Sashe 19
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daddy yace anjuma da daddare duk su sameshi a parlour. Amira tana fita daga parlourn ta wuce d’akinta, fashewa tayi da kuka, zuciyarta yana mata zafi sosai, tana jin son Sultee har cikin ‘bargon jikinta saidai tasan dole ta ha’kura dashi tunda Nafisa yakeso, ta gwammaci ta rasashi gaba d’aya akan su zauna a ma’aurata amma baya sonta, tayi kuka sosai sannan ta tashi ta d’aura alwala ta hau nafila tana ro’kon Allah ya cire mata son Sultee daga zuciyarta. Sultee kuwa yana komawa d’aki tausayin Amira ya lullu’beshi, yasan ya zalunce ta duk da ba laifinshi bane. Yamma lis Amira ta sami gimbiya a garden tana zaune tana shan fruits, zama tayi a gefenta. Nafisa ta dubeta taga damuwa a tattare da ita, cike da kulawa ta hau tambayarta “Anty, me ke damunki?, baki da lafiya ne?, ko an ‘bata miki rai ne?”, girgiza kai Amira tayi tace “Ina neman alfarma a wajenki sis, ke kad’ai ce zaki iya taimakona, nasan bazaki ‘ki ba saisa na zo ro’karki”, Gimbiya ta d’anyi jim sai tace “Ba komai sis, duk abinda kike nema daga wajena ni mai baki ne, ke kad’ai fah gareni, ina jinki, gayamin”, murmushi Amira tamata sannan tace “Inaso in daddy ya kiraki akan kin yarda ya Sultee ya aureki kice mishi eh”, dafe ‘kirji Gimbiya tayi da sauri ta mi’ke tsaya tace “Anty ya Sultee fah kikace, mijinki”, Amira tace “Ehh shi dai”, Gimbiya tace “Ai ba aure tsakaninmu tunda ke yake aure”. Amira tace “Akwai!, nan ta mata bayani kaman yanda tayi ma su daddy, nan take kan Gimbiya yafara juyawa, zama tayi da’bas a cikin lallausan grass carpet da ya zagaye garden din, azuciyarta tace “Noo, ya Sultee?, he can’t be my husband, yamin girma, noooo!!!!”, nan wata zuciyar kuwa tace mata “Haba Nafisa, ita kad’ai ce addarki, ki tuna fa tun kamin tasan ke ‘kanwarta ce take kula dake kamar ‘yar uwarta, ai koma me ta ro’ka daga wajenki ya kamata ki mata”. Amira ta sau’ko daga kan kujerar da take zaune, ta zauna dab da Gimbiya, dafa kafad’arta tayi tace “Ba komai in har baza ki iya ba, karki damu, nagode”, tana kaiwa nan sai ta tashi tana share hawaye. Dasauri Gimbiya ta ri’ko hannunta, ba tare da ta juyo ba tace “Sis Allah ba komai, ba sai kin takura kanki ba”, hawaye Gimbiya takeyi sosai, cikin muryar kuka tace “Kinfi ‘karfin komai a wajena, wallahi na amince in har hakan zai faranta miki rai”, juyowa Amira tayi ta rungumeta suna kuka, sun dad’e ahaka sannan Amira ta zaunar da ita ta ‘kara mata ‘karfin guiwa akan don Allah ta amince in daddy ya tambayeta, ahaka suka rabu. Bayan Isha duk suka hallara a wajen daddy, sun d’an ta’ba hira sai daddy ya gyara zama yace “Yanzu dai inaso agama maganar nan kowa ya huta”, ya kalli Gimbiya yace “Mamana, Amira tazo min da wani magana wanda na’ki amincewa don nace sai in dukkanku biyu ke da Sultan kun yarda”. Atare zuciyarta da na Sultee ya buga, Saleem kuwa bai san dawar garin ba sai ya gyara zama don jin bayani, daddy ya gayamusu ‘kudirin Amira, Saleem mutuwa ne kawai baiyi a wajen ba amma idonshi yayi jawur, nan wani zuciyarshi yace mishi “Me na damuwa?, kai takeso ai tunda basu shiri da ya Sultee”, maganar daddy ne ya katse mishi tunani, daddy yace “muna sauraronku, Sultan ka amince?”