← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma shikam yalura da akwai mutum a wajen,”yauwa” kawai yace sai ya nufi cikin babban parlour. Anci ansha,anyi wasanni duk don tarbar Sultan amma shi tun da yagama cin abinci ya tafi d’aki bai sake fitowa ba sai da dare da mai martaba ya kirashi. Nabila tana zaune da Saleem tace “Ya Saleem,amma kafi Yarima fara’a da son mutane ba kad’an ba” murmushi Saleem yayi yace “Hakane kam,kinga shi baison surutu da yawan hayaniya,ko dani fah wani lokacin neh muke hira don yacika miskilanci”. Dariya Nabila tayi tace “Aikuwa sai na sashi surutun dole”. Washegari Nabila tasaka dogon riganta ba’ki mai ratsin ja,batayi ado ba amma tayi kyau sosai,ta hada fruits a tray saita kama hanyar side na Sultee,da sallamarta tashiga,ciki-ciki ya amsa,zaune yake a kan kujera yana danne danne da laptop. Kallo d’aya yamata saiya d’auke kanshi. Ta nemi guri ta zauna tace “Ya Sultan ina kwana?” batare da ya kalleta ba yace “Lafiya”,batayi ‘kasa a guiwa ba tace “Ni sunana Nabila,ni ‘yar baba Rabi ce” still idonshi yana kan laptop nashi yace “Okay yayi kyau”. Taji ba d’ad’i kam amma haka ta fara zuba mishi surutu,tun yana amsa mata sama-sama har ya daina. Nabilah ta d’anyi shiru,azuciyarta tace “Kyakkyawa amma sai uban miskilanci,ko don yaga yanada kyau neh oho”,chan tace “Ya Sultan,ni inason naje Qatar,kabani labarin garin”,cikeda ‘kosawa ya bar danna laptop din,ya d’ago ya kalleta yace “Don Allah tashi ki tafi,kin cikamin kunne da surutu har kaina yafara ciwo”, zata sake magana kenan ya d’aga mata hannu yace “Please go” GIMBIYA NAFEESAH [2:52pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Duk zafin da zuciyarta yayi sai tayi ‘ko’karin dannewa,ta tashi a sanyaye tace “Kayi ha’kuri in na ‘bata ma rai,it wasn’t my intention”,ko ci kanki baice mata ba, itama dama bata sa ran zai bata amsa ba,juyawa tayi acikin tafiyarta mai fizgar hankali ta fita daga side din. Tana fita ya bi bayanta da kallo,azuciyarshi yace “Masha Allah,tana da kyau ba laifi gashi komai ya ji enough”,murmushi yayi afili, dasauri yayi Istighfari ya kawar da tunanin daga ranshi sannan ya ci gaba da aikin da yakeyi a laptop nashi. Abangaren Nabila kuwa tana fita daga side din lambu ta wuce,tana isa kuwa taga Auta zaune a wajen yana waya,samun wuri tayi ta zauna,kallonta da Auta yamata yasa yagane tana cikin damuwa duk da kuwa ta saka fake smile a fuskarta,katse wayar yayi. Arikice yafara tambayarta “‘kanwata wa ya ta’baki?” girgiza kai tayi,tayi ‘ko’karin maida hawayen da ke nema ya zubo mata,murmushin da akace yafi kuka ciwo tayi tace “Ba komai ya Saleem,kawai tunda na tashi bana jin dadin jikina neh”,kallon tuhuma yabita dashi yace “Yaushe muka fara wasar ‘boye-‘boye dake?”,kanta a sunkuye tace “Gaskiya na gayama”. Tashi tsaye yayi yace “Okay toh sai anjuma tunda bazaki iya gayamin matsalarki ba”,d’ago ido tayi taga fuskar nan tashi a had’e alamun ya ‘bata rai. Hanee OHW da maman Khalil [3:13pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Dasauri ta mi’ke tsaye,ganin yajuya zaibar wajen yasa tayi saurin ri’ke hannunshi tace “Yi hakuri,zan gayama”,murmushi yayi sannan ya maida idonshi kan hannunshi da ta ri’ke,ai ba shiri ta sake hannun cike da kunya don ita bata ta’ba ko da wasa neh ta ri’ke mishi hannu ba saidai in mistakenly hannunsu ya gugi juna,rufe fuskarta