Sashe 3
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH [6:06pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Ta dauki kusan minti daya sannan numfashinta ya dawo normal,Jamila tahau tambayarta “Yadai?ya dakeki neh?Biyoki yayi?” nan Nabila ta tanka mata tace “Iskanci,ke ba” sai ta kwashe da dariya. Tayi mai isarta sannan taci gaba “Ba kin gudu kin barni ba,ai na nuna mishi nima ba tayar baya bace sannan namishi gwalo nagudu shine fah yabiyoni kikaga na shigo nan a bai bai”,dukkansu biyu suka hau dariya,basu masan baba Rabi tashigo ba saida tace “Lafiyarku kam?wannan irin dariya haka saikace sabbin kamu”. Nabilah da Jamila suka tsaya kallon kallo ba wanda yayi magana har saida baba Rabi tagaji da jirar amsarsu sai kawai ta girgiza kai tace “Allah ya shiryeku,mutane neh ba abinda suka sa a gaba sai sha’kiyanci” sannan ta sa kai ta fice daga d’akin. Akazo cin guava nan fah rikici ya kachame,Nabilah ta mi’kama Jamila guda hudu itakuma ta ri’ke guda tara,Jamila tace “Haba Nabila,tare fah mukaje muka tsinko abunnan,ai ko guda shida neh saiki bani inyaso sai ke kici bakwai” Nabilah tace “Tabdi!! Kamar ya tare muka tsinko?ke fah ba abinda kika tsinana inba kallo ba,da wanchan mutumin yazo kuma gudu kikayi kika barni,kin ma ci sa’a neh ai da ko daya bazan baki ba” Jamila tayi ‘kwafa tace “Bazan yarda ba wlh”. Nan fada ya kaure tsakaninsu,Nene da tashigo wajen baba Rabi neh taga damben da sukeyi da kyar ta rabasu sannan ta sasanta su tabama Jamila guda biyar,Nabila kuma guda takwas. Da dare Nabilah na zaune a d’aki tana bitar haddarta baba Rabi tashigo tace “Yauwa Nabilah zo ki dauki madarar auta ki kai mishi dakinshi yanzun nan” saida ta kai aya sannan tace “Toh Umma” saita tashi ta ajiye Al- Qur’anin a kan drawer. Tayi sallama yakai sau uku amma bai amsa ba,kawai saita yanke shawarar shiga d’akin. Ta bud’e a hankali ta ‘kusa kanta,chan ta jiyo muryarshi yana waya a bedroom,tsaki taja a fili tace “Yana waya da ‘karfi kamar wani mahaukaci” ashe shikuma da yaji an bud’e ‘kofa saiya fito parlourn. Yana fitowa caraf maganar da ta fad’a a kunnenshi Haneefah Usman da Maman Khalil [6:56pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Bata ji fitowarshi ba sai kawai taga mutum a gabanta,ta zaro ido tabude baki da niyar magana amma maganar ta’ki fita,buge bakinta yayi da hannunshi yace “Ke wato nagane bakida kunya ko?kin rainani,bakisan ni waye ba ko?” taji ras kam kuma gabanta sai dukan uku uku yakeyi amma tayi ‘karfin halin cewa “Ayyah ba fah dakai nakeyi ba amma shine harda buga min baki” juyawa yayi ya ‘kare ma d’akin kallo sannan ya juyo wajenta yace “Na dai ga ba kowa a d’akinnan,daga ke sai ni,da wa kike magana?ko da aljanun da suka haukataki kikeyi?” murguda mishi baki tayi tace “Ni ba mahaukaciya bane saidai in kaine mahaukacin,ni da ba don aikena akayi bama meh zai kawoni da’kinka?” har ya d’aga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya fasa,furzar da iska yayi sannan yace “Ajiye abinda aka aikeki ki ‘kara mai kamin na ‘ballaki” Cikin rawar jiki ta ajiye jug din har takai ‘kofa ‘kasa-‘kasa tace “Allah ya isan min mugu” murmushin gefen baki yayi yace “Na jiki”,ai dagudu tayi waje. Tana cikin tafiya itakadai tana magana azuci “Duk yanda akayi wannan yanada cin zali,ashe dai jinshi yafi ganinshi tunda