Sashe 11
Gimbiya Nafeesa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GIMBIYA NAFEESAH [7:52pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Nabilah tace “Bazan baka kunya ba in Allah ya yarda,kuma bazan ta’ba zubar da mutunci nah ba”,wani ajiyar zuciya Sultee ya sau’ke wanda sai da duk ‘yan parlourn suka dubeshi,fuskewa yayi ya tsare kaman ba shi ba. Mai martaba yayi gyaran murya yace “Alhamdulillah tunda kin amince zaki bisu,yanzu sai muyi addu’ar Allah ya kaiku lafiya tunda gashi lokacin tashin jirgin ya ‘kusa”,sarkin gida ne yayi addu’a sannan taro ya watse,duk aka dunguma zuwa inda aka parka motocin da zasuyi rakiya zuwa airport. Yabi,Baba Rabi,mai martaba,Saleem,Amina da Jamila duk anje airport,Amina da Jamila sai kuka sukeyi zasu rabu da bestfriend nasu,Nabilah ma dai kuka takeyi,ta bibbisu d’aya bayan d’aya ta rungumesu. Da tazo wajen Saleem saita kasa rungumeshi,tsayawa kawai tayi tana goge hawayen idonta,Saleem kasa jurewa yayi,bashiri ya jata jikinshi ya rungume yana bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun d’au mintuna ahaka sai rarrashinta yakeyi,tayi shiru sai ajiyar zuciya. Sultee da ke gefe haushin Saleem ya cikashi,cikin masifa yafara “Ya zaka wani rungumeta saikace muharraminta?bawai ku yara ‘kanana ba, wannan ai d’abi’ar jahilai neh”,wani kallo Saleem ya bishi dashi sannan ya sake Nabila,ya bud’e baki zaiyi magana amma kallon da mai martaba yamishi alaman yayi shiru yasa yayi controlling temper dinshi,afusace ya juya ya koma motar. Mai martaba ya ‘kara ma Sultee nasiha akan ya dinga ‘ko’karin danne ‘bacin ranshi,ha’kuri yaba ma mai martaba sannan suka lula cikin jirgi zuwa Qatar,ko ya zaman zai kasance achan,kudai biyomu… Ni da maman K ma muna tare dasu don d’auko muku rahoto Hanee da maman Khalil [10:26pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil QATAR Sun sau’ka a Doha dake cikin Qatar lafiya lau,driver’n Sultee da ke chan yazo ya d’aukesu zuwa Al Asmakh street,anguwa neh mai kyaun gaske. Wani gida driver yayi horn aka bud’e gate,gidan flat biyu ne aciki,Sultee ya bud’e d’aya daga ciki ya shiga sannan su Amira ma suka bi bayanshi,driver ya kwaso kayaki daga booth ya diresu a parlour sai ya musu sallama ya fice. Parlour neh ‘katon gaske,kujerun coffee colour neh,daga chan gefe kuma dinning area,ta hagu kitchen neh da store aciki,ta dama kuma wani ‘kofa neh. In an bud’e ‘kofar akwai toilet d’aya sai d’akuna guda biyu kowanne da toilet aciki,duka d’akunan royal beds neh aciki,d’aya coffee colour,d’ayan kuma pink. Ata’kaice dai gidan ya tsaru kuma ba acika kayaki dewa ba,just kad’an amma komai acikin tsari akayi. Sultee ya sallami Amira yace “Ni na tafi side nah,nan d’in saiku zauna ku biyu”,Amira tayi murmushi tace “Toh,daman ni nafiso mu zauna tare da ita”. Yana fita Amira ta maida kallonta wajen Nabila sai tace “‘kanwata tashi ki shiga d’aki mana ki huta,duk wanda yamiki ki saka kayanki aciki”,murmushi Nabilah ma tayi sannan tace “Nagode sosai Anty Amira,barin shiga ciki”. Da yake kujerun parlourn coffee colour neh kuma d’aki d’aya gadon shima coffee colour ne sai Nabilah ta saka kayanta a d’aki mai pink bed d’in. Da dare Sultee yamusu ordering na abinci daga restaurant,sunci sun ‘koshi sai suka zauna suna hira sama-sama,Nabila kam hankalinta yana kan wayanta ma sai chatting takeyi. Magana d’aya-biyu sai Sultee ya sakota aciki,chan sai ta tashi ta musu sai da