tayi,Saleem ya gyara tsayuwarshi yace “Uhum,ina jinki”. Ahankali ta janye hannunta daga fuskarta tace “Ba yaya Sultee bane”,sanin halin Sultee yasa Saleem ya zaro ido yace “Meh yamiki?” Samun wuri tayi tazauna,tafara “kawai fah don naje na gaishe shi saina zauna nafara mishi hira shine yace wai nacika surutu kuma ina sa mishi ciwon kai sannan ya koreni daga d’akinshi” dariya Saleem yayi sosai har saida Nabila ta ‘kulu,saida yayi mai isarshi sannan yace “Meh ya kaiki?kema dai baki jin magana wlh,ba na gayamiki baison surutu ba?”,guntun tsaki Nabila taja tace “Yo ni ina ruwana,ba dai naje ba?” zama Saleem ma yayi sannan yace “da zaki bi shawara ta da kin bar shiga sabgar Ya Sultee don in kin kaishi bango wlh zai iya dakaki” zaro ido tayi ta dafe ‘kirji tace “Duka???” jinjina kai Saleem yayi yace “kwarai kuwa”. Nabilah ta d’anyi jim kamar mai tunani sai chan tayi murmushi tace “Ya Saleem kasan meh?” girgiza kai yayi alamun a’a saiyace “Sai kin fad’a”,wani murmushi Nabila ta sakeyi tace “Kasan bana rantsuwa akan banza ko?” kallonta yayi sannan yace “Eh”,Nabilah tace “toh wallahi tallahi kaji na rantse ko ya Sultee kasheni zaiyi saina je side nashi kullum don hira,kai ko baya tankani zanje na zauna nayita surutu,watarana shi da kanshi zai fara surutu”. Kallon Nabila yayi cike da mamaki yace “In dai haka neh kam toh wlh kin d’auka ma kanki aiki ja,zakije kita magana ke kadai in ya gaji kuma ya koraki,amma daga yau in ya sake koroki ko yamiki duka kuma kika gayamin Allah dariya zan miki tunda ke bakijin magana”. Murgud’a mishi baki tayi tace “Ehh naji d’in,meh ruwanka? ai ni nace zan yi kuma naga zan iya neh saisa,nidai kar wani ya sake gayamin maganar banza”,murmushi yayi ya tashi tsaye yace “Masifa kike ji kenan,bani na ta’boki ba amma zaki sauke haushi akaina,barin tafi kamin ki rufeni da duka” ya ‘karasa maganar yana dariya,itama dariyar tayi tace “Kai ya Saleem,wasa fah nakema,kayi ha’kuri don Allah”. Dawowa yayi ya zauna suka cigaba da hirarsu sunata kyakyala dariya gwanin ban sha’awa Haka dai kullum safe,rana da dare Nabilah tana zuwa side na Sultee tayita surutu shikuma ko sannu baya ce mata,in ya isheshi neh sai ya koreta Hanee da maman Khalil [3:41pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bayan Sultee yayi kwana biyu sai mai martaba ya ‘kirashi da dare. Sun d’an ta’ba hira irinta tsakanin d’a da mahaifinshi,chan sai mai martaba yace “Yarima,yaushe kake shirin zuwa ka dubo matarka?” cike da rashin fahimta Sultee yace “Bangane ba abba,mata kuma?”,murmushi yayi yace “Amirah nake nufi,wanda za ayi aurenku nan da wata daya and some weeks”,sosa ‘keya Sultee yayi yace “Eh toh,daman cikin satin nan nakeso naje”,mai martaba ya jinjina kai yace “Hakan yayi,amma da jirgi zaka je ai ko?don ni gaskiya ban cika son kuna dogon tafiya a motar ba” murmushi Sultee yayi yace “Duk yanda kace abba,bani da ja”. Har dare yayi nisa sannan Sultee yayima mahaifinshi sallama yakoma d’akinshi. Yau ya kama asabar kuma yau neh yarima Sultan zai tafi Adamawa wajen Gimbiya Amirah,duk da shi har cikin ranshi ba son auren nan yake ba amma sabida biyayya haka ya daure,fuskar nan tashi ba yabo ba fallasa da yake shi baicika dariya har chan ba saisa ba wanda zai gane ko farinciki yakeyi ko akasin haka. Abangaren Gimbiya Amira kuwa zaune take akan lumtsumemen gadonta acikin d’akinta wanda