← Book details Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 23

Sashe 23

Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

mutum, azuciyarshi yace “Aure rahma ne”, yayi ta jinyarta har ta warke suka cigaba da soye wansu. Kullum maganarshi d’aya- “Babyna inason yara, Allah yasa nayi ajiya a cikinki”, ita kuma sai dai tayi murmushi tace mishi “Allah ya kawo ya Sultee”, cikin ikon Allah kuwa ko 3 weeks basuyi da daidai tawa ba ta fara laulayin ciki, gwajin farko likita yace tana da ciki, Sultee yayi sujudul shukr ya dinga kwararo godiya ma Allah, aranar both families saida suka ji batun cikin, Nafisa kam abun ya soma bata kunya har ta dinga mishi complain “Haba ya Sultee yanzu shi ne zaka bi ka bazani a dangi cewa inada ciki?, kai ko kunya baka ji?”, had’e fuska yayi yace “Abun murna ne ai babyna, meh na kunya aciki tunda dai ni ne ubanshi?, lallai har yanzu yarinta yana damunki”, cike da kunyar maganarshi ta kai mishi dukan wasa tace “Ni don Allah kabari, Allah kana sa naji kunya”, dariya yayi ya dinga lallashinta yana gayamata yanda yakeson ta da kuma unborn babynsu. Sabuwar shafin kulawa ya bud’e mata, tare suke aikin gida sannan every evening su fita strolling ta arean anguwansu, kwana biyun su da fara fita har ta saba da neighbours nata su biyu amma ba ‘yan africa bane, da turanci suke hiransu kullum. Lokacin bikin Amira Nafisa tazo da ‘karamin cikinta mai 3 months and some weeks, bini-bini Sultee zai kirata ya tambayeta ya take da babynshi, mutane har dariya suka soma musu shikam ko a jikinshi. Anyi biki an watse, amarya a Manchester zata zauna da yake an ma Ahmed transfer daga Qatar, saidai mu musu fatan zuri’a d’ayyiba. Bayan biki da sati Sultee da Nafisa suka je Hamaz don Yabi ta damu tanaso taga Nafisa da jikanta da ke ciki, gaskiya Nafisa tayi sa’ar dangin miji don ba ‘karamin tarairaya suke nuna mata ba, Yabi tana matu’kar son cikin. Sunyi sati biyu sannan suka wuce, yana matu’kar kula da ita wane ‘kwai (Ya Allah kabamu masu sonmu tsakani da Allah), kullum baba Rabi, Amira, Ammi, mummy, Yabi duk sai sun kirata su tambayi lafiyarta, ita har tana mamakin su ganin yanda suka ‘kwallafa rai akan cikin nidai nace ba abin mamaki bane in akayi la’akari da shekarun Sultan don kuwa kowanne iyaye sunason ganin jikansu gashi yanzu sun samu ai dole suyi murna sosai. Cikinta ya cika wata tara suka dawo gida don haihuwa, Yabi taso suzo Hamaz amma Abba yace mata tayi ha’kuri tunda dai itama Nafisa za tafi so ta haihu a gidansu kuma anan ba zata sake sosai ba tunda gidan surukai ne, ba don taso ba haka ta ha’kura. Kwana uku da zuwarsu Nigeria cikin ikon Allah ta haifo ‘ya mace kamanninta sak Sultee, murna a wajenshi bazai fad’u ba, washe gari Yabi ta iso kallon jikanta don ta kasa ha’kuri, rungumeta tayi tana tuna lokacin da ta haifi Sultan don yarinyar tafi kama da babanta akan mamanta, baba Rabi ita tayi ungo zoma. Ana jibi suna Amira da Ahmed ma suka iso itama da d’an ‘karamin cikinta, tayi kyau abunta, da ta d’auki babyn har hawaye tayi a zuciyarta tace “Allah sarki, ashe rabon babyn nan ne yasa muka rabu da Sultan”, ranar suna yarinya taci sunan Amira don yace Amira ta cancanci fiye da haka daga wajenshi tunda ita ta sadashi da farin cikinshi, dama Amira tayi shopping na kayan suna akwati biyu, ai tuni tace tunda an mata takwara dole ta ‘kara kaya, sabon shopping ta shiga tayi ma little Amira har akwati biyar, baby ta tashi da akwati bakwai daga wajen takwararta, Sultee kam kaya kaman hauka yayi ma ‘yarshi da