umma tacemin shi baida damuwa kuma yanada fara’a da son mutane,toh ko dai abokinshi neh wannan ya rainamin wayo?” afili tayi murmushi tace “Duk yanda akayi ma abokinshi neh bashi ba” haka dai tayita sa’ke- sa’ke har ta isa dakinsu. Abangaren Saleem kuwa kwanciya yayi akan kujera yafara tunani “Wace yarinya ce wannan? anya tasan ni kuwa?kodai tsaba rashin kunya neh yasa takemin haka?ko dai itace ‘yar baba Rabi?” wani zuciyar kuma yace mishi “Ina!! Ba yanda za ayi ‘yar baba Rabi ta zama haka”. Kwana biyu da faruwar hakan duk Nabila da Saleem basu sake haduwa ba. Yau yakama lahadi,Nabilah tadawo daga islamiya sai ta tafi da’kinsu Amina,anan ta tarar da ita tana wanki,dama Nabilah akwai son harka da ruwa sai kawai tace “Amina barin tayaki wankin”,Amina taji dadi har ranta sai tace “Ko kefa,dauko bokitin chan saiki zo kina daurayemin inna wanke” Haneefah Usman [7:32pm, 15/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Haka kuwa akayi,Nabilah taje ta ciko bucket ‘kato da ruwa tafara dauraye ma Amina kayan sannan ta shanya,ta dauraye mai d’an yawa saikuma ta tsaya. Amina ta tambayeta “Ya kika tsaya?ko kin gaji neh?” Nabila ta girgiza kai tace “Haba gajiya,kawai naga ruwan ya’baci neh,barinje ta chan gefen na watsar tunda dare neh kinga ba mai zuwa tanan” Duk da bokitin yana rinjiyarta amma haka ta dagashi,taje daidai bakin wani kwana haka saita watsar,watsarwar da zatayi gaba daya ajikin Saleem da yasha wankarshi sai ‘kamshi yakeyi zaije dinner na auren abokinshi. Wani ihu da Saleem yayi neh ya fargar da ita ajikin mutum ta watsa,arazane ta dago idanunta da niyar bashi ha’kuri amma ina!! Saleem ya harzu’ka iya harzu’ka,baima jira meh zatace ba ya iso wajenta ya wanwanketa da mari har uku,bashiri ta yar da bokitin dagudu tayi hanyar d’akinsu. Tana shiga tasaka key,hannunta dafe a kumatun da ya wanka mata mari sannan ta jingina da jikin ‘kofar d’akin,wasu hawaye neh suka zubo mata wanda batasan sun zubo ba don harga Allah marin ya shigeta kuma tunda taga yanda ranshi yabaci tasan in ba gudu tayi ba zai iya kaita lahira( ga tsoro ga rashin kunya) Amina ta gama wanki tanata jiran Nabila ta dawo amma shiru ba ita ba labarinta,daga ‘karshe ma kawai saita dauraye abunta ta shanya sannan taje ta kwankwasa ‘kofar d’akinsu Nabilah. Nabila da bacci yafara kwasarta ajikin ‘kofar taji ana knocking,a firgice ta farka ta fara karanto addu’o’in tsari,ita a tunaninta Saleem neh,da yake baba Rabi ta dade da yin bacci sai ta kwanta a bayanta tsaba tsoro. Da Amina taga ba abude ba sai kawai ta koma d’aki ta kwanta Washegari duk wanda yaga Saleem yasan ranshi a ‘bace yake,gaba daya yinin ranar da d’aki yayi shi,duk wanda ya tambayeshi meke damunshi sai yace kawai kanshi neh ke d’an ciwo. Mai martaba yatura baba Rabi ta tambayi Saleem watakila zai gayamata,da sallamarta ta shiga,suka gaisa sai ta gyara zama tace “Saleem,meke damunka?karkace min ba komai don ba tun yau ba nasanka” guntun tsaki Saleem yaja sannan ya labarta mata duk abinda ya faru akan wata yarinya ta watsa mishi ruwan dotti. Tayita bashi baki har dai ya d’an sake,suna cikin hira sai akayi sallama,dukkansu biyu suka amsa. Nabilah ce tashigo d’auke da tray na fruits da Yabi ta bata ta kawo ma auta. Saleem yana ganinta ya mi’ke,afusace ya nufeta yace “ke meh ya kawoki d’akina mara kunya,ko da yake gwanda da kika kawo kanki watakila na sassauta miki hukuncin ki”,cikin rawar murya Nabila tace “Kayi ha’kuri don Allah,wallahi ban san kana ta wajen bane saisa” baba Rabi da ta rasa gane meke faruwa tace “Auta meh ya hadaka da Nabila?ta maka rashin kunya ko?”