← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajenta har yana neman fad’uwa tsaba sauri, dama dogari da cin zali balle an bashi order, tunkud’eta yayi yace “ke matsiyaciya, tashi ko na buga miki sandar nan na kaiki lahira”, bashiri ta mi’ke amma ko alamun nadama bata nuna ba, sai ma wani murmushin mugunta da tayi ta yi waje dogari yana ‘kara zungurar kanta yana dukanta da dorina. Duk parlourn jimamin abun sukeyi, ammi ta ja girgiza kai cike da takaici tace “Kai amma d’an Adam ba a mishi, ba abinda bamu mata- abinci, sutura, kud’in kashewa, amma tsohuwa da ita maimakon ta koma zuwaga Allah amma ina!! tana ‘kara loda ma kanta wasu zunubbai, Allah ya karemu daga sharrin zuciya”, gaba d’aya aka amsa da “Ameen”. Daddy ya kira Nafeesah (Nabilah) yace “zo ‘yata”, da sauri ta isa wajenshi, ka ma ta yayi ya rungumeta sosai, ita dad’i ne ya cikata yau gata a gaban iyayenta na asali duk da achan baya ma batayi maraicin rashin iyayenta ba tunda Baba Rabi ta zame mata uwa da uba. An yi hira cike da raha kaman ba abinda yafaru, yau gidansu yacika full house, dad’i kam ba za a fad’eta ba, gaba d’aya family sai da sukaji batun ganewar Nafeesah acikin daren nan, Saleem yayi murna sosai don yana ganin ta kwana gidan sau’ki tunda dai ‘kanwar Amira ce, Amira kuma matar Sultee ce. Har wajen biyun dare suna hira, Abba ne ya duba agogo, atake ya mi’ke tsaye yace “Hira yayi dad’i mun manta da time ya tafi, ya kamata a shiga bacci haka ai ko?”, daddy ya duba time yayi murmushi sai yace “Hakane fah, kaga Nafeesah ta dawo mana da farin cikin familynmu”, duk sukasa dariya sannan sukayi sallama da juna. Hauwa, Amira da Nabila a d’aki d’aya suka kwana, abun gwanin sha’awa, basuyi bacci ba sai bayan sunyi asubah. Abangaren Sultee kuwa yana komawa d’aki ya zube a kan gado, tunanin mafita yakeyi har baisan time d’in da hawaye ya soma zubo mishi ba, daren ranar shima dai baiyi bacci ba. Saleem kuwa yasha baccinshi hankalinshi kwance don a ganinshi ya samu Nabila ya gama. Washegari tun da sassafe ba ‘ki masu taya murnar dawowar Nafisah suka fara zuwa, da yamma aka had’a Walima akayi wa’azi sosai mai shiga jiki wanda malamar tayi magana akan son zuciya har ya kai mutum ga hala’ka, kaman yanda yazo a hadisi “Akwai wani ga’ba ajikin mutum in har ya gyaru toh dukkan jiki ya gyaru, in ya ‘baci kuma dukkan jiki ya ‘baci, wannan ga’ba itace ZUCIYA”, ta kuma yi addu’ar Allah ya karemu daga son zuciyar da zaisa mu sa’ba ma Allah, taro ya watse wajen maghriba, aranar kuma Abba da Yabi suka bi jirgin dare suka koma garin Yura, baba Rabi taso ta bisu amma Nafisah ta sa kuka wai ita abar ummarta anan, nan take Daddy ya ro’ki Abba akan ya bar baba Rabi tadawo Hamaz da zama tunda Nafisah tanaso, a wajen kuwa Abba ya amince. Baba Rabi tayi murna ta gode ma Allah da yasa ta had’u da mutane masu halacci. Bayan kwana uku Sultee ne kwance a d’akinshi, tunani yakeyi har baisan a fili yake magana ba “Ya Allah ka bani mafita, inason Nafisah sosai, in har ban sameta ba zan iya rasa rayuwa ta”, ya fashe da kuka kaman ‘karamin yaro “Gashi uwa d’aya uba d’aya suke da Amira, nasan na rasa Nafisah har abada”. Amira da tashigo d’akin don tanaso suyi magana akan diary