safe. Har ta bud’e ‘kofar da zai sada ta da d’akinta sai Sultee ya tsaidata Hanee da maman Khalil [10:43pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Yace “Aff! Kinga na manta”,juyowa tayi amma bata dawo ta zauna ba,da yaga bata da niyya sai yace “Zo ki zauna,magana nakeso muyi”. Taso ta mishi gardama amma kunyan idon Amira yasa ta koma ta zauna akan kujera,ciki- ciki tace “Gani” tana cigaba da danne-danne da wayarta. Sultee ya d’anyi jim sai yace “Ajiye wayar nan zakiyi fah don in ina magana da mutum banaso yana ta’ba waya”,tura baki Nabila tayi amma ba ta ajiye wayar ba sai tace “Ai ba wai kunne nah bane ya toshe da in ina danne danne bazan ji me kake fad’a ba”,tsaki yaja sannan yace “Tashi ki tafi in har bazaki iya ajiye wayar ba”. Jin yadda yayi maganar tasan ranshi ya ‘baci neh sai tayi saurin ajiyewa,dama abinda takeso kenan wato ranshi ya ‘baci. A hankali tace “Yi ha’kuri”,Amira kam dariya tayi tace “Ohh Nabila,ashe dai kema ba tayar baya bace”,murmushi Nabila tayi ta sunkuyar da kai. Saida ya gama jan ajinshi sannan ya dubeta yace “Rules na gidannan nakeso na gayamiki,na farko….”,da sauri Nabila ta d’ago kanta tana kallonshi,a razane ta katseshi tace “Ohh masifa!!wani rules kuma ya Allahu?,ni fah banason takura”,kallonta ya yi na ‘yan seconds sannan ya yi wani shu’umin smile sai yace “Ban nemi ji ta bakinki ba..and karki sake katse min magana,in ina magana shuru zakiyi sai na gama sannan ki d’ora da taki”. Nabila tace “Okay,Allah ya baka ha’kuri”,gyara zama Sultee yayi sannan yafara “Kaman yanda kika sani kinzo garin nan neh domin karatu,na samo miki admission a Carnegie Mellon University,zaki karanta Biological Science” murmushi Nabila tayi don taji dad’i,daman course da takeso kenan. Hanee da maman Khalil [11:08pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Sultee yaci gaba “karki kuskura na ganki da saurayi,don kinzo ne kiyi karatu ba ki tsaya ‘bata lokacin ki akan samari ba,in har ba lectures kike dashi ba karki fita ko da bakin gate ne,bake ba fita ke kad’ai sai in da Amira ko kuma ni” “zan je na duba time table naki naga schedules na lectures naki don kar kimin ‘karya kice kin tafi lectures bayan ba haka bane,na samo miki driver domin kaiki school kawai,he’ll always be available,in time na cin abinci yayi dole ne ki fito mu had’u a dinning aci tare don bazan yarda da barin kanki da yunwa ba,nasan ki da baki…zaki iya cema abba bamu baki abinci saisa nayi ma tufkar hanci,a nan zan tsaya for today saidai ba iyakacin rules d’in ba kenan,a sannu zakisan sauran” Tun da yafara maganar nan Amira da Nabila suka sake baki suna kallonshi,Amira tunani kala-kala ya fara yawo a kanta “Anya ya Sultee ba son yarinyar nan yakeyi ba?irin wannan rules haka?”. Abangaren Nabila kuwa kasa ‘boye mamakin ta tayi,’kwafa tayi ta turo d’ankwalinta gaban goshi irin ture kaga tsiya dinnan,tana karkad’a ‘kafa,cike da rashin kunya tace “Ehh?meh kace??wai kar in kula samari?in ban kulasu ba kai zan kula?so kake nayi bunga a gida ko meh?batun fita yawo kuma wallahi saina fita,haka kawai ka hanani zagaya gari? tab!!ai wallahi sai dai sama da ‘kasa su had’u amma abinda naga dama zanyi”. Cike da mamakin irin rashin kunyanta yake kallonta,ranshi in yayi dubu toh ya ‘baci,tashi tsaye yayi yace “Okay fine,haka kikace ko?ban isa na kapa dokoki agidana kibi ba?that’s good,duk rawan da kanki yakeyin nan i promise u saina saita miki hankali,bana son reni”. Tsaki taja sannan ta tashi da niyyar tafiya d’aki,cafkota yayi,cikin wani loud voice yace “Wa kika ma tsaki?”