← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

toshe akan ta cire lock din ‘kofar daga ciki Bude motar da akayi neh yasata d’ago kanta,security neh ya bud’e ma Saleem ‘kofar motar,da yake baisan tana ciki ba,ji yayi an ‘kira sunanshi. Ya tsorata ya fara kiran sunayen Allah da addu’o’i,yafara ‘ko’karin balle murfin motar amma yakasa tsaba rikicewa,duk da takaicin da ya cika zuciyar Nabila bai hanata dariya ba,dariya takeyi ba kakkautawa. Jin dariyar da yayi neh yasashi saita hankalinshi waje daya,ya matso daf da ita ya taba jikinta,ya tabbatar mutum neh,d’aga kan da zaiyi saiyaga fuskar Nabila hawaye taf amma tana dariya. Wani uban tsaki yayi yace “Wai ke wace irin mutum neh?wlh kin bani tsoro,na zata ma aljana ce” Hanee da maman Khalil [6:42pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Nabila ta kasa daina dariya,da farko ya ‘kulu amma daga baya shima dariyar ya soma. Yi sukeyi kaman zararru,saida sukayi suka gaji sannan sukayi shiru. Maida numfashi kowannensu yafara sai daga baya yake tambayarta ya akayi tazo nan,tsaki taja tace “Wlh ya Sultee mugu neh”,Saleem ya tambayeta “Meh yafaru?”,nan ta bashi labarin abinda yafaru. Ai tun kamin tagama meh Saleem zaiyi in ba dariya ba,dariyan mugunta harda hawaye,Nabila kuwa tacika tayi fam,tafara masifa “Wlh ya isheka,ya zaka sakani a gaba kana min dariyar ‘yan tasha?” dariya Saleem ya sakeyi sannan yace “Ko ma mene ki fada,ko dariyar ‘yan giya neh na yarda,ba ke bakiji ba?ai ya Sultee yamin daidai wlh”,murmushin takaici Nabila tayi sannan tayi ‘kwafa tace “Wlh bashi yaci don saina rama”,Saleem yayi murmushi yace “Ya za ayi ki rama?”,hararshi tayi sannan tace “Bazan gayama ba”. Nan ya kira driver awaya yace mishi yashigo ya kaisu gida,daman yace ya tsaya awaje neh don in yaga Nabila ya kirata. Har suka isa gida dariyar junansu sukeyi Masarautar Hamaz Shirye shirye ake tayi na tarar Yarima Sultan,abinci kala-kala dai gasunan barkatai,sun sauka lafiya akazo aka daukesu daga airport. Sarkin Hamaz mutum mai mutunci,ya tarbe Sultee hannu bibbiyu wane d’an cikinshi,akazo aka gaggaisa sannan su Ukasha da Hauwa ma suka shigo,sun gaisa a mutunce sannan suka tashi suka fita daga side din da aka ma Sultee masau’ki,suna fita Hauwa tace “Ya Ukasha kana ganin wannan guy din,kyakkyawa,inama da ni aka bashi” rankwashinta yayi yace “Ji iskanci,mijin addanki zaki wani ce inama da ke zai aura,kika sake maimaita hakan saina pasa miki bakin surutun kowa yahuta” tayi fuskar tausayi tace “Ni fah wasa nake maka shine zaka rankwashen,saina had’aka da Momy(S.Fatima),nan ya shiga rarrashinta tace ita atapir bata ha’kura ba saiya kaita yawo,ba yanda ya iya haka yace taje ta shirya don yasan halin momy in dai aka ta’ba Hauwa toh akwai rikici. Misalin ‘karfe biyar Ameerah ta shiga side na Sultee, ya amsa sallamarta ba tare da ya kalleta ba,sai danne danne da waya yakeyi abunshi hankalinshi kwance,samun kujera tayi d’an nesa dashi kad’an ta zauna sannan tace “Barka da isowa ya Sultee,ina yini?”,jin ta kirashi da “Ya Sultee” yasashi d’ago kanshi bashiri don ba wanda yake kiranshi da hakan sai Nabila,kallonta ya tsaya yi yaga tana mishi yanayi da wanda ya sani amma ya kasa tuna waye,saida ta sake maimaita gaisuwar sannan ya amsa,fuska a sake yace “Na sameku lafiya?” ta sunkuyar da kai tace “Lafiya lau”,nan fah duk sukayi shiru,da yaga dai miskilanci takeji itama sai kawai ya ajiye nashi yace “I believe kinsan dalilin zuwa na nan,inaso ki gayamin meh da meh kike shiryawa zakiyi” ta d’ago fararen idanunta ta sau’kar akanshi,azuciyarta tace “Guy din kyakkyawa fah na karshe,saidai ba yaro karami bane,Allah dai yasa yanda yakeda kyaun fuska haka zuciyarshi ma yake”,jin tayi shiru kuma ta zuba mishi ido yasa yace “Ke nake jira fah,kin zubamin ido kinkasa magana”,wani kunya neh yarufe Amira don bataso ya kama ta tana kallonshi ba,sunkuyar da kanta tayi tace “Ni ba abinda zanyi illa Walima”,jinjina kai yayi yace “Okay good”. Shiru suka ‘karayi,sun dad’e a hakan sannan ta mi’ke tsaye tace “Ni zan shiga ciki,sai anjuma,ahuta gajiya”,guntun murmushi yayi yace “Thank you,saida safe”. Ta kama hanya sai d’akinta ta fad’a kan gado sannan ta sauke wani ajiyar zuciya,abangaren Sultan kuwa kwanciya yayi akan dogon kujerar dake parlourn amma kuma meh? Tunanin surutun Nabila yakeyi,yana tuna in da yana gida da yanzu tazo ta dameshi da shegen surutun ta,nan take yaji shi so bored,murmushi neh ya subuce mishi wanda ya rasa gane na mene,chan kuma yayi tsaki afili yace “Na rasa meh zanyi missing akan gida sai yarinya mai shegen surutun tsiyar nan” Hanee da maman Khalil
Chapter 6 · 0% Book details