yaji kayan alatu,tana ri’ke da hoton wata yarinya ‘karama da bazata wuci 6 years ba tana shafawa,a hankali take magana “Lil sis,ina kika shiga? We so much miss u,ina matu’kar bu’katar ganinki,gashi yau zan hadu da wanda zan aura amma bakinan,dis place has never been same since u went missing” nan ta fara hawaye,S. Maryam ce tashigo wacce suke kira da ammi,ahankali ta tako har zuwa inda Amirah take zaune,saka hannunta tayi ta kar’be hoton,kar’be hoton da akayi neh yasa Amirah dago kanta,da sauri tashiga share hawayenta,ammi ta rungumeta tashiga bubbuga bayanta tace “Yi ha’kuri Amira,inaji a jikina Nafisa tana raye kuma In Sha Allahu zata dawo wajenmu ko ba jima ko ba dadewa,dukkanmu muna kewarta amma kuka ba shine mafita ba,addu’a ya kamata mu ci gaba dayi har Allah ya bayyana mana ita. Amirah ta tsagaita kukanta tace “Nagode ammi”. Nan dai ta dinga bata baki har tabar kukan sai ajiyar zuciyar da takeyi,da kyar ta lalla’bata tayi wanka sannan S. Maryam ta chanchara mata ado,dama ammi ba baya ba wajen iya kwalliya,Amira tafito fes da ita. Da azahar Sultee na airport don zuwa land of beauty,ni da maman K muma ba a barmu abaya ba don dukkanmu trolley d’ad’d’aya muka cika bem da kaya,Saleem da Nabee sune sukayi rakiya har airport din,a airport uwar surutu Nabila sai damun Sultee takeyi,shi duk haushinta neh ma ya cikashi,da abun ya isheshi saiya dubeta yace “Zo inason magana dake”,su Nabee sai zumudi akeyi ta tsamman wani maganar arziki neh,shiga motar yayi itakuma ta zagaya ta d’ayan ‘kofar tashiga,tana shiga shikuma ya fito da wayarshi kaman meh answering na call sai yayi murmushi yace “Inazuwa”,tayi fari da ido tace “Toh”. Yana fita daga motar ya danna car lock ajikin key din sannan ya juya ya koma inda yake tsaye kafin lokacin tashin jirgin. Hanee da maman Khalil [6:02pm, 18/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Saleem yaji wajen yayi shuru sai ya juya ya duba baiga Nabilah ba,nan ya hau tunanin ko ina taje don lokacin da Sultee yajata motar Saleem ya d’anyi gefe don amsa call. Nan Saleem yashiga trying na numbanta amma unfortunately ta ajiye shi acikin bag nata kuma bag din yana ajiye akan seat da ta zauna,a rikice ya taka zuwa wajen Sultee yace “Ya Sultee kaga Nabila neh?”,ko d’ago ido baiyi ba,ya fuske kawai abunshi sai chan yace “Wacece Nabilah kuma?”,kallonshi Saleem ya tsaya yi cike da mamaki sannan yace “‘yar baba Rabi”,nan neh Sultee ya d’ago idonshi yace “Saleem i have no idea gaskiya,kadai dubata maybe taje wani waje neh”. Sunkai minti goma sannan akayi announcing kowa yashiga jirgi,sannan neh ya mi’ka ma daya daga cikin drivers din key’n motar da ya kulle Nabila aciki, securities da zasuyi tafiyan da shi suka kinkimi trolleys nashi,muma dai muna biye dasu. Sun shiga jirgi kowa yasa belt,na juya wajen maman K dake zaune ta window nace “Maman K yau zakije kiga garinmu” murmushi tayi tace “ki bari kawai Hanee,duk na ‘kosa naga mun isa”,dariya nasa mata ganin irin d’okin da takeyi zata Yola. Nan jirgi ya d’aga cikin sararin samaniya,sai fatan Allah ya kaimu lafiya Abangaren Nabila kuwa tunda taji yasa key ba abinda takeyi sai kuka,gashi motar tinted ce ba wanda yaganta aciki,gaba daya tunaninta ya toshe,daga baya ta had’a kai da guiwa kawai tana hawaye da Allah wadai da mugun hali irin na Sultan,gaba daya basirarta ta
Chapter 5 · 0% Book details