. Hanee da maman Khalil [11:33pm, 27/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH Na Haneefah Usman ®ONLINE HAUSA WRITERS da Khadijah maman Khalil Hanjin cikinta suka kad’a ganin gaba d’aya yafita hayyacinshi,jikinta yana rawa tace “wayyo Allah ya Sultee zaka karya min hannuna,kayi ha’kuri bazan sake ba,wallahi na tuba,zan bi dokokin ka” tsaba azaban yanda ya ri’ke hannunta batasan time da ta fara hawaye ba,wurgata yayi tafad’i ‘kasa,bai yi mata magana ba ya juya ya fita daga parlourn. Yana fita Amira tazo inda Nabila take kuka,d’agota tayi ta taimaka mata ta tafi d’aki sannan ta fara mata nasiha “Nabila,kinga ya Sultee yana da mugun zuciya,kuma zuciyarshi bai da kyau,komai zai iya miki inhar kika kaishi bango,kinga nan ba 9ja bane,babu abba babu kowa sai mu kad’ai,rashin kunya ba naki bane,ajiyeshi a gefe zakiyi ki bishi a hankali kar watarana ya dakaki ko ma fiye da haka a gidannan”,tana hawaye ta rungume Amira tace “Toh anty Amira,zan yi iya ‘ko’kari nah na ganin na kauce ma hanyar da zaisa ya ta’ba lafiya nah”,Amira tayi murmushi tace “Yauwa,ko kefa? kiyi shiru toh”,sun dad’e suna hira sannan Amira ta koma d’akinta. Bayan sati daya Nabila tana taka-tsantsan da Sultee,gaishe shi takeyi kaman babanta,ga ladabi da takeyi kaman ba ita ba,yana cewa tayi abu cikin ‘barin jiki takeyi,wani lokacin har dariya ma abun yake bashi. Suna zaune a dinning suna lunch sai Nabila tace “Ya Sultee ayyah alfarma nake nema”,ba tare da ya kalleta ba yace “Uhum,na meh?”,a sanyaye tace “tunda mukazo ko gate banje ba,gashi jibi zan fara zuwa school kuma inaso naje nayi shopping abubuwan da zan bu’kata”. ‘dagowa yayi ya kalleta sai yaji tausayinta,chan sai yace “Bari mu gama sai muje”,godiya Nabila tashiga kwararowa,Amira kam sai dariya take mata. Sunje wani babban shopping mall,Sultee yace su za’bi abinda sukeso ita da Amira,kowa ya d’auki troller. Nabila taje ta wajen perfumes tana za’ba sai wani saurayi yazo yamata sallama,amsa mishi tayi sannan taci gaba da abinda takeyi. Nan ya mata introducing na kanshi as Yusuf sannan shima d’an 9ja neh amma yana aiki a nan Qatar,bata tanka mishi ba har ya ‘karaci flows nashi wai shi yana sonta. Ro’konshi tafara akan ya rufa mata asiri yatafi kar yayanta yazo ya sameshi amma Yusuf ya’ki,tura troller’nta tayi shima yana tura nashi a ‘kusa da ita. Dum!! Gabanta ya buga ganin Sultee a gabansu,kallonta yayi cike da ‘bacin rai,jikinta har rawa yakeyi don tsoro,Yusuf da baisan dawar garin ba ya mi’ka mishi hannu,Nabila ta fara kame-kame “Ya…Sul…tee…wallahi ban… sanshi ba” fincikarta yayi ya jata ita da troller dinta fuuuu suka bar wajen. Hanee da mama GIMBIYA NAFEESAH [8:36pm, 31/01/2016] Haneefah : GIMBIYA NAFEESAH © Haneefah Usman ®OHW da © Khadijah maman Khalil Har counter sukaje amma still yana ri’ke da hannunta, ana cikin lissafi sai Amira ta iso wajen da nata troller din, ita duk bata lura da hannun Amira da Sultee ya ri’ke ba saidai taga yanayinshi ya chanja ba kamar yanda yake dazun ba. An gama lissafi aka kai musu kayakin cikin boot, janta ya ‘karayi yana sauri itakuma da yake high heel ta saka sai tana neman fad’uwa, Amira tayi saurin tarota tace “Yadai Nabee, kiyi tafiya a hankali mana”, Nabila kaman zatayi kuka tajuyo tana kallon Amira sai tace “Don Allah anty ki bashi