. D’agowa yayi ya kalli Gimbiya wacce itama a lokacin shi take kallo, sau’kar da kanta ‘kasa tayi da sauri, ya maida dubanshi zuwa ga Amira wacce idonta yayi ja tsaba kuka, murmushi ta mishi alamun yayi magana, a hankali yace “Na amince daddy, in har hakan ne zai sa Amira farin ciki, ban ‘kullace ta ba kuma bazan ta’ba ‘kullatarta ba don tamin biyayya fiye da tunanin mutum”, jin Sultee ya amince yasa Saleem fara zufa. Daddy ya girgiza kai yace “Mamana ke fa?”, kallon Amira tayi sai taga bazata iya cewa a’a ba, cikin ‘karfin hali da muryar kuka tace “Na yarda daddy”. Nan take wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Saleem, yayi nadamar jinkirta gayama Nafisa sonta da yakeyi, daman ance “abari ya huce shi ke kawo rabon wani”. Gaba d’aya parlourn yayi shiru sai sautin kukan Nafisa da Amira ke tashi, a tunaninsu dad’in Nafisa ta amince ne yasa Amira kuka, basu san tana kukan ta rasa masoyinta har abada bane, Gimbiya kuwa kukanta tanayi ne don batasan wani irin zama zasuyi ita da Sultee ba. Daddy ya sau’ke ajiyar zuciya ya dubi Amira yace “Shikenan kuka ya ‘kare ai, sun amince, hankalinki ya kwanta”, murmushin dole Amira tayi sannan ta mi’ke ta d’auki paper da biro ta isa wajen Sultee, cikin ‘karfin hali tace “Sai ka cika aiki”, jiki ba ‘kwari Sultee ya ‘karbi papern ya rubuta mata saki uku cif sannan ya mi’ka mata, murmushi tamishi tace “Nagode ya Sultee”, Sultee baisan time da hawaye suka zubo mishi ba. Kowa da abinda yake sa’kawa, Amira ta kalli daddy tace “Daddy yaushe za asa date?”, daddy ya d’anyi jim sai yace “Sai nayi magana da abbanku(sarkin Yura) tukunna”. Daddy ya kira Abba washegari suka gama maganar date d’in bikin, da yake ya riga ya gayamishi abinda Amira ta ro’ka kuma shima yace in har sun amince ba matsala. Sun saka date nan da 1 month don hutun Nafisa ya kusa ‘karewa. Daddy ya kirasu ya gayamusu, Sultee dad’i yakeji sosai kaman an mishi albishir da Aljannah, Nafisa ma dai ta d’an sake kad’an but saidai ba kamar da ba don ita tana ganin abun bambara’kwai wai ace tayi soyayya da Sultee, Amira da Saleem kuwa duk sun maida lamuransu zuwaga mai dukka Allah. Bayan kwana uku Sultee da Saleem suka koma Yura, nan fah aka kama shirye shiryen biki, d’okin da Sultee yakeyi har ya bama Abba mamaki yasoma zargin ko dai tun dama wannan yaron yana son Nabila(Nafisa) ne? Amma dai ya barma zuciyarshi batun. Ahmed da Abdul da yake sun san komai game da son Nafisa da yakeyi sun tayashi murna sosai, da yamma yana waya da Ahmed sai yake ce mishi “Sultan ni fah gaskiya ina son Amira ba tun yau ba, ko zakamin hanya ne?”, Sultee cike da mamaki yace “Kamar ya ba tun yau ba?, kana nufin ka dad’e da kamuwa da sonta?”, murmushi Ahmed yayi yace “I’m serious, ina ranar da muka je gidanka muka samu tana viewing Nafisa tana rawa sannan daga baya tafito muka gaisa?, to wallahi tun time din na ganta ta mugun fizgata, na dai danne ne kawai don nasan haramun ne abinda zuciyata yake raya min”, tsaki Sultee yaja yace “Wato kai dama kallon matan mutane kakeyi ko?, Allah yasoka ma ba Nafisa ka kare ma kallo haka ba, but Amira matata