Gimbiya, bikin suna sai sam barka don naira yayi kuka, yarinya tayi farin jini. A daren ranar neh Amira ta gayama Nafisa cewa tasan Sultee yana sonta tun bayan aurensu da diary da tagani da dai sauransu har ‘karyar da ta shirya don su daddy su yarda ya saketa ba tare da sunga laifinshi ko nata ba, Nafisa mamaki ‘karara a fuskarta, ta ‘kara tabbatar da lallai Amira mai sonta ne na gaskiya wanda azamanin yanzun nan da ‘kyar asamu irinta, godiya bila adadin tayi ma Amira saka makon sadau’karwar da ta mata ta kuma yi al’kawarin bazata ta’ba nuna ma Sultee tasan maganar ba. Ranar da tayi arba’in akayi auren Saleem da wata ‘yar katsina mai suna Amrah, kowa sai yaba hankalinta yakeyi don yarinyar akwai nitsuwa. Bayan bikin ne suka koma ita da Sultee ta cigaba da zuwa school suna kula da Noor. Bayan 10 years Ba mu muka waiwaye su ba sai bayan shekaru goma, mun samu Sultee ya ‘kara zama babban mutum, naira ya ‘kara zaunuwa, soyayya tsakaninshi da Gimbiya kuwa kamar yau suka soma, ta gama makaranta amma ya hanata aiki wai yafiso ta dinga kula dashi da yaransu. Yanzu ‘ya’yansu bakwai, Amira wacce ake kira Noor, mai sunan Yabi wato Hafsat amma ana kiranta Mami, Ibrahim takwarar Daddy amma suna kiranshi Anas, Rabiya wacce suka yi ma baba Rabi takwara wacce suke kira da Futha, twins mata Fatima da Maryam takwarar Ammi da mummy ana kiransu Ilham da Ummitah, sai auta mai sunan Abba wato Mu’awiyah ana kiranshi Haneef. Yara kyawawa dasu sai Allah ya raya ya sa su girma akan turban addinin Musulunci. Anan muka ji labarin Amira yaranta hudu: Usman takwarar baban Ahmed suna kiranshi Zunnurayn, Abdullahi, Sultan ‘karami wanda ake kira Boy sai auta Fawziyyah ana kiranta Zeebly. Gidan Saleem da Amrah kuwa yaransu biyar: Nafisa ‘karama ana kiranta Feesha, Sabir, Sadiya, Abbakar Sadiq sai auta Aisha. Family ya ‘kara girma gashi kansu a had’e yake, every december gaba d’aya ake yin family re-union gwanin ban sha’awa. Ya Allah ka bamu zuri’a d’ayyiba mai albarka (Ameeeeen). Anan muka kawo ‘karshen littafin nan mai suna Gimbiya Nafeesah, duk kuran kuran da ke ciki Allah ya yafe mana. Gaisuwa zuwa ga: Aisha Naany(Allah ya saukeki lafiya), Sadydy gulgul, Shukurah, Amirah Maisikeli na Ahmed, Amrah Auwal Mashi, Bahiratu my crazy sis, Milly Balalau, Anty Muma, Hajju, Zainab Sifawa, Kdeey and duk sauran ‘yan Novels Novella da ban ambaci sunayenku ba, Allah ya bar zumunci. Godiya da jinjina zuwaga Fawziyyah maman Ilham, nagode ma Allah da yabani sister kamar ki, thank u for all the love and support, Jamila Moh Ali bansan ya zan gode miki ba, Allah ya saka da alkhairi, Khadijah body ke ta dabance. Excellent writers, Mu farka mata 1 & 2, House of novella na kdeey, Yau uwan juna na sisi axland, Zauren karatu na Sis Bena, M.Jabo munbarin hausa novels na Jabo our honourable admin, Be a lady with fashion na Futha, Sahaf’s Novels, Er lele hausa novel group, Maman Aleesha novels, Maman Haneep novels, matan kwarai na Serdeeyer, Hausa novels, Rookie Sadau novels, da ma duk sauran da ban ambata ba we luv you all da soyayyar da kuka nuna ma littafin nan. NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA), thanks for being here, duk members na ciki na gaisheku Allah ya ‘kara had’a kanmu ya kuma ‘kara basira. Dedicated to Faty Axland and Maryam Gidado (Ummieterh), love u loads and loads. Allah ya had’amu a aljannah baki d’aya (Ameen). Sai kun jini bayan exams a sabon littafina mai suna………. Www.haneefahusman.wordpress.com 07053072615.
Chapter 23 · 0% Book details