. Daga Nabila har Auta a firgice suka juyo zuwa wajen baba Rabi,cikin rashin fahimta auta yace “Nabila ce wannan?” kusan lokaci daya Nabila ma tace “Umma dama wannan neh Auta????” Haneefah Usman da maman Khalil GIMBIYA NAFEESAH [8:37pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi ta tsaya tana kallonsu sai chan tace “Meh ke faruwa neh?kumin bayani”. Jiki asanyaye Saleem ya zauna a kan kujera,ya furzar da iska da ya zama mishi kaman jiki,Nabilah kuwa tsugunawa tayi a wajen batace komai ba,saida baba Rabi ta sake maimaita tambayar sannan Saleem ya labarta mata daga farkon haduwarsu inda ta jefeshi da dutse kuma yace da gangan neh,caraf Nabilah ta kar’be “wlh umma karyanshi neh,banmasan yana wajen ba fah nikuma ina cire guava,inbanda shi ma mai yakaishi zama a lambu illah neman magana”,zaro ido Saleem yayi yace “Ke waye yayi karya?wlh zan pasa bakinki” cikeda tsiwa tace “Atoh,karya neh……” kiran sunanta da baba Rabi tayi neh yasa ta ja bakinta tayi shiru,nan baba Rabi tace “Yi ha’kuri auta,cigaba,ina jinka”. Saleem ya had’ama baba Rabi ‘karya da gaskiya yace “ko ranar da kika aikota da madara ma don nace ta zubamin a cup saita d’aga jug d’in ta juyemin madarar a jikina,Nabilah ta dafe ‘kirji tace “Lahh!!amma kai babba da kai kana ‘karya?” baba Rabi ta tashi da niyyar marinta amma dasauri Saleem ya tareta,cikin zafin rai baba Rabi tace “Kabarni na saita mata hankali,yarinya neh sam batasan girman na gaba da ita ba”,murmushi Saleem yayi sai yace “Yi ha’kuri,inhar ni neh toh wlh na yafe mata,abinda ya faru yariga da ya faru saidai a kiyaye na gaba”. Haka dai baba Rabi takoma ta zauna tashiga bama Saleem ha’kuri,shiko gogan sai wani murmushin mugunta yakema Nabila,daga ‘karshe yace “Bakomai,ni a matsayin ‘kanwata na d’auketa”,murmushi baba Rabi tayi sannan tamishi godiya,tasa Nabila ta bashi ha’kurin dole,ba don taso ba ciki ciki tace “Yi ha’kuri”. Murmushi dauke a fuskarshi ya matso kusa da inda take tsugunne sannan ya dagota ta tsaya,saiyace “I forgive u lil sis,amma daga yau karki ‘kara min rashin kunya kinji?”,murmushin ‘karfin hali Nabila tayi sai tace “In Sha Allahu bazan ‘kara ba” Hanee:mrgreen: da maman Khalil [8:54pm, 16/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Baba Rabi bakinta ya kasa rufuwa tsaba murna ganin Auta ya saki ranshi kuma ya nuna ya d’auki ‘yar tilor ‘yarta a matsayin kanwarshi,ji tayi kaman ta zuba ruwa a ‘kasa tasha. Jawo Nabilah yayi zuwa kan kujera dukkansu biyu suka zauna,nan yafara tambayarta wani makaranta take,wani aji da dai sauransu. Nabila uwar surutu haka ta zage ta bashi harda labarin da bai tambayeta ba,hira sukeyi kaman sun saba da juna. Sun dade suna hira sannan baba Rabi tace “Auta saika tashi kaje wajen Yabi ko?duk hankalinta a tashe yake da taga baka walwala” mi’kewa tsaye yayi sai yace “Kuma haka neh fah” sannan ya maida kallonsa zuwa ga Nabilah “Kanwata tashi muje” cike da zumudi Nabila ta mi’ke tace “Toh yaya Saleem”. Yabi taji mamaki sosai da taga Saleem ya saki fuskarshi,nan ta tambayi baba Rabi