ne before so na yafema kallonta da kayi”, dariya Ahmed yayi yace “Shege, kanason Nafisa har yayi yawa fah, ni dai yanzu ka bani number Amira inaso na mata magana”, Sultee ya amsa da “Okay ba matsala, zan turoma amma please kar ka ‘kara kallon matar mutane, ba kyau”, Ahmed yace “Toh nagode abokina, ina jiran number din”, sun d’an jima suna hira sannan sukayi sallama. (Tohh fah kunji, abokai ‘kare ma matan abokai kallo sukeyi, in ya zama dole afita agaisa toh a zumbula hijab babba wanda bazai nuna surarki ba, Allah yasa mudace). 2 weeks to biki aka kai kayan aure, size nata na bra da pant duk Amira ya tambaya ta gayamishi don ya tambayi Nafisa awaya amma tace mishi ita batasani ba, batason iskanci. Kayan aure yayi kyau sosai don ba ‘karamin kud’i Sultee ya kashe ba. Tun wednesday Sultee ya dira a Hamaz dashi da friends nashi da kuma ‘yan uwa da abokan arziki, tsakaninshi da amaryarshi kuwa ba wani hirar kirki sukeyi ba, kullum sai ya kirata amma in ta d’auka sai ta yi shiru, yayi ro’konta har ya gaji daga baya ya ha’kura tunda dai takusa zama mallakinsa zama ta sanine. Around 9 yana waya da wata childhood friend nashi(Safiya) yanata dariya sai kawai yaci karo da Gimbiya wacce ta biyo ta hanyar don zuwa wajen Ammi, tana d’aga kai taga Sultee ne sanye da farar shadda, yayi kyau sosai, bata mishi magana ba saita bi ta gefenshi da niyar wucewa, ri’ko hannunta yayi sannan yayi sallama da Safiya. Janta yayi zuwa wajen kujeru ata ‘kar’kashin bishiya suka zauna, sai tuttura baki takeyi ita adole bataso. ‘Kare mata kallo yayi sannan yaja tsaki yace “Yanzu da d’an iskan kayan nan kike yawo acikin gida?, karki manta fa akwai maza agidannan, ga dogarai ko ta ina, gaskiya ni ban yarda kina yawo ba hijabi a tsakar gidan nan ba”. A tsiwace tace “Ai a gidanmu nake ba gidanka ba, kayan da naga daman sawa zansa”, “haba sis, bazaki bar rashin kunya ba?, by saturday dai fah in an shafa fatiha shikenan”, maganar Amira ne ya katse mishi ansar da yayi niyan ba ma Gimbiya. Sultee ya furzar da iska mai cike da ‘bacin rai yace “Sis ki mata magana kam, gaba d’aya fa ta rainani, tana ganin kaman ni sa’anta ne, ko wayana fah bata d’agawa tsaba rashin kunya da ke yawo a kanta, amma barni da ita, zan sauke mata su, Allah ya kaimu saturday”, mi’kewa tsaye yayi, Amira ta tsaidashi tace “Please ya Sultee kayi ha’kuri, kasan yarinta yana damunta amma zan mata magana, kaji big bro?”, murmushi yayi sannan yace “Thanks lil sis”. Amira ta koma ta ja hannun Gimbiya, basu tsaya a ko ina ba sai d’akin baba Rabi, wasu magunguna ta bata wai tasha, ba don taso ba haka ta dinga shansu d’aya bayan d’aya. Chan sai Amira tace “Umma(baba Rabi), ‘yar kin nan bata jin magana wallahi, ya Sultee fah take ma rashin kunya, kuma agaba na yamata magana akan ta dinga saka hijab in zatayi yawo a tsakar gida tunda akwai maza sosai amma bud’ar bakinta sai tace mishi abinda taga daman sawa shi zata sa”, baba Rabi ta kama baki tace “Haka kika mishi Nafisa??, bakisan namiji ba a mishi haka ba ko?, shi ne fa zai aureki karki manta”, Gimbiya ta had’a fuska ita adole an ‘bata mata rai, baba Rabi ta dinga mata nasiha har dai ta sau’ka tace in