikenan, sai da safe”. Tana fita Ammi ta matsa kusa da Nafisa tace “Kiyi bacci kinji?, kinga dare yayi”, “toh” Nafisa ta amsa mata, Ammi ta mata sai da safe sai ta fita ta ja mata ‘kofar. Tana fitowa ta wajen verendah na flat na Nafisa ta kusa cin karo da Sultan, ja da baya yayi da sauri yana sosa ‘keya, rusunawa yayi ya gaisheta, fuska d’auke da murmushi ta amsa mishi sai tace “Tana ciki ai, ka shiga mana”. Murmushin mara gaskiya yayi ya kasa magana, ganin kunya yacika shi ne yasa Ammi yin murmushi kawai ta wuce. Shiga d’akin yayi da sallamarshi, lokacin Nafisa ta d’aura towel zata shiga wanka, da yake ta bama ‘kofa baya shiyasa bata ganshi ba shikuma komai nashi ya tsaya cak, kallonta yakeyi kaman zai cinyeta. Rufe ‘kofar toilet da tayi ne ya dawor dashi hankalinshi, da ‘kyar ya kai kanshi kan kujera ya zauna yana jiran fitowarta, ta d’an dade kad’an sannan ta fito, bata ma lura da mutum a d’akin ba, ta bud’e wardrobe tafito da night gown wanda riga ne iya guiwa, ta gama shafe- shafe shafenta da feshe feshe sai ta saka night gown d’in, har ta hau kan gado duk bata lura da Sultee da ke neman mutuwa a zaune ba yana kallonta baki bud’e. Ta hau gado sai ta d’an mi’ka hannunta don ta kashe bulb d’in d’akin ne ta ga mutum zaune ya ‘kura mata ido, ihu ta tsala tayi hanyar parlour da gudu, ganin taji tsoro yasa ya tashi da sauri ya cafkota kar aji ihun a waje, rufe mata baki yayi asanyaye yace “Shhhh, ni ne fah”, sai sannan ta d’an nitsu amma still jikinta yana rawa. ‘kwace kanta tayi daga ri’kon da ya mata, tsaki taja tace “Shine zaka wani shigo min d’aki ka zauna ba ko sallama?, wai ma yaushe ka shigo ne?”, murmushi ya mata sannan yace “Tun kamin ki shiga wanka na shigo amma baki ganni ba sai yanzu”, murgud’a mishi baki tayi tace “Amma kuma kasan ba kyau kallon jikin mace kana namiji ko?”, kasake ya tsaya yana kallonta yana kuma jin mamakin abinda ta fad’a amma dai sai
Chapter 20 · 0% Book details