da tagani sai ta tsaya tana sauraronshi, tunani ta shiga yi azuciyarta “Nasan ko da Nafisa bata son Sultee nan gaba zata soshi tunda dai shi yana sonta ahankali zai koya mata sonshi, kums yana da qualities da kowace mace zataso ta samu a matsayin miji”, chan sai tayi murmushi ta ‘karasa kan kujera ta zauna, har lokacin Sultee bai ma san ta shigo ba, ahankali ta kira sunanshi “Ya Sultee, Ya Sultee”, dasauri ya juyo, ganin ita ne yasa ya wayance ya share hawayen dake fuskarshi sai yace “Yaushe kika shigo?”, dariya tayi tace “Tun d’azu amma kai baka sani ba don ka tsunduma acikin kogin son Nafisah”. Kallonta yayi cike da mamakin abinda yafito daga bakinta, murmushi tayi tace “Don’t be surprised, nasan komai fah”, nan ta bashi labarin diary’nshi da ta karanta pages 1-4 da kuma abubuwan da taji yana fad’a yanzu sai ta ‘kara da cewa “Ya Sultee, ni mai iya giving up abinda nake so ne akanka tunda dai ita kakeso bazanso na kasance katangar da ya hanaka aurenta ba, kuma kaga bazanso rabo ya kasheni ba”, ta ‘karasar da maganar tana dariya, sai ta ‘kara “akwai shawarar da zan bayar inhar mukayi hakan toh i guarantee you inhar Nafisah neh ka aureta ka gama, ajiyar zuciya Sultee yayi sannan yayi murmushin ciwo yace “Hmmm, nasan kina fad’ar haka ne don ki kwantar min da hankali amma there’s no way da hakan zai faru”. Kallonshi tayi tace “Just listen to me”. Ku biyomu don jin wani shawara ne wannan, shin akwai wani hanyar da Amira da Sultee zasubi har Sultee ya auri Nafisa wacce suke uwa d’aya uba d’aya alhalin ita Amira tana raye?. Zamu baku amsoshin nan in har kuna tare damu. 07053072615 ©Hanee da maman Khalil SHARE THIS: Twitter Facebook Google LIKE THIS: Like Be the first to like this.  RELATED GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH FEBRUARY 10, 2016 ⁄ Advertisements GIMBIYA NAFEESAH GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ® NHW da © Khadijah maman Khalil - Amira ta nisa sannan tace “Zan je nasamu Daddy nace mishi banida lafiya ta fannin mu’amalar auratayya, bana jin sha’war komai, duk zaman da mukayin nan zaman ha’kuri kakeyi dani, ba abinda ya ta’ba shiga tsakaninmu don ko hannuna baka ta’ba ri’kewa ba sannan zance inaso ka sakeni ka auri Nafisah tunda aure tsakaninka da ita bai haramta ba, kuma exact thing da zan gayama Nafisah kenan, kaima in ya kiraka ka san abinda zaka gayamishi yanda zai yarda”, kallonta yakeyi baki bud’e yana jinjina irin son da take mishi da kuma Nafisah har zata iya hana kanta abinda takeso don ya samu farin ciki, hawaye ne ya sauko daga idanunshi, yace “Anya kina ganin hakan zaiyi?”, jinjina mishi kai tayi tace “Ofcourse, wait and see”, sai ta mi’ke ta nufi parlourn daddy. Ta sameshi yana zaune da Ammi da mummy suna hira, ta mishi sannu da rana sannan tace “Daddy inaso na ro’ki wani alfarma a wajenka, don Allah karka ‘ki amince min, ko da na mutu inaso wannan ya zama wasiyya na”, daddy ya dubeta a rikice yace “Whatt!!??, me kike fad’a ne haka?, me kike so na miki?, ki fad’i koma menene namiki al’kawarin zanyi in Allah ya yarda”. Sunkuyar da kai tayi sai tace “Daddy, inaso ya Sultee ya auri Gimbiya(Nafisah)”. A razane duk suke kallonta, mummy a birkice tace “Kinada hankali kuwa?, mijinki ne fah na tsawon shekara d’aya, kina a raye kuma kina cewa ya auri Gimbiya?, ‘kanwarki sakike ne fa”, share hawaye Amira tayi ta mai da dubanta zuwa ga daddy, cikin sanyin murya tace “Daddy karku tsamman banda hankali, wallahi babu abinda ya ta’ba shiga tsakanina da ya Sultee”. Ammi tace “Ehhh!??!, kamar ya?, kallonki ya tsaya yi har tsawon lokacin nan?”, Amira tayi ya’ke tace “Wallahi ku yarda da magana na, duk zamanmu ha’kuri yakeyi dani don ko hannuna bai ta’ba ri’kewa ba, ba wai don bana sonshi ko baya sona ba, matsalar daga waje na ne, nasan banida lafiya don har asibiti naje aka bani magunguna, na d’auki alha’kin shi da yawa duk da bai ta’ba nunamin ba, ta hanyar nan ne kawai zan iya saka mishi”, ta ‘karashe maganar tana kuka sosai. Gaba d’aya parlourn jikinsu yayi sanyi, nan take daddy ya tura akira mishi Sultee, batare da ‘bata lokaci ba kuwa ya zo parlourn. Nan daddy ya tambayeshi “Sultan, duk tsawon zamanku a matsayin ma’aurata kai da Amira kun ta’ba samun matsala ne?”, girgiza kai Sultee yayi yace “A’a daddy, wani abu ne ya faru?”, ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan ya maida dubanshi wajen Amira, a hankali yace “Gayamishi abinda kika gayamana yanzu”, nan kuwa Amira ta koro ma Sultee bayani kaman yanda ta ma su daddy, sunkuyar da kai yayi ya kasa cewa komai, ganin haka yasa daddy yace “Gaskiya ta fad’a?, in har haka ne karka ‘boyemin komai, ka d’auke ni a matsayin mahaifinka ba mahaifin Amira ba”, cike da kunya Sultee yace “Haka ne daddy, ba abinda ya …..”, sai kuma yayi shiru ya kasa ‘karasarwa. Furzar da iska Daddy yayi sai yace “Amma all this while mesa duk cikinku ba wanda ya tinkare mu da maganar?, ba kasan cutar kanka kayi ba?, ka girma Amira kuma ka fita hankali da hangen nesa, in ita bata fad’a ba don ita ke da matsala ai kai zaka fad’a tunda lafiyarka kalau kuma shekaru sun ja”, ahankali Sultee yace “Ayi ha’kuri daddy”. Daddy ya mishi nasiha sosai sannan yace ya tashi ya tafi. Har ya fita daga parlourn sai Amira tace “Daddy, ya batun maganar aurenshi da Gimbiya?”, daddy afusace yace “Baki da hankali ne, don ke kin yarda ya auri ‘kanwarki an gayamiki shi zai yarda ne ko ita mamana (Gimbiya) zata yarda?, banason sake jin maganar nan daga bakinki, gobe zaki shirya Ammi’nku ta kaiki asibiti”, zaro ido Amira tayi sai ta fashe da kuka mai karya zuciya, cikin kuka tace “Yanzu daddy wannan abu d’ayan baza a iyamin a gidannan ba?, in da Gimbiya ce ai da ba abinda zatace tanaso ayi kuma a’kiyi, don Allah daddy ka taimaka ma rayuwa na ka yarda ya Sultee ya aureta, wallahi nasan ba za a samu matsala ba”, jikin daddy yamutu sosai, ya sauke ajiyar zuciya yace “Ba haka bane Amira, da ke da Nafisa duk d’aya kuke a wajenmu, na yarda amma bisa sharad’in in har d’ayan su bai amince ba toh fah maganar ta watse”. Nan take Amira ta share hawayen idonta sannan tayi murmushi ta rungume daddy tace “Nagode daddy, In Sha Allahu zasu yarda tunda suna sona kuma ai alfarma zasu min”, daddy ya d’an bubbuga bayanta yace “Ni dai na gayamiki, in d’aya bai yarda ba toh sai dai kiyi ha’kuri”, mi’kewa tsaye tayi ta ‘kara mishi godiya tana d’an hawaye,
Chapter